Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Fauziyya Kabir Tukur, Nasidi Adamu Yahaya da Umar Mikail

time_stated_uk

  1. Mu kwana lafiya

    Mun kawo ƙarshen rahotannin. Muna fatan za ku kwana lafiya.

  2. Labarai da dumi-dumiSaka takunkumi na damu na – Buhari

    Muhammadu Buhari

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce babu abin da ke damun sa bayan da aka yi masa allurar rigakafin korona karo na biyu sai dai saka takunkumin kariya daga cutar.

    Ya bayyana haka ne yayin wata hira da ya yi da gidan talabijin gwamnatin tarayya na NTA a daren yau Juma'a.

    Da ɗan jarida Adamu Sambo ya tambaye shi: "Kwana nan aka yi maka rigakafin korona karo na biyu, ko akwai wani abu da allurar ta haddasa maka?"

    Sai Buhari ya amsa da cewa: "Babu wani abu da nake ji zuwa yanzu. Amma saka wannan abin da nake kira da takunkumi yana damu na gaskiya."

    A watan Janairun 2021 ne Shugaba Buhari ya saka hannu kan dokar da ta tilasta saka takunkumi a bainar jama'a, sai dai a watan ne aka gan shi ba tare da takunkumin ba a garin Daura mahaifarsa, lokacin da ya je sabunta rajistarsa ta jam'iyyar APC.

    Buhari
  3. Ethiopia ta ƙaryata batun cewa akwai yunwa a yankin Tigray

    Ethiopia

    Gwamnatin Habasha wato Ethiopia ta musanta rahotannin da ke cewa ana cikin halin matsananciyar yunwa a yankin Tigray, wanda yaƙi ya ɗaiɗaita.

    Martanin ya biyo bayan wani rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya ne wanda ya ce mutum 350,000 na raye cikin yunwa, abin da gwamnatin ta ce "ba shi da tushe".

    Batun na zuwa ne bayan wata bakwai da aka shafe ana yaƙi a arewacin Ethiopia, inda aka kashe dubbai kuma aka raba wasu da muhallansu.

    Ethiopia ta ce rahoton da ya yi gargaɗi game da yunwa ba gaskiya ba ne.

    Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin waje ya ce gwamnati na bai wa mutanen da ke cikin buƙata abinci.

  4. Ba za mu hukunta masu amfani da Twitter ba - Abubakar Malami

    Abuabakar Malami

    Ministan Shari'a a Najeriya, Abubakar Malami, ya faɗa wa jaridar Vanguard cewa gwamnati ba ta taɓa yin niyyar hukunta waɗanda suka ƙi daina amfani da Twitter ba sakamakon haramta shi da aka yi a ƙasar.

    Malami ya ce za a ɗauki mataki ne kawai a kan "duk wani mutum ko kamfani da ya taimaka wa Twitter wajen kauce wa haramcin da gwamnati ta yi masa a Najeriya".

    "Saboda dalilai na tarihi, bari mu bayyana ƙarara cewa Abubakar Malami ba ya neman hukunta dulk wani ɗan Najeriya da ke yin Twitter a Najeriya ko kuma daga wani wuri amma duk wani ɗan Najeriya ko kamfani da ya taimaka wa Twitter wajen kauce wa haramcin za mu hukunta shi," in ji Malami.

    A makon da ya gabata, mai magana da yawun ministan ya faɗa wa BBC cewa barazanar da Malami ya yi cewa za a hukunta duk wanda ya bijire wa umarnin daina amfani da Twitter ta ƙunshi kowane ɗan ƙasa da ya ci gaba da amfani da shafin.

    Akasarin 'yan Najeriya ba su daina amfani da dandalin ba tun bayan sanar da haramcin a ranar Juma'a da ta wuce, inda suka dinga amfani da manhajar VPN domin kauce wa toshewar da kamfanonin sadarwa suka yi wa Twitter.

    Sai dai Malami ya ce sanarwarsa ta farko ba ta ce a hukunta "duk wanda ke amfani da Twitter ba ko wani dandalin zumunta domin bayyana ra'ayinsa".

  5. Gwamna ya sha caccaka bayan ya nemi Musulmai su rage haihuwa a Indiya

    Indiya

    'Yan siyasar hammaya a Assam da ke Indiya sun cacaki gwamnan jihar bayan da ya yi kira ga Musulman da ke jiharsa da su yi amfani da tsarin kayyade iyali domin rage talauci da matsalolin zamantakewa.

    Himanta Biswa Sarma ya ce za a iya shawo matsalar gine-gine a filayen wasu idan Musulmai suka takaita yawan haihuwa.

    Gwamnan wanda dan jamiyyar BJP mai mulki ne wanda kuma ya yi wata ɗaya da hawa kan mulki ya bayyana haka ne lokacin da yake amsa tambayoyin 'yan jarida kan matakan da ake dauka domin magance matsalar.

    Wakiliyar BBC ta ce Himanta Biswa Sarma ya fada wa 'yan jarida cewa idan aka ci gaba da samun matukar karuwa a yawan haihuwar da Musulmi ke yi ko shi kansa gidan da ya mallaka zai fuskaci barazana.

    Sai dai 'yan hammaya sun zargi gwamnatin da saka muradun mabiya adinin Hindu a gaba, sun kuma ce wadanda aka tilsata wa barin gidajensu talakawa ne.

  6. MDD ta yi gargaɗi game da rikici a Myanmar

    Shugabar hukumar kare hakkin ɗan Adam ta MDD ta yi gargadi game da ci gaba da zubar da jini a Myammar yayin da ake samun rahotannin girke sojoji a yankuna da dama.

    Michelle Barchelet ta ce sun samu rahotanni da ke cewa sojojin Myanmar sun kashe mutum sama da 800 tun bayan juyin mulki kuma suna ci gaba da amfani da manyan makamai a kan farar hula da kuma kungiyoyi masu rike da makamai da ke adawa da gwamnatin soji.

    Wakiliyar BBC ta ce an yi ammanar cewa mutum fiye da 100,000 sun gudu daga jihar Kayak a cikin mako uku da suka gabata.

    MDD ta ce tashin hankalin ya fi shafar kabilu da addinai marasa rinjaye da ke kasar

  7. An rufe Kwalejin Nuhu Bamalli bayan 'yan fashi sun sace ɗalibai

    Kwalejin Nuhu Bamalli

    Hukumar Kwalejin Nuhu Bamalli da ke Jihar Kaduna ta sanar da rufe makarantar sakamakon harin 'yan fashin daji da ya yi sanadiyyar kashe ɗalibi da kuma sace wasu guda takwas.

    Da daren Alhamis ne 'yan bindigar suka afka makarantar, inda suka kashe ɗalibi sannan suka yi garkuwa da malamai biyu da kuma wasu ɗaliban guda takwas.

    Mazauna yankin sun ce maharan sun dinga harbi a kan kowa da kowa domin korar mutane.

    Wata sanarwa da ofishin yaɗa labaran kwalejin ya fitar ta umarci dukkan ɗalibai da su zauna a gida ban da 'yan sashen IJMB waɗanda ke shirin fara jarrabawa ranar Talata mai zuwa.

    Lamarin na zuwa bayan wasu 'yan bindiga sun sace mata 60 a Jihar Zamfara da ke yankin na arewa maso yammacin Najeriya a farkon wannan makon.

    Har yanzu masu satar mutane don neman kuɗin fansa na riƙe da ɗaliban Islamiyya kusan 136 da suka sace a makarantar Salihu Tanko da ke JIhar Neja mai maƙotaka da Abuja, babban birnin ƙasar.

  8. Buhari zai yi hira da NTA a daren yau Juma'a

    Muhammadu Buhari

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai sake yin hira ta musamman da kafar talabijin ɗin gwamnatin tarayya ta NTA a daren yau Juma'a, 11 ga Yuni.

    A cewar wata sanarwa daga bakin mai ba shi shawara kan kafofin yaɗa labarai, Femi Adesina, za a yaɗa hirar ce da ƙarfe 8:30 na dare.

    "Mun yi alƙawarin za ta kasance (hirar) mai cike da bayanai da ilimantarwa," a cewar Mista Adesina.

    Tattaunawar na zuwa ne kwana ɗaya bayan wadda shugaban ya yi da kafar Arsie TV, inda a ciki ya jaddada matsayarsa kan masu tayar da fitina a yankin kudu cewa "za mu yi maganinsu ta hanyar da suka fi ganewa".

    Sai dai Femi bai bayyana ko hirar za ta kasance kai-tsaye ba ko kuma wadda aka naɗa.

    View more on facebook
  9. Kotu a Brazil ta amince a gudanar da gasar Copa America a ƙasar

    Copa America

    Kotun Ƙolin Brazil ta yanke hukunci ranar Alhamis cewa ƙasar za ta iya karɓar baƙuncin gasar ƙwallon ƙafa ta Copa America duk da annobar korona.

    Hakan na nufin za a fara gasar ta ƙasashen yankin Kudancin Amurka nan da kwana biyu masu zuwa.

    Yayin zaman da aka yi ta bidiyo, akasarin alƙalan kotun guda 11 ba su amince da ƙudirin masu shigar da ƙara ba cewa gasar barazana ce ga lafiyar al'ummar ƙasar.

    Sai dai alƙalan sun gargaɗi gwamnati da ta ɗauki dukkan matakan kariya daga cutar.

    Gasar wadda ya kamata a gudanar tun a 2020 amma aka ɗaga saboda korona, ta shiga ruɗani ne bayan ƙasashen Argentina da Colombia sun ce ba za su iya ɗaukar nauyinta ba 'yan kwanaki kafin gudanar da ita.

    Ana gudanar zanga-zanagar ƙin jinin gwamnati a Colombia, yayin da Argentina ta ce cutar korona ce ke ƙara yaɗuwa a ƙasarta.

  10. Tafki mafi girma a Amurka na barazanar ƙafewa

    Tafkin Mead n Amurka

    Tafki mafi girma a Amurka na fuskantar barazanar kafewa wani mataki da bai taba kai wa ba a tarihi yayin da yammacin kasar ke fama da karancin ruwan sama.

    Tafkin Mead da ke iyakar Arizona zuwa Nevada na samar da ruwa ga sama da mutum miliyan 20 a birane kamar Las Vegas da Los Angeles.

    Lamarin ya kawo cikas ga harkokin noma da kuma rashin samun ruwan sha.

    A makon jiya ne gwamnan Utah ya yi kira ga jama'a da su tashi tsaye da addu'a domin neman saukar ruwan sama.

  11. Buhari ya naɗa Balarabe Shehu Ilelah shugaban hukumar NBC

    Balarabe Shehu Ilelah

    Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya naɗa tsohon ma'aikacin BBC Hausa, Balarabe Shehu Ilelah, a matsayin Babban Daraktan Hukumar Kula da Kafofin Yaɗa Labarai ta National Broadcasting Commission (NBC).

    Wata sanarwa da ta fito daga ofishin Ministan Yaɗa Labarai Lai Mohammed a yau Juma'a ta ce Balarabe Ilelah ya maye gurbin Armstrong Idachaba, wanda aka naɗa riƙon ƙwarya a watan Fabarairun 2020.

    Sanarwar ta ce sabon shugaban zai jagoranci hukumar na tsawon shekara biyar a matsayin wa'adin farko.

    Babban aikin hukumar NBC shi ne sa ido da tantancewa da tabbatar da dokokin yaɗa labarai masu sauti a Najeriya.

    Balarabe Shehu Ilelah ya yi aiki da Sashen Hausa na BBC na tsawon lokaci kafin daga baya ya koma sashen Hausa na rediyon China (CRI).

  12. Harin da Houthi ta kai ya kashe mutum takwas a Yemen

    Mutum takwas ne suka mutu yayin da sama da 27 suka ji raunuka a birnin Marib na Yemen a wani harin makami mai linzami da na jirgi marar matuki da ƴan tawayen Houthi suka kai, a cewar kafar yaɗa labarai ta Al-Masdar Online.

    A wani rahoto da ya fito jiya, kafar yaɗa labaran ta Yemen ta ambato wata majiya na cewa ƴan Houthi sun yi ƙoƙarin kai hari da makami mai linzami a wani masallaci "lokacin sallar Maghariba" da wani gidan yarin mata.

    Ma'aikatar harkokin wajen gwamnatin da ƙasashen duniya suka amince da ita sun fitar da sanarwar da acikinta suka yi kakkausar suka kan harin, inda suka ce birnin Marib "na fuskantar hare-hare mafi muni kan fararen hula."

    Marib na ɗaya daga cikin yankunan ƙarshe da gwamnati ke riƙe da su a yankin arewaci da ƴan Houthi ke riƙe da shi.

  13. Yadda jirgin kasa na Abuja zuwa Kaduna ya lalace

    Video content

    Video caption: Yadda jirgin kasa na Abuja zuwa Kaduna ya lalace

    Jirgin kasa da ke jigila tsakanin Abuja zuwa Kaduna ya lalace a ranar Juma'a.

    Jirgin, wanda ya tashi daga tasharsa ta Idu da safiyar Juma'a da ke Abuja, ya tsaya sau biyu kafin ya isa tashar Kubwa.

    A tashar ta Kubwa , ya tsaya tsawon fiye da awa daya saboda matsalar da yake fama da ita.

    Daga bisani jirgin ya ci gaba da tafiya bayan da aka kawo wani kai aka sanya masa.

    Sai dai hukumomi sun bai wa fasinjoji hakuri suna masu cewa injin jirgin ne ya lalace.

    Ba wannan ne karon farko da jirgin yake lalacewa ba lamarin da ake dangatakawa da rashin kulawa da shi sosai.

  14. Ana ce-ce-ku-ce kan rage ƙarar kiran sallar Asuba a Burundi

    Prayers

    Shugabannin Musulmi a Burundi sun nesanta kansu daga sukar da wani malami ya yi kan ministan harkokin cikin gida bayan da ya buƙaci Ladanai su riƙa kiran sallar asuba a hankali don kar su damu jama'a.

    Ministan cikin gidan Gervais Ndirakobuca ya nemi shugabannin addinai su daina ibada cikin dare da ƙarfi kuma ya ce Malaman addinin Muslunci sun riƙa kiran sallar asuba ba da ƙarfi ba.

    Ministan ya yi maganar ne a wata tattaunawa da shigabannin addinai.

    A lokacin sallar asuba ne ranar Talata Ndikumana Rashid ya soki ministan kuma ya ce ya janye kalamansa kuma ya ba da haƙuri.

    Mista Rashid ya ce kalaman ministan alamu ne na ƙin jinin Musulunci.

    Sai dai wakilan addinin Musulunci sun ce Mista Rashid na da alhakin kalamansa na sukan ministan wanda suka ce dai-dai suke da zagi.

    Shugaban majalisar Musulmi a Burundi Zuberi Mohamed ya ce babu tababa tsakanin Musulmi da gwamnati, inda ya ce babu wata doka da ta hana su kiran salla yadda suka saba.

    Ya ce ba ya ganin kalaman ministan za su janyo rikicin addini saboda Musulmi ƴan Burundi mutanen kirki ne".

  15. An sace wani malamin addinin Musulunci a Nijar

    Bindiga

    Wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne sun sace wani malamin addinin Musulunci a yankin Diffa da ke fama da rikici a Jamhuriyar Nijar, kamar yadda gidan rediyon sojoji na Bouclier ya wallafa a Twitter.

    Sheikh Ligari Mahmoud fitaccen malamin ne a Blabrine kuma an sace shi ne a unguwar N'Guigm.

    Dama dai ranar 6 ga watan Yuni ne aka sace wasu ƴan China biyu a yankin Tillaberi na Nijar.

    An ayyana dokar ta-ɓaci a Diffa tun shekarar 2015 amma wannan bai shawo kan matsalolin hare-haren ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya ba da ke auka wa jami'an tsaro da fararen hula.

    A wani ɓangaren kuma, aƙalla jami'an tsaro huɗu ne aka kashe a wani hari a yankin Agadez da ke arewa maso yammacin ƙasar.

  16. Amurka da Burtaniya sun sha alwashin ba da gudumuwar riga kafin korona

    Amurka da Burtaniya sun sha alwashin ba da gudummawar miliyoyin alluran rigakafin korona ga wasu daga cikin kasashe matalauta a wani bangare na ganin an kawo karshen annobar a duniya.

    Ana sa ran shugabannin kasashe 7 mafiya karfin tattalin arziki za su dauki makamancin alkawarin a farkon taronsu na yau a gundumar Cornwall da ke Burtaniya.

    Shugaba Biden ya ce Amurka za ta samar da allurar kamfanin Pfizer miliyan dari biyar domin hanzarta yaki da annobar ta korona.

    BBC ta ce bayan alkawarin da Shugaban Amurka Biden ya yi na ba da gudummawar alluran rigakafin miliyan dari biyar, shugabannin da dama ciki har da Firaministan Burtaniya sun yi tunanin bukatar hana afkuwar wata annoba a gaba.

  17. Za a dasha bishiyoyi miliyan biyar a Ghana ran Juma'a

    Ghana plantsa trees

    Ana dasa bishiyoyi miliyan biyar a Ghana ran Juma'a a wani yunƙuri na mayar da martabar dazukan ƙasar.

    An buƙaci duka ƴan ƙasar su sa hannu.

    Shugaba Nana Akufo Addo ya ce zai shiga a yi da shi a shirin da za a riƙa yi duk shekara.

    A wani jawabi da ya yi ta bidiyo, ya buƙaci ƴan ƙasar su killace muhallinsu ta hanyar kula da tsirran da za a shuka.

    Hukumomi sun yi ƙiyasin cewa kashi 80 cikin ɗari na dazukan Ghana ya lalace saboda lalata muhalli da sare bishiyoyi.

    Ƙasar ta riga ta fara ganin illolin sauyin yanayi.

    An yi ƙiyasin cewa za a samu raguwar kayan abinci da kashi 7 cikin 100 a tsakiyar wannan karnin.

  18. Amurka na fuskantar barazanar fari

    Tafki mafi girma a Amurka na fuskantar barazanar kafewa wani mataki da bai taba kai wa ba a tarihi yayin da yammacin kasar ke fama da karancin ruwan sama.

    Tafkin Mead da ke iyakar Arizona zuwa Nevada na samar da ruwa ga sama da mutum miliyan 20 a birane kamar su Las Vegas da Los Angeles.

    Lamarin ya kawo cikas ga harkokin noma da kuma rashin samun ruwan sha.

    A makon jiya ne gwamnan Utah ya yi kira ga jama'a da su tashi tsaye da addu'a domin neman saukar ruwan sama.

  19. An yi garkuwa da malamai da ɗalibai a makarantar Nuhu Bamalli da ke Zariya

    Nuhu Bamalli Polytechnic

    Rahotanni da ke fitowa da Zariya a jihar Kaduna na cewa wasu sun auka wa makarantar kuma sun yi garkuwa da mutane a ƙalla mutum takwas ranar Alhamis da daddare.

    Rahotannin na cewa cikin mutanen da aka sace akwai malamai da ɗalibai da iyalin wani malamin makarantar.

    Wasu rahotannin na cewa ɗalibi ɗaya ya rasa ransa sanadiyyar harbin bindiga yayin da wani ya samu rauni.

    Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya tabbatar wa BBc faruwar lamarin kuma ya ce jami'an tsaro sun yi gaggawar zuwa makarantar don tarwatsa maharan.

    Sai dai bai bayyana adadin mutanen da ka yi garkuwa da su ba.

    Makarantar Nuhu Bamalli Polytechnic ba ta da tazara sosai da sansanin sojoji da ke Jaji a jihar Kaduna.

  20. Amurka ta yi Allah wadai da matakin Najeriya kan Twitter

    Biden

    Amurka ta yi tur da matakin gwamnatin Najeriya na haramta amfani da Twitter a kasar.

    Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka Ned Price ya ce umarnin ba shi da waje a tsarin dimokradiyya sannan ya saba wa dokar da ta bai wa jama'a yancin fadin albarkacin bakinsu.

    A makon jiya ne gwamnatin Najeriyar ta sa dokar bayan da shafin ya goge wani bangare na kalaman Shugaba Muhammadu Buhari.

    Sai dai duk da matakin hana amfani da shafin, wasu yan kasar sun yi burus inda suka ci gaba da shiga shafin ta hanyar amfani da manhajar da za ta taimaka musu samun intanet ba tare da shinge ba.