Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Ahmad Tijjani Bawage

time_stated_uk

  1. Mu wayi gari lafiya!

    Masu bibiyar mu a wannan shafi na kai-tsaye, a nan za mu dakata, sai kuma gobe Juma'a, idan Allah Ya kai mu inda za mu ci gaba da kawo muku rahotanni daga Najeriya da sassan duniya.

    Nabeela Mukhtar Uba, a madadin sauran abokan aiki, nake cewa asuba ta gari.

  2. Ƴan Afirka miliyan 135 na fama da matsalar ji – WHO

    Kunne

    Hukumar lafiya ta duniya, WHO ta ƙiyasta cewa mutum miliyan 135 na fama da matsalar ji a Afirka.

    Daraktar WHO a Afirka, Dr Matshidiso Moeti, ce ta bayyana haka cikin wata sanarwa da ta fitar gabanin zagayowar ranar ji ta duniya ta bana.

    Moeti ta ce adadin na ƙaruwa kuma akwai yiwuwar nan da 2050, a samu sama da mutum miliyan 338 da ke fama da matsalar ji a Afirka.

    Ana bikin ranar ji ta duniya ne duk ranar 3 ga watan Maris domin wayar da kan mutane game da matsalar kurumta da kuma matakan kariya da kuma inganta lafiyar kunne a faɗin duniya.

    "A faɗin duniya, sama da mutum biliyan ɗaya da rabi ne ke fama da matsalolin kunne, kusan kashi 80 cikin 100 na zaune ne a matsakaitan ƙasashe. A Afirka, kimanin mutum miliyan 135 na da matsalar ji. Adadin kuma na ƙaruwa." in ji Moeti.

    Ta kuma tabbatar da ƙoƙarin da ƙasashe ke yi na samar da kula ga masu matsalar kunne tare da aiwatar da wasu dabaru domin inganta lafiyar kunne.

  3. 'Za a samu ƙaruwar masu teɓa nan da 2035'

    .

    Ƙungiyar da ke yaƙi da matsalar teɓa ta duniya ta ce nan da shekarar 2035, za a bayyana sama da rabin al'ummar duniya ko fiye da mutane biliyan huɗu a matsayin masu teɓa.

    A sabon rahotonta, ƙungiyar ta ce adadin mutanen na ƙaruwa musamman a tsakanin yara - sannan kuma galibin ƙasashen da ake hasashen za su fuskanci ƙaruwar masu teɓa cikin shekara 12 masu zuwa za su kasance daga matsakaita ko ƙasashe masu ƙaramin ƙarfi a Afirka da Asia.

    Ƙungiyar ta ce nan da shekarar 2035, kuɗin kula da teɓa zai kai dala triliyan huɗu duk shekara inda kuma ta buƙaci gwamnatoci da su ɗauki mataki.

  4. Yadda baƙar fata ƴan Afirka ke fuskantar tsangwama a Tunisia

    .

    Baƙar fata ƴan Afirka sun ce suna fuskantar rashin tsaro a Tunisia la'akari da yadda ake kai musu hari saboda launin fatarsu, kamar yadda wata ɗaliba a Tunisia ta faɗa wa shirin Africa Daily na BBC.

    Wata mata, wadda kawai take son a bayyana sunanta da Mary ta ce an cinna wa gidajen wasu mutane wuta wasu kuma an zane su, yayin da wasu kuma suka fuskanci aibatarwa.

    Akwai ma direbobin tasi da ba sa ɗaukan baƙar fata, in ji Mary.

    Mary ta ce ƙaruwar nuna wariya na zuwa ne bayan da Shugaba Kais Saied, a makon da ya gabata, ya ce tururuwar baƙi ba bisa ka'ida ba wani shiri ne na kawo sauyin al'umma a Tunisiya, ya kuma zargi baƙin da ke shiga ƙasar ta haramtacciyar hanya da hannu a ƙaruwar laifuka a ƙasar.

    An tsare gomman baƙi daga yankin kudu da hamadar sahara yayin da Ivory Coast da Guinea suka ce suna aika jirage na musamman domin kwaso jama'arsu.

    "Kamar ba a yi maka maraba a nahiyarka," kamar yadda Mary ta ci gaba da cewa.

    Ta ce tana da ƙawaye ƴan Tunisia da ke ƙoƙarin tallafa mata kuma tana da niyyar zama a ƙasar na wasu ƴan watanni domin ƙarasa karatunta.

  5. Amurka ta yi tayin miliyoyin kuɗi domin kama jagoran ƴan tawayen Congo

    Amurka ta yi tayin bayar da tukwicin kusan $5m ga duk wanda ya samar da bayanan da suka taimaka wajen kama shugaban ƙungiyar ƴan tawaye a gabashin Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo wadda ke da alaƙa da ƙungiyar IS mai iƙirarin jihadi.

    Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta ce a ƙarƙashin jagorancin Seka Musa Baluku, ƙungiyar ƴan tawaye ta Allied Democratic Forces ta halaka tare da yin fyaɗe da kuma sace farar hula har da yara.

    Jagoran ADF ɗan asalin Uganda ne inda ƙungiyar ta fara kai hare-hare a shekarun 1990.

    A 2021, Amurka ta ayyana ADF a matsayin ƙungiyar ta'addanci. Ɗaya ce daga cikin ƙungiyoyin ta'addanci da ke aiwatar da harkokinsu a gabashin Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo.

  6. APC ta ce wa Obi mu haɗu a kotun

    .

    Kwamitin yaƙin zaɓen Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ya mayar wa ɗan takarar Jam'iyyar Labour Peter Obi martani bayan da ya yi barazanar zuwa kotu domin ƙalubalantar sakamakon zaɓen shugaban ƙasar da ya bai wa Bola Ahmed Tinubu nasara.

    Jam'iyyar mai mulkin ƙasar, a martaninta, ta ce a shirye take ta haɗu da Obi a kotun.

    Ɗan takarar na Labour a taron manema labaran da ya yi a yau Alhamis a Abuja, ya yi iƙirarin shi ne ya lashe zaɓen amma aka yi murɗiya a cewarsa.

    Ya kuma ce zai tabbatar da cewa shi ne ya yi nasara.

    Idan za a iya tunawa a ranar Laraba ne hukumar zaɓen Najeriya ta ayyana Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya ci zaɓen.

    Amma da yake mayar da martani, daraktan yaɗa labaran kwamitin yaƙin zaɓen APC, Bayo Onanuga ya ce jam'iyyar ta yi maraba da matakin Obi na zuwa kotu.

    Idan har yana da yaƙinin zai gabatar da hujjojin da suka tabbatar an yi maguɗi a zaɓen.

    Ɗan takarar jam'iyya mai mulki, APC, wato Bola Ahmed Tinubu, shi ne ya yi nasara a zaɓen shugaban ƙasar inda ya samu ƙuri'a miliyan 8.79, wato kashi 37 cikin ɗari na ƙuri'un da aka kaɗa.

    Sai Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP wanda ya zo na biyu, da ƙuri'a 6,984,520, wato kashi 29.07 cikin ɗari.

    Yayin da Peter Obi ya zo na uku da ƙuri'a 6,101,533, wato kashi 25.4 cikin ɗari.

  7. An kai hari a yankin Somaliland sau huɗu cikin mako uku – MSF

    Kungiyar likitoci masu ba da agaji ta kasa da kasa ta Médecins Sans Frontières tace a karo hudu ke nan ana kai hari kan wani asibiti a yankin Somaliland cikin makonni uku sakamakon yakin da ake gwabzawa tsakanin sojoji da mayakan ‘yan tawaye.

    MSF tace an shafe kusan wata guda ana gwabza yakin, kuma har yanzu ana ci gaba da kwasar mutanen da aka raunata zuwa asibiti a garin Las Anod, inda ake fama da rashin jinin da za a kula da majinyata.

    Yankin Somaliland ya ɓalle daga Somalia a 1991, sai dai har yanzu bai samu amincewar duniya a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta ba.

    Gomman mutane aka hallaka tun bayan da mayaƙan ƴan tawayen suka fara gwabza yaƙi da dakarun gwamnati.

  8. Macron na neman ƙarfafa alaƙa da ƙasashen Afirka

    .

    Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce ƙasarsa ba ta da wani buri na komawa kan tsofaffin tsare-tsare na yin katsalandan a Afirka.

    Yana magana ne a Gabon a farkon ziyarar da zai yi a ƙasashen Afirka huɗu.

    Da alama Shugaba Macron yana ƙoƙarin shata layi kan abin da ƙasarsa ta gani a Afirka inda ya ce zamanin mulkin mallaka ya zo ƙarshe.

    A ƙasashen da ta yi wa mulkin mallaka a baya, Faransa ta daɗe tana fuskantar togaciya.

    An sha zargin shugabanni a Paris da yin burus da maguɗin zaɓe tare da rungumar mulkin kama-karya da jagorori masu cin hanci domin tafiya dai-dai da buƙatun Faransa na tattalin arziki a nahiyar.

    Sojojin da suka ƙwace mulki a Mali da Burkina Faso sun yanke alaƙa tare da korar sojojin Faransa daga ƙasar suka kuma kusanci Rasha.

    Sai dai masu nazari suna ganin Rasha za ta yi tasiri wajen daidaita al'amura ko kuma ta taimaka wajen rage rikicin masu iƙirarin jihadi a Afirka.

  9. Shugaban Kenya ya ƙalubalancin hukuncin kotu na bai wa masu neman jinsi damar kafa ƙungiya

    Kenya

    Shugaban Kenya, William Ruto da jagoran ƴan hamayya, Raila Odinga sun haɗa kai a ƙalubalantar hukuncin Kotun Ƙolin ƙasar da ya nemi a bai wa masu neman jinsi damar yin rajista a matsayin ƙungiya.

    Shugaba Ruto ya yi alƙawarin ba zai taɓa barin auren jinsu a Kenya ba abin da ya ce ya saɓa da al'adu da kuma addinin ƙasar.

    Mutane da dama suna ganin hukuncin kotun ya bai wa masu neman jinsi ragamar yin aure a tsakaninsu a Kenya.

    A ranar Juma'ar da ta gabata ne, kotun ƙolin ta yanke cewa matakin hukumar bayar da lasisin kafa ƙungiyoyi a Kenya na hana rajistar ƙungiyar masu neman jinsi ko wata ƙungiya mai kama da haka, ya saɓa wa kundin tsarin mulki.

    Kotun ta ce hana rajistar ƙungiyar kawai saboda ra'ayinsu na neman jinsi ya take ikon da kundin tsarin mulki ya ba su na yin hulɗa ba tare da tsangwama ba.

    Sai dai tun lokacin ne ake ta samun ƙorafe-ƙorafe daga jama'a da majalisa da masana addini da jami'an gwamnati masu faɗa a ji har da kakakin majalisar dokokin ƙasar da kuma shugaban ƙasar a yanzu.

    A ranar Laraba ne, majalisar dokokin ƙasar ta ɗauki lokaci tana tattaunawa kan hukuncin kotun.

    Kuma galibin ƴan majalisar da suka yi magana sun bayyana mamakin yadda kotun ta yanke hukuncin bai wa masu wannan ra'ayin damar kafa ƙungiya kan abin da aka bayyana da ya saba doka.

    Kundin tsarin mulkin Kenya ya bayar da damar yin auratayya ne kawai tsakanin mace da namiji yayin da kundin shari'a na ƙasar ya tanadi hukunci kan waɗanda suka saɓa haka da hukuncin shekara 14 a gidan yari.

  10. Elon Musk ya sake ɗarewa kan matsayinsa na mafi arziki a duniya

    Musk

    Fitaccen attajirin nan Elon Musk ya sake ɗarewa kan matsayinsa na mafi arziki a duniya inda yake da dukiyar da ta kai dala biliyan 187, ya kuma zarce Bernard Arnault na Faransa.

    Elon Musk ya kasance mamallakin kamfanin Tesla da ke ƙera motocin lataroni.

    Baya ga Tesla, Musk ne babban jami'in SpaceX, kamfanin ƙera jiragen roka kuma yana da hannun jari a shafin sada zumunci na Tuwita.

    A cewar wani rahoto na baya-bayan nan da Bloomberg Billionaires Index, ya fitar, ƙaruwar hannun jari da aka samu a Tesla ya taka rawa a sake komawarsa kan matsayinsa bayan da hannun jarin Tesla ya ƙaru da kashi 92 cikin 100.

    Bloomberg Billionaires Index yana fitar da jadawalin mutanen da suka fi arziki a kullum kuma ana bayyana yawan arzikinsu a ƙarshen kowace rana a New York.

    Yawan arzikin Musk ya yi ƙasa da sama da dala biliyan 200 tsakanin Nuwamba da Disambar shekarar da ta gabata, abin da aka bayyana a matsayin asara mafi girma da ya tafka a baya-bayan nan.

    A watan Aprilun 2022, Musk ya yi tayin sayen Tuwita kan $44 billion inda kuma ciniki ya faɗa a watan Oktoban 2022.

    Bayan da ya karɓi ragamar shugabancin Tuwita, Elon Musk ya rage sama da ma'aikata 3,700 kusan rabin ma'aikatan kamfanin.

    A baya-bayan nan Tuwita ya sanar da matakin rage ma'aikata karo na takwas kuma an sallami fiye da mutum 50 a ƙarƙashin jagorancin Musk.

  11. Mauritania ta yi kira ga ƙasashen Sahel su haɗa gwiwa don yaki da masu iƙirarin jihadi

    Mauritania

    Shugaban ƙasar Mauritania, Mohamed Ould Ghazouani, ya ce akwai bukatar kasashen yankin Sahel su kara hada kai wajen yaki da kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi.

    Duk da cewa Mauritania bata fuskanci mummunan tasirin hare-haren masu tsatsauran ra’ayi dake da alaka da kungiyar Al-Qaeda da kugiyar IS ba, amma tana bayar da gudunmawar dakaru ga rundunar tsaron hadin gwiwa ta G5 ta Sahel.

    A hirarsa da BBC, shugaban kasar Mauritania Ghazouani ya ce horar da dakarun muhimmin aiki ne a yaki da kungiyoyin masu ikirarin jahadi.

    Ya ce kasashen G5 Sahel na bukatar hadin gwiwa da juna da samar da makudan kudade.

  12. An yi zazzafar mahawara a taron ministocin ƙasashen G20

    G20

    An yi wata zazzafar mahawara a taron ministocin kasashen G20 kan batun mamayar da Rasha ta yi Ukraine.

    Indiya mai masaukin baki ta bayyana cewa rashin cimma matsayar da aka samu ba lallai ne a samu sanarwar hadin gwiwa game da taron ba.

    Firaminsitan Indiya Narendra Modi ya ce tattaunawarsu ta shafi batun yadda za’a laluɓo hanyoyin warware takaddamar:

    Ya ce dukkansu suna da matsaya da kuma burin ganin an warware wannan matsalar.

    Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken, ya ce tattaunawar ta mayar da hankali kaco-kan kan batun hare-haren da Rasha ta kaddamar kan Ukraine.

  13. Putin ya zargi Ukraine da yi wa ƙasarsa zagon ƙasa

    Putin

    Shugaba Vladimir Putin na Rasha yayi zargin kutsawar da wasu kwamandoji suka yi zuwa yankunan kasar Rasha da cewa ayyukan ta’addanci ne da Ukraine ta shirya.

    Tun da farko fadar Kremlin tayi ikirarin cewa, dakarun tsaronta suna kokarin kawar da abin da ta kira zagon ƙasa da Ukraine ke shiryawa, inda aka kaddamr da hare-hare kan wasu kauyuka biyu a kan iyakar kasar, tare da yin garkuwa da mutane.

    Mista Putin ya yi ikirarin cewa mayakan sun buɗe wuta kan wata motar fararen hula.

    Wani hoton bidiyo da ke yawo a yanar gizo ya nuna dakarun Ukraine a wani asibiti da ke yankin Rasha, sai dai Kyiv tayi watsi da rahoton inda ta bayyana shi da cewa wani salon tsokana ne daga Rasha.

  14. Museveni ya tattauna da Zelensky kan matsalar ƙarancin abinci

    Museveni

    Shugaba Yoweri Museveni na Uganda ya ce a baya-bayan nan ya tattauna da takwaransa na Ukraine Volodymyr Zelensky kan matsalar ƙarancin abinci a nahiyar Afirka.

    Mista Museveni ya bayyana haka ne a ranar Laraba yayin amsa tambayoyin 'yan jarida a wani taron zuba jari tsakanin Uganda da Afirka ta Kudu da aka gudanar a Pretoria.

    "Mun yi tattaunawa mai tsawo...sai dai, abin da na faɗa masa shi ne Uganda bata da matsalar abinci...amma wasu ƙasashe na da matsalar,'' in ji Museveni.

    "Amma ina son ya san cewa akwai wasu ƙasashen Afirka da suke da karfin tattalin arziki."

    Shugabannin biyu sun tattauna ta wayar tarho a ranar 22 ga watan Fabrairu, inda suka tattauna kan yiwuwar bunƙasa alaƙar ƙasashen biyu.

    Farashin man fetur da na abinci sun yi tashin gwauron zabo a faɗin duniya tun watan Fabrairun bara lokacin da Rasha ta mamaye Ukraine.

    Afirka ta dogara ne kacokan kan samar da hatsi daga ƙasashen biyu wanda a haɗe ke da kashi 29% na alkama da ake fitarwa a duniya.

  15. Barcelona da Real Madrid za su fafata a Copa del Rey

    Copa Del Rey

    Real Madrid za ta fafata da Barcelona a wasan farko na daf da karshe a Copa del Rey da za su kara a Santiago Bernabeu ranar Alhamis.

    Wannan shi ne karo na uku da za su fafata a tsakaninsu a bana, bayan da Real ta ci Barcelona 3-1 a gasar La Liga a Santiago Bernabeu ranar 16 ga watan Oktoba.

    Sai dai Barca ta doke Real 3-1 ranar 15 ga watan Janairu ta lashe Sifanish Super Cup a Saudi Arabia.

    Barcelona za ta buga wasan, bayan da Manchester United ta fitar da ita daga Europa League da cin 4-3 gida da waje.

    Haka kuma kungiyar Nou Camp ta yi rashin nasara a hannun Almeria a La Liga a karshen mako, karo na biyu da ta yi rashin nasara a gasar a kakar nan.

    Ita kuwa Real Madrid ta tashi 1-1 a wasan hamayya da Atletico Madrid a dai fafatawar hamayya a babbbar gasar tamaula ta Sifaniya.

  16. ECOWAS ta taya Tinubu murnar cin zaɓe

    Kungiyar Bunƙasa Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka ta taya Bola Tinubu murnar cin zaɓe da ya yi a zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar a ranar Asabar.

    A cikin wani sako da ECOWAS ɗin ta wallafa a shafinta na twita, shugabanta Janar Umaru Sissoco Embalo, ya buƙaci dukkan masu ruwa da tsaki da su ɗaɓɓaka zaman lafiya a ƙasar.

    Ya kuma yi kira ga jam'iyyun da suke da ja a kan zaɓen, da su bi hanyoyi da suka kamata wajen bin hakkinsu.

    View more on twitter
  17. Buhari na ziyara a Maiduguri

    ...

    Shugaba Muhammadu Buhari na wata ziyara ta kwana ɗaya a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

    Buhari ya isa Maiduguri ne da misalin karfe 11 na safe, inda yake tare da rakiyar manyan jami'an gwamnati.

    Shugaban ya samu tarba daga gwamnan jihar Babagana Zulum.

    Ana sa ran zai gana da 'yan kasuwar da suka rasa shagunansu a wata gobara a babbar kasuwar jihar da kuma kaddamar da tashar samar da wutar lantarki.

  18. Afenifere ta yi Alla-wadai da zaɓen Tinubu

    ..

    Pa Ayo Adebanjo, shugaban kungiyar Yarabawa ta Afenifere, ya mayar da martani kan ayyana ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa.

    Yayin da yake magana a wata tattaunawa ta wayar tarho da BBC, Adebanjo ya bayyana zaɓen da ya bai wa Tinubu nasara a matsayin mai cike da kura-kurai.

    Ya ce sakamakon zaɓen shugaban ƙasa ba abu ne da za a amince da shi ba, kuma hakan na iya haifar rikici a ƙasar.

    Adebanjo ya ce gazawar da INEC ta yi na amfani da na'urar BVAS a rumfunan zaɓe kamar yadda ta yi alkawari tun da farko, ya nuna cewa wasu sun tsara yadda zaɓen zai gudana da kuma ɗan takara da suke so ya yi nasara.

    Ya ƙara da cewa a iya saninsa, shi dai ba a gudanar da zaɓe a ƙasar ba a ranar Asabar ɗin da ta gabata.

    “Wannan ba zaɓe ba ne kuma duk mun san haka, a fili ta ke cewa an tafka maguɗi kuma hakan ba abin yarda ba ne.

    "Hakan ba zai yiwu ba, su waye ke aika sakon taya murna ga zaɓabɓen shugaban ƙasa? Har yanzu ba mu gudanar da zaɓen shugaban ƙasa ba."

    Adebanjo ya bayyana cewa ba jam’iyyarsa ta siyasa ce kaɗai ta yi Allah-wadai da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa ba, har ma da masu sa-ido na cikin gida da na waje da suka shaida yadda zaɓen ya gudana da ma ɗaukacin jam’iyyun adawa ba su ji daɗin yadda zaɓen ya gudana ba.

    Ya kuma yi nuni da cewa maguɗin zaɓe na iya jefa ƙasar cikin rikici kamar yadda wani tsohon shugaban ƙasar ya yi kira da a soke zaɓen.