Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza da Umar Mikail

time_stated_uk

  1. Sai da safenku

    Ƙarshen rahotannin ke nan a wannan shafi na kai-tsaye.

    Mu haɗe gobe da safe domin kawo muku wasu sababbi.

    Umar Mikail ne ke cewa ku duba ƙasa don karanta rahotannin da muka kawo a yau Litinin.

  2. Mu da gwamnati muke amfana da matsalar tsaro - Ƙasurgumin ɗan fashin daji

    Abu Sani

    Wani ƙasurgumin ɗan bindiga mai satar mutane a Jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya ya ce matsalar rashin tsaro na ƙara ta'azzara ne a arewacin ƙasar saboda an mayar da lamarin na neman kuɗi.

    Abu Sani wanda shi ne ya jagoranci sace ƴan matan sakandaren gwamnati ta garin Jengeɓe a bara, ya faɗi hakan ne a wani shiri na musamman na binciken ƙwaƙwaf da BBC ta gudanar kan ayyukan ƴan bindigar.

    A yau Litinin ne BBC ta saki shirin na Africaa Eye a shafukanta na sada zumunta cikin Hausa da Turanci.

    "An mayar da abin neman kuɗi a wannan ɓangare, kowa kuɗi yake nema,shi ya sa harkoki suke lalacewa, tun daga manyan har zuwa ga ƙananan," in ji ɗan bindigar.

    "Su kuma jami'ai su ma gwamnati idan ana rikici ana tura mata da kuɗi, ka ga ta wannan ɓangaren suna samu ke nan.

    "Mu ma ta nan duk da dai za a zubar da jini a yi rashe-rashe, amma kuma a yi ta yi haka nan."

    A cikin hirar ya kuma bayyana cewa sai da gwamnatin Jihar Zamfara ta ba su fansar naira miliyan 60 kafin su saki ƴan matan sakandaren Jageɓe da suka yi garkuwa da su.

    Sai dai gwamnatin ta daɗe da musanta cewa ta bayar da kuɗi kafin a sako ƴan matan.

    Kuna iya latsa nan don karanta cikakken labarin da kallon bidiyon:

  3. Ministan sufuri na Najeriya ya yi alƙawarin kuɓutar da sauran fasinjojin jirgin ƙasa

    Mu'azu Jaji Sambo

    Ministan Sufuri na Najeriya Injiniya Mu'azu Jaji Sambo ya sha alwashin fara aiki gadangadan don ceto mutum 43 da suka rage a hannun 'yan bindigar da suka sace su a jirgin ƙasa na Abuja zuwa Kaduna da zarar ya daidaita zamansa a ofis.

    Ministan ya bayyana hakan ne yayin da yake yi wa 'yan uwan mutanen jawabi a ƙofar ma'aikatarsa bayan sun gudanar da zang-zanga a yau Litinin.

    "Akwai abubuwan da ba zai yiwu a faɗa a bainar jama'a ba, amma ina so ku ba ni loƙci. Ku bari na fara aiki gadangadan a ofishin nan, ni kuma na yi muku alƙawarin wannan ce matsalar da zan fara magancewa cikin ikon Allah," a cewarsa.

    Tun a ranar 7 ga watan Yuli aka rantsar da Mu'azu Jaji a matsayin ministan sufuri bayan an sauya masa muƙami daga ƙaramin ministan ayyuka.

    Yayin zanga-zangar da suka gudanar da safiyar Litinin ɗauke da alluna masu hotunan Shugaba Muhammadu Buhari, mutanen sun yi kira ga gwamnatin Najeriya ta taimaka ta ceto 'yan uwansu.

    View more on twitter
  4. Shugaba Muhammadu Buhari zai tafi Laberiya

    Shugaba Buhari

    Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya zai tafi Laberiya a gobe Talata 26 ga watan Yulin 2022.

    Sanarwar da fadar shugaban ƙasar ta fitar mai ɗauke da sa hannun mai taimaka wa Buhari kan yaɗa labarai Malam garba Shehu ta ce, tafiyar na nuna muhimmancin da ke akwai na tsaro da zaman lafiyar Laberiya da sauran ƙasashen Afirka ta Yamma.

    Bulaguron na Shugaba Buhari ya zo daidai ne da ranar da Laberiya ke bikin murnar shekara 175 da samun ƴancin kanta.

    Shugaba Buhari ne babban baƙo na musamman a bikin har ma zai gabatar da jawabi.

    Sanarwar ta ce bulaguron na Laberiya na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta samun matsaloli na rushewar dimokrɗaiyya da juyin mulki a yankin Afirka ta Yamma.

    A shekara mai zuwa ta 2023 ne za a gudanar da zaɓuka a Najeriya da Laberiya da kuma Saliyo, kuma ana sa ran Shugaba Buhari zai yi wa ƴan Laberiya jawabi kan muhimmancin sahihin zaɓe marra magudi.

    Kazalika fadar shugaban Najeriyar ta ce, Buhari zai jaddada wa ƴan ƙasar muhimmancin girmama dokar ƙasa a baki ɗayan yankin.

    “Idan ba a bin dokar ƙasa, ba za asamu tsaro da zaman lafiya da ci gaba ba,” in ji sanarwar.

    Saƙon Buhari na tafiyar ya ce zaman lafiya da tsaron Laberiya da Saliyo na da muhimmanci ga Najeriya.

  5. 'Ƴan uwanmu ne suka karɓo mu daga hannun 'yan bindiga'

    Video content

    Video caption: Latsa hoton sama ku kalli bidiyo

    Ɗaya daga cikin fasinjojin jirgin ƙasa na Kaduna zuwa Abuja da 'yan bindiga suka saki ranar Litinin ya ce 'yan uwansu ne suka gana da masu garkuwa da su don kuɓutar da su.

    Hassan Usman wanda aka gani a bidiyon da 'yan bindigar suka fitar ranar Lahadi yana neman ɗauki daga gwamnatocin ƙasashen waje, na cikin mutum uku da aka sako a ranar Litinin.

    Ya ce tun ranar Juma'a 'yan uwan nasa suka yi yunƙurin shiga daji wajen masu garkuwa da su amma sai jami'an tsaro suka hana su.

    "Sai kuma a jiya [Lahadi] suka sake komawa kuma Allah ya kuɓutar da mu cikin aminci," in ji shi. Sai dai ya ce ba zai iya bayyanawa ba game da ko an biya kuɗin fansa kafin sakin nasu.

    Hassan ya tabbatar da cewa mutanen da suka rage a dajin sun kai aƙalla 40, yana mai cewa su 64 aka kwasa daga jirgin a ranar 28 ga watan Maris da ya gabata - lokacin da suke kan hanyar zuwa Kaduna daga birnin tarayya Abuja.

  6. Ba ma jin dadin yadda alƙalai ke sakin mutanen ake zargi da manyan laifuka - 'Yan sandan Najeriya

    Kwamashinan 'yan sanda na Kano Samaila Dikko

    Rundunar ‘yan sandan a Najeriya ta koka dangane da bangren shari’a ke sakin wadanda suke zarginsu da aikata manyan laifuka da suke gabatar don a yi musu hukunci.

    Yan sandan dai sun ce duk da irin wahalar da suke sha wajen kamo irinwadan nan mutane da ake zargi da aikata laifin, amma bayan wani lokaci sai a bayar dasu beli, wanda al’umma ke ganin laifinsu wajen rashin yin abin da ya kamata.

    Kwaminshin ‘yan sandan Kano Sama’ila Dikko ne dai ya bayyana hakan a wata hira da BBC jim kadan bayan gabatar da jawabinsa na karshe a matasyin kwamishinan yan sandan jihar.

    Ku latsa hoton da ke ƙasa don saurraon rahoton da Khalifa Shehu Dokaji ya aiko mana daga Kano:

    Video content

    Video caption: Hira da Kwaminshin ‘yan sandan Kano Sama’ila Dikko
  7. Tarayyar Turai na son maye gurbin gas ɗin Rasha da na Najeriya

    Putin

    Ƙungiyar Tarayya Turai ta ce za ta maye gurbin amfani da gas ɗin Rasha da na Najeriya, a yayin da ake tsaka da yaƙin Ukraine da Rasha, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana.

    Mataimakin darakta janar na sashen kula da makamashi na kwamitin Tarayyar Turai, Matthew Balwdin, ya je Najeriya a ƙarshen makon da ya gabata, inda ya gana da jami'an ƙasar.

    An shaida masa cewa Najeriya na ƙarfafa tsaro a yankin Neja Delta, inda a can ne ake samar da fetur din.

    Jami'an Najeriya sun gaya masa cewa an sake bude bututun gas da yake taso daga kudu zuwa arewa, wanda zai taimaka wajen faɗaɗa fitar da gas zuwa Turai.

    A yanzu haka dai, EU na samun kashi 14 cikin 100 na iskar gas dinta daga Najeriya, amma akwai alamun yawan zai nunka, kamar yadda Mr Baldwin ya shaida wa Reuters.

    Ƙasasehn yammacin duniya sun ƙaƙaba wa Rasha takunkumai kan fetur da gas ɗinta saboda kutsen da ta yi wa Ukraine.

  8. Rasha ta tuhumi sojojin Ukraine 92 da aikata laifukan yaƙi

    Rasha ta tuhumi sojojin Ukraine 92 da aikata laifukan yaƙi.

    Shugaban kwamitin bincike na Rasha Alexander Bastrykin ya shaida wa wata jaridar gwamnatin ƙasar cewa akwai wasu kusan mutum 100 da ake nema ruwa a jallo.

    Ya kuma zargi ma'aikatan kiwon lafiya na Ukraine ba tare da hujja ba, cewa suna samar da makaman ƙare dangi.

    Mr Bastrykin ya bayar da shawarar kafa wata kotu ta musamman tare da samun goyon bayan kasashe da suka hada da Bolivia da Iran da Syria -- ƙawayen Rasha.

    Babu wani martani kawo yanzu daga ɓangaren Ukraine.

    Akwai kotun hukunta manyan laifuka ta duniya da ke gudanar da bincike laifukan yaƙi da ake zargin Rasha da aikatawa a Ukraine.

    Zargin da Moscow ta musanta aikatawa.

  9. Tarayyar Turai na son maye gurbin gas din Rasha da na Najeriya

    .
    Image caption: Tarayyar Turai na samun kashi 14 cikin 100, na gas din da take amfani da shi daga Najeriya.

    Kungiyar Tarayyar Turai na wani yunkuri na maye gurbin gas din da take saya daga kasar Rasha, da na Najeriya sakamakon yakin da Rasha take yi a Ukraine, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.

    A wata ziyara da ya kai Najeriya mataimakin babban daraktan hukumar gudanarwa ta Tarayyar Turai Matthew Balwdin ya ce, ya ziyarci Najeriya ne domin tattaunawa da jami'an kasar don kulla yarjejeniyar.

    A halin da ake ciki dai, tarayyar turai na samun kashi 14 cikin 100, na gas din da take amfani da shi daga Najeriya.

    Shugabannin kasashen Turai sun sanya wa Rasha tarin takunkumai saboda mamayar da ta yi wa Ukraine

    Kungiyar ta EU dai na son rage yawan gas din da take shigarwa daga Rasha da kashi biyu cikin uku.

  10. Gwamnatin Najeriya ta bayar da umarnin rufe Sakandiren Kwali

    .
    Image caption: .

    Ma'aikatar ilimi ta Najeriya ta bayar da umarnin rufe makarantar sakandiren Kwali da ke Abuja babban birnin kasar.

    A wata sanarwa da jami'in hulda da jama'a na ma'aikatar Ben. Bem Goong ya fitar, ya ce Ministan ilimi na kasar Malam Adamu Adamu ne ya bayar da umarnin.

    Ya ce rufe makarantar ya zama wajibi ne bayan da 'yan bindiga suka kai hare-hare a kauyukan Sheda, da Lambata da ke makwabtaka da makarantar, abinda ke zama barazana ga makarantar.

    Dama dai tun da safiyar ranar Litinin ne iyayen yara suka fara kwashe 'ya'yansu bayan da suka ce sun samu kiran waya daga hukumomin makarantar cewa su zo su kwashe 'ya'yansu, saboda fargabar da hukumomin makarantar ke ciki, kan wasu hare-hare da 'yan bindiga suka kai wa wasu yankuna da ke makwabtaka da makarantar.

  11. Ministan harkokin wajen Rasha na ziyara a Afirka

    Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov na wata ziyara a kasar Congo-Brazzaville, a wani yunkuri da Rasha ke yi na farfado da alaka da kasashen Afirka, bayan da dangantakarta da kasashen Turai ta fara yin tsami.

    Ana sa ran Mista Lavrov zai gana da shugaban kasar Denis Sasou-Nguesso domin tattauna batutuwan da suka shafi tasirin da yakin Ukraine ke yi ga kasashen Afrika ta fuskar karancin abinci, kamar yadda shafin intanet na mujallar Brazza ta ruwaito.

    Nan gaba kadan ne kuma ake sa ran Mista Lavrov zai wuce zuwa Uganda domin ganawa da shugaban kasar Yoweri Museveni.

    Sannan kuma Ministan zai wuce zuwa kasar Habasha, a kokarin da kasar ke yi na karbar bakuncin taron hadin gwiwa tsakanin Rasha da nahiyar Afirka da za a gudanar a birnin Addis Ababa tsakanin watan Oktoba zuwa Nuwamba.

  12. An fara kwashe daliban Sakandiren Kwali saboda fargabar kai hari

    .
    Image caption: .

    Iyayen dalibai na kwashe 'ya'yansu daga Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Kwali a Abuja babban birnin Najeriya, saboda fargabar hare-haren 'yan bindiga.

    Jaridar daily Truyst a Najeriya ta ruwaito cewa tun da sanyin safiyar ranar Litinin iyayen daliban ke cincirindo zuwa harabar makarantar da ke kan babban titin Abuja zuwa Lokaja, domin kwashe yaransu.

    Iyayen yaran sun bayyana cewa sun samu kiran waya ne daga hukumomin makarantar cewa su zo su kwashe 'ya'yansu, saboda fargabar da hukumomin makarantar ke ciki, kan wasu hare-hare da 'yan bindiga suka kai wa wasu yankuna da ke makwabtaka da makarantar.

  13. 'Yan tawayen M23 sun kashe mutum 29 cikin wata guda a DR Kongo

    Kungiyar kare hakkin bil-adama ta Human Rights Watch, ta ce 'yan tawayen M23 ta kashe akalla fararen hula 29, a gabashin Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo cikin watan da ya gabata.

    Shaidu sun ce a wani hari guda daya da kungiyar ta kai yankin Kivu, ta kashe mutum 17, wadanda take zargi da bai wa jami'an tsaron kasar bayanai game da ayyukan kungiyar.

    Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo na zargin makwabciyarta Rwanda da goya wa kungiyar 'yan tawayen baya, zargin da kasar Rwanda ta sha musantawa.

    Kungiyar ta M23 ta fara jan hankalin duniya a shekarar 2012, kafin dakarun hadin gwiwwa na kasar da na Majalisar Dinkin Duniya su tilasta mata ficewa daga kasar. To amma ta dawo da ayyukanta cikin watan Nuwamban bara

  14. Cutar Marburg ta kashe karin mutum guda a Ghana

    .
    Image caption: .

    Hukumomin lafiya a Ghana sun ce wani karin mutum guda ya mutu sakamakon cutar Marburg da ta bulla a kasar.

    Mutumin, wanda dan uwa ne ga mutane biyu na farko da cutar ta fara kashewa a kasar, ya rasu ne bayan da gwajin da aka yi masa ya gano cewa yana dauke da cutar.

    Da wannan dai adadin mutanen da cutar Marburg ta kashe a kasar sun kai uku.

    Hukumar lafiya ta duniya ta gargadi kasashen da ke makwabtaka da kasar da su zama cikin shirin ko-ta-kwana game da barkewar cutar a kasashensu.

  15. Mutum 17 sun mutu bayan kifewar kwale-kwale a Haiti

    .
    Image caption: .

    Gwamnatin kasar Haiti ta ce akalla mutum 17 ne suka mutu bayan da girjin ruwan da suke ciki ya kife a tekun kasar

    Firaministan kasar Philip Davis ya ce ana tunanin wadanda ke cikin jirgin sun taso ne daga Haiti zuwa Miami da ke jihar Florida ta Amurka.

    'Yan sanda sun ce kwale-kwalen ya kife ne, kilomita 11 bayan tashinsa daga tsibirin Providence

    Al'umar kasar da dama na jefa rayuwarsu cikin hatsari a kokarinsu na shiga Amurka ta kwale-kwale, domin guje wa kuncin rayuwa da kasar ke fuskanta.

  16. Kotun Masar na so a yada zartar da hukuncin kisa kan wani mutum kai-tsaye a talbijin

    .
    Image caption: A kasar Masar ba a yada aiwatar da hukuncin kisa a gidajen talbijin

    Wata kotu a Masar ta nemi a yada aiwatar da hukuncin kisa kai-tsaye da aka yanke wa wani mutum da ya kashe wata daliba kasar.

    'Yan kasar da dama sun kadu bayan da aka yada bidiyon dake nuna Mohammed Adel, lokacin da yake daba wa wata daliba mai suna Nayera Ashraf wuka, a wajen jam'iar da dalibar ke karatu, saboda ta ki amincewa da bukatunsa.

    A wata wasika da kotun ta aike wa majalisar dokokin kasar, kotun ta nemi amincewar majalisar domin a yada zartar da hukuncin kisan kan mutumin mai shekara 22, kai-tsaye a gidan talbijin domin hakan ya zama izina.

    A kasar Masar dai, ba a yada aiwatar da hukuncin kisa a gidajen talbijin, wadanda galibi ake yanke musu hukuncin ta hanyar rataya.

  17. Mutum 33 sun mutu bayan da motarsu ta fada cikin kogi

    Akalla mutum 33 ne suka mutu, wasu da yawa suka jikkata lokacin da wata mota makare da fasinjoji ta fada cikin kogin Nithi a kasar Kenya.

    Hukumomin kasar sun an samu nasarar kubutar da mutum 10, a hatsarin da ya auku ranar Lahadi da daddare.

    Motar dai na kan hanyarta ta zuwa birnin Mombasa daga garin Meru.

    'Yan sanda sun ce binciken farko da aka gudanar ya gano cewa burkin motar ne ya shanye lokacin da take tsaka da gudu.

    Ana ci gaba da aikin ceto, yayin da ake tunanin adadin wadanda suka mutu zai iya karuwa.

    A 'yan shekarun nan dai ana samun yawaitar hatsarin mota a titunan kasar Kenya.

  18. Ba zan taba sassautawa wajen murkushe 'yan ta'adda ba - Buhari

    .
    Image caption: .

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kara nanata aniyar gwamnatinsa na kawo karshen matsalar tsaron da kasar ke fuskanta, yana mai cewa ko kadan bai zai raga wa 'yan bindiga da 'yan ta'addan da ke kai hare-hare a fadin kasar.

    A wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu, ya fitar ranar Lahadi, ya ce manyan hafsoshin tsaron kasar na iya bakin kokarinsu wajen ganin an kawo karshen matsalar 'yan bindiga a kasar.

    Ya kuma jajanta wa tsohon shugaban jam'iyyar PDP, Adamu Muazu, saboda kashe dan uwansa da 'yan bindiga suka yi tare kuma da kame 'yar uwarsa.

    Yayin da yake bayyana 'yan bindigar a matsayin makiya al'uma, Shugaba Buhari ya ce ya kadu matuka da wannan kisan

    Ya kara da cewa ''Na yi matukar kaduwa da jijn labarin kashe dan uwanka, tare da kama 'yar uwarka. Wannan masifa kullum karuwa take yi a kasar nan. Na sani kuna cikin halin damuwa, ina taya ku bakin-ciki''

    ''Matsalar tsaro ita ce babban abin da na sa a gaba, na kuma umarci manyan hafsoshin tsaron kasar da su yi iya bakin kokarinsu, domin kawo karshen wannan matsala da kasarmu ke ciki''. In ji Buhari

    Wadannan kalaman na zuwa ne bayan 'yan bindigar da suka sace gomman fasinjojin jirgin kasan nan na Abuja zuwa Kaduna, tun ranar 28 ga watan Maris din da ya gabata, sun sake fitar da wani sabon hoton bidiyo da ke nuna mutanen da ake garkuwa da su cikin mummunan yanayi.

    A cikin bidiyon mai tsawon kusan minti goma sha daya, an ga 'yan bindigar na lakada wa fasinjojin maza dukan tsiya da ita ce.

  19. Barkanmu da warhaka

    Abdullahi Bello Diginza ne ke muku barka da safiyar Litinin, 25 ga watan Yulin 2022. A yau ma za mu ci gaba da kawo muku labarai da rahotanni kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya ziyartar shafinmu naFacebookdaTwitterda kuma naInstagramdomin bayyana ra'ayoyinku kan irin labaran da muke wallafawa ko kuma tafka muhawara a kai.