Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Muhammad Annur Muhammad da Ahmad Tijjani Bawage

time_stated_uk

  1. Mu kwana lafiya

    Nan muka zo karshen rahotanni a wannan shafi na kai tsaye, sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.

    Ahmad Bawage ke cewa sai da safen ku.

  2. Jirgin Amurka mara matuki ya faɗa cikin teku

    Jirgin Amurka mara matuki

    Wani jirgin sama mara matuki na Amurka da ke shawagi a sararin samaniya ya faɗa a cikin tekun Black Sea a wani alamari da ya shafi wasu jiragen saman yaki Rasha biyu.

    Amurka da Rasha sun yi bayanai masu karo da juna game da abinda ya faru.

    Rundunar sojin Amurka ta ce jiragen saman Rasha sun zuba man fetur a kan jirgin saman mara matuki kafin daya daga cikinsu ya lalatanaurar jirgin abinda ya sa ya fada cikin tekun.

    Wakilin BBC y acekakakin fadar White house ya bayyana harina matsayinmatakin da ke cike da sakaci da rashin kwarewa

    Sai dai rundunar sojin Rasha ta musantacewa cewa daya daga cikin jiragenyakinta neya kai wa jirgin hari tana mai cewa jirgin samanmara matukin ya samumatsala nekafinya fada a cikin ruwa

  3. Shugaba Biden ya sa hannu kan dokar taƙaita amfani da bindiga

    Bindiga

    Shugaba Biden ya sa hannu kan dokar takaita amfani da bindiga domin rage yawan harbe harben da ake yi a Amurka.

    An tsara dokar ta yadda za ta bukaci a tsaurara matakan bincike kafin a ba da damar siyan bindiga. Ya zuwa yanzu dokokin sun bambanta daga Jiha zuwa jiha.

    Shugaba Biden ya sanar da haka ne yayin ziyarar da ya kai wurin da aka kashe mutane da dama a California a watan janairun daya gabata.

    Mutum11 aka harbe bayan an kamala shagulgulan sabuwar shekarar Luna

  4. Meta zai sake korar ma'aikata 10,000

    Mark Zuckerberg

    Kamfanin Meta wanda shi ne ya mallaki shafukan sada zumunta na Facebook da Instagram da kuma WhatsApp, ya sanar cewa zai sake korar ma’aikata dubu goma.

    Wannan shi ne karo na biyu da kamfanin ke ɗaukar matakin korar ma’aikata da dama a baya-baya nan.

    Wakiliyar BBC ta ce kamfanin Meta ya kori ma’aikata dubu goma sha ɗaya a cikin watanni huɗu da suka gabata, inda a yanzu ya sanar cewa zai sake sallamar dubban ma’aikatan sauran manyan kamfanoni fasaha irinsu Amazon da Microsoft suma sun kori dubban ma’aikata.

    Kamfanoni fasaha sun samu matukar ci gaba a lokacin kullen annobar korona. Sai dai fargabar da aka nuna akan durkushewar tattalin arzikn duniya ta sa mutane sun rage amfani da kayayakin fasaha abinda ya sa kamfanonin suka dauki matakin korar ma’aikata.

  5. 'Mun daƙile yunƙurin kutse ta intanet har sau miliyan 13 lokacin zaɓe'

    Kwamfuta

    Hukumomi a Najeriya sun ce ƙasar ta daƙile yunƙurin kutse ko hare-hare a kan hanyoyin sadarwa na intanet har kimanin miliyan 13 a lokacin zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar.

    Babban daraktan hukumar bunƙasa fasahar sadarwa ta Najeriya, wato NITDA, Kashifu Inuwa AbdulLahi, shi ya bayyana haka a lokacin da yake tattaunawa da BBC, inda ya ce an samu nasarar ce sakamakon wasu cibiyoyi da aka kafa don yaƙi da kutsen ta intanet da kuma wani kwamiti na musamman da aka kafa da ya ƙunshi hukumomin NITDA da NCC da Galaxy Backbone.

    Ya ce a ranar zaɓe kaɗai sun daƙile yunƙurin kutse har miliyan shida da dubu ɗari tara.

    Daraktan na NITDA ya ce an yi ƙoƙarin yin kutsen daga cikin gida da kuma ƙasashen waje saboda suna amfani da wasu manhajoji.

    Ya ce kutsen ya shafi shafukan intanet na hukumomi da na kamfanoni masu zaman kansu da kuma na hukumar zaɓe wanda shi ne aka fi kai wa hari saboda zaɓe.

    Ya ce babban hatsari da ke tattare da yin kutsen, shi ne hakan zai sa a deɓi bayanai da canza wasu da kuma sanya wa mutane shakku kan amincewa da sahihan bayanai.

  6. Ƴan sanda sun dakatar da masu zanga-zanga isa fadar shugaban ƙasa a Sudan

    Ƴan sanda sun watsa wa masu zanga-zangar hayaki mai sa hawaye
    Image caption: Ƴan sanda sun watsa wa masu zanga-zangar hayaki mai sa hawaye

    Ɗaruruwan masu zanga-zanga ne suka fito kan tituna a birnin Khartoum na ƙasar Sudan a yauTalata, inda suka nufi fadar shugaban ƙasar.

    Sai dai ƴan sanda sun harba musu hayaki mai sa hawaye tare da hana su isa fadar.

    Matasa maza da mata ne suka fito ɗauke da tutoci masu nuna sunayen waɗanda aka kashe a zanga-zangar adawa da ci gaba da mulkin soja.

    Wasu allunan kuma na ɗauke da sakonnin cewa za a ci gaba da zanga-zangar har sai an samu mulkin farar hula.

    Mahalarta zanga-zangar da dama sun fito ne daga birane uku na babban birnin ƙasar - Omdurman, Arewacin Khartoum da kuma birnin Khartoum.

    Zanga-zangar ta zo ne a matsayin bikin kafa sabbin kungiyoyin kwadago a ƙasar.

    An soma zanga-zangar ne tun watan Disamban 2018, inda kwararru suka jagoranci gudanar da ita - waɗanda suka haɗa da likitoci da 'yan jarida da lauyoyi da malamai da kuma injiniyoyi.

    Sun kara tsananta ta ne bayan da Janar Abdul Fattah al-Burhan, shugaban ƙasar kuma shugaban majalisar mulkin ƙasar ya yi juyin mulki a shekarar 2021 wanda ya kawo karshen wa'adin mulkin dimokuraɗiyya na shekaru biyu.

    Wata sabuwar yarjejeniya da ke da nufin komawa mulkin farar hula, wadda aka rattaɓa wa hannu a karshen shekarar da ta gabata, ta fuskanci shakku daga masu fafutukar tabbatar da dimokuraɗiyya.

    Some demonstrators hit back at police with stones
    Image caption: Wasu masu zanga-zanga sun mayar da martani ta hanyar jifan ƴan sanda da duwatsu
  7. Morocco na son karɓar bakuncin gasar Kofin Duniya

    Piers Edwards

    Morocco na fatan zama kasa ta biyu a Afirka da za ta karɓi bakuncin gasar kwallon kafa ta duniya, inda ta bayyana aniyar ta a ranar Talata na neman shiga gasar cin kofin duniya ta 2030. Wannan dai shi ne karo na shida da ƙasar ke da burin karɓar bakuncin gasar.

    Wakilin BBC Piers Edwards ya ce a wannan karon za ta haɗa kai da Spain da Portugal.

    A watan da ya gabata, ƙasashen Argentina da Chile da Paraguay da Uruguay, sun gabatar da bukatar haɗaka ta karɓar bakuncin gasar tare. Suna fatan karɓar bakuncin gasar shekaru 100 bayan gudanar da gasar ta farko a Uruguay.

    Morocco ta samu ɗimbin magoya bayanta a faɗn Afirka da ma duniya baki daya, saboda rawar da ta taka a gasar cin kofin duniya da aka yi a Qatar a bara, inda ta zo ta hudu kuma ta zama ta farko a Afirka.

    A watan Yuni ne tsarin ba da izini na hukumar zai fara kuma za a jira na aƙalla wasu watanni 13 bayan haka don gano ko Maroko za ta yi maraba da duniya zuwa ga ƙasarta.

    A shekarar 2010 ne aka gudanar da gasar cin kofin duniya ta farko a Afirka a Afirka ta Kudu.

    View more on twitter
  8. An kuɓutar da mata 11 da aka yi niyyar safararsu zuwa Libya

    NAPTIP

    Hukumar yaƙi da fataucin bil-Adama ta Najeriya ta ce tana gudanar da bincike kan lamarin da ya kai ga safarar wasu mata 'yan Najeriya 11 daga ƙasar.

    An ceto 'yan matan ne a makwaɓciyar ƙasar Jamhuriyar Nijar lokacin da wata ƙungiyar masu safarar mutane ke niyyar jigilar su zuwa ƙasar Libya.

    Ƴan matan da suka kasance dukkaninsu matasa, an dawo da su gida Najeriya tare da miƙa su ga hukumar hana fataucin mutane ta kasa NAPTIP reshen Sokoto.

    Kwamandan NAPTIP na shiyyar Sokoto, Abubakar Tabra ya shaida wa BBC cewa jami'an hukumar kula da shige da fice ta ƙasa reshen Illela ne suka karɓi 'yan matan a karshen makon da ya gabata, inda ya ce a yanzu sun soma bincike da nufin kamo waɗanda ake zargi da safarar ƴan matan.

    Ya kuma ce ana kuma kokarin bincike don gano 'yan uwan ƴan matan don sake haɗa su da iyalansu.

    Bayanan da aka tattara sun nuna cewa waɗanda abin ya rutsa da su sun fito ne daga kudancin Najeriya.

    Rahotanni sun ce an sace musu wayoyinsu da kayayyakinsu a cikin dazukan Jamhuriyar Nijar, inda waɗanda suka yi safararsu suka yi watsi da su, kafin jami’an ‘yan sandan Nijar ɗin su kuɓutar da su tare da miƙa su ga jami’an shige da fice na Najeriya da ke kan iyaka.

  9. Saudiyya za ta ɗauki mata sama da 80 a matsayin direbobi a filayen jirgin sama

    Transport system

    Gwamnatin Saudiyya ta ce za ta ɗauki hayar mata sama da 80 a matsayin direbobi a manyan filayen jirgin sama na ƙasar guda huɗu.

    Filayen jirgin sun haɗa da na Khalid da ke Riyadh da na Sarki Abdulaziz a Jeddah da na Sarki Fahd da ke birnin Dammam da kuma na Yarima Muhammad da ke Madinah.

    Gwamnatin ƙasar ta ce hakan na cikin wani tsari da hukumar kula da sufuri ta ƙasar ta kaddamar a ranar Lahadi tare da haɗin gwiwar ma'aikatar albarkatun ƙasa da ci gaba, wanda aka yi domin sama wa mata aiki a bangaren sufuri, kamar yadda jaridar Al-Watan ta ruwait.

    Ta ce tsarin ya haɗa da kirkiro da wani shiri da zai horar da matuka motocin da kuma bayar da taimakon agaji da sauransu. Hukumar ta ce tsarin zai kuma taimaka wajen ci gaban ɓangaren sufuri da yanda ake kula da fasinjoji don tabbatar da ɗorewar fannin.

  10. Magoya bayan Imran Khan sun yi artabu da ƴan sanda

    Imran Khan supporters clashed with police

    Magoya bayan jagoran 'yan adawa na Pakistan Imrah Khan, sun yi artabu da ƴan sanda a wajen gidansa lokacin da suka yi yunkurin kama shi bayan da wata kotu ta bayar da umarnin yin haka.

    Ƴan sandan sun harba hayaki mai sa kwalla don tarwasa dandazon mutane waɗanda suka yi jefa duwatsu kan jami'an.

    A wani sakon bidiyo, Imran Khan ya bukaci magoya bayansa da su fito daga gidajensu domin ƙwatar yancinsu ko da an kai ga kama shi.

    Hotuna da jam'iyyarsa ta watsa, sun nuna hayaki mai sa kwalla na faɗa wa kan gidan Imran Khan.

    Tsohon Firaministan dai na fuskantar tuhuma kan sayar da wata kyauta da aka bai wa gwamnati lokacin da yake kan mulki.

    Sai dai ya ce tuhumar na da alaƙa da siyasa.

  11. EFCC ta ƙama mutum 21 da ake zargi da zamba ta intanet a Abuja

    EFCC Nigeria/Twitter

    Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya EFCC, ta ce ta kama mutum 21 da ake zargi da aikata zamba ta intanet a Abuja.

    A wani sako da EFCCn ta wallafa a shafinta na twita, ta ce ta kama mutanen ne a unguwannin Kubwa da Lugbe bayan samun bayanan sirri kan ayyukan da suke aikatawa.

    Ta ce ta gano manyan wayoyin salula na zamanai guda 25 da motoci ƙirar Mercendes da kuma kwamfutocin tafi-da-gidanka guda uku a hannun waɗanda take zargin.

    EFCC ɗin ta kara da cewa za a tura mutanen zuwa kotu da zarar an kammala bincike.

    View more on twitter
  12. Indonesia na shirin haramta wa 'yan yawon buɗe ido amfani da babura

    Indonesia

    Mahukunta a birnin Bali na ƙasar Indonesia sun ce za su taƙaita wa 'yan yawon buɗe idanu amfani da babura waɗanda suke kai ziyara tsibirin sakamakon ƙaruwar karya dokokin tuƙi.

    BBC ta gano cewa dokokin da masu yawon bude idon suke karyawa sun haɗa da rashin amfani da hular kwanu ko tuki cikin maye da kuma tuki ba tare da lasisi ba.

    Ƴan sanda sun ce masu yawon bude ido fiye da 170 ne suka karya dokokin tuki a watan Fabairarun da ya gabata da kuma watan Maris din nan.

    Gwamnan tsibirin na Bali, Wayan Koster ya ce a karskashin sabuwar dokar da za a kafa , masu yawon bude ido za su iya samun babura ne kawai daga masu shirya wa mutane tafiye tafiye da hukumomi suka tantance

  13. An hallaka mutum biyar da jikkata 11 ciki har da gwamna a Somalia

    Hoton hari a Somalia

    An hallaka aƙalla mutum biyar da jikkata wasu 11 ciki har da gwamnan yanki a wani harin ƙunar-baƙin-wake da aka kai a kudancin Somalia, kamar yadda wata majiyar 'yan sanda ta sheda wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

    An kai harin ne da wata mota da ke ɗauke da bama-bamai, wadda aka kara ta a jikin wani gidan sauƙar jami'an gwamnati a Bardera, garin da ke da nisan kilomita 450 yamma da babban birnin ƙasar Mogadishu.

    Rahotanni sun ce harin ya lalata ginin gidan sosai sannan kuma wasu jami'an tsaro biyar sun rasa ransu a fashewar.

    Waɗanda suka ji rauni sun kai 11 ciki har da gwamnan yankin, Ahmed Bulle Gared.

    Babu wani ko wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin kai harin, amma abu ne sananne cewa ƙungiyar masu iƙirarin jihadi ta Al-Shabaab, ta saba kai hare-hare irin wannan a ƙasar da ma wannan yanki na ƙuryar gabashin Afirka.

  14. Ƴan sanda a jihar Bauchi sun sa tukucin naira miliyan ɗaya domin kama ɗan majalisar wakilai

    Hoton Sufeto Janar Usman Alƙali

    Rundunar ƴan sanda a jihar Bauchi ta sanya tukuicin naira miliyan ɗaya ga duk mutumin da ya bayar da bayanan inda ɗan majalisar wakilai na tarayya na mazaɓar tarayya ta Bauchi Yakubu Shehu yake.

    Ana neman ɗan majalisar ne ruwa a jallo kamar yadda rundunar ta bayyana a wata sanarwa, bisa zarginsa da laifin tayar da husuma da rikici da kuma kisan kai.

    A sanarwar rundunar wadda ta sanya hoto da kuma adireshin ɗan majalisar mai shekara 45, ta ce za ta bayar da tukuicin naira miliyan ɗaya ga duk wanda ya bayar da bayanin da zai kai ga kamashi, inda ta sanya lambar waya da za a tuntuɓe ta ko kuma duk wani ofishin ƴan sanda mafi kusa.

    Shehu ɗan jam'iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) ne, wadda a cikinta ya yi takarar majalisar dattawa amma ya yi rashin nasara a hannun Sanata Lawal Yahaya Gumau.

    An zaɓe shi zuwa majalisar wakilai ta tarayya a 2019, a ƙarƙashin jam'iyyar Peoples Redemption Party (PRP), amma kuma ya sauya sheƙa zuwa All Progressives Congress (APC), kafin ya tafi NNPP.

  15. INEC ta yi alƙawarin bai wa jam'iyyun PDP da LP damar duba kayan zaɓen shugaban ƙasa

    Hoton shugaban INEC
    Image caption: Jam'iyun PDP da LP na ƙalubalantar sakamakon zaɓen

    Hukumar zaɓen Najeriya, ta yi alƙawarin miƙa dukkanin kayan zaɓen da ƴan hamayya za su buƙata waɗanda aka yi amfani da su a zaɓen watan da ya gabata na shugaban ƙasa ba tare da ɓata wani lokaci ba.

    Shugaban na INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce, hukumar ba ta da wani abu da za ta ɓoye a zaɓen da ake taƙaddama a kansa.

    Babbar jam'iyyar hamayya ta PDP da kuma ta Labour (LP), suna son duba kayan zaɓen ne domin su samu damar shirya wa ƙarar da za su shigar ta ƙalubalantar sakamakon zaɓen, wanda INEC ta ayyana ɗan takarar jam'iyyar APC mai mulki, Bola Tinubu, a matsayin wanda ya yi nasara.

    Jam'iyyun suna da mako biyu ne kawai su shigar da ƙara.

    Jam'iyyar Labour ta yi barazanar shirya zanga-zanga ta ƙasa baki ɗaya idan INEC ta hana ta duba kayayyakin.

  16. An bai wa matar da aka ɗaure kan satar kuɗi muƙamin ma'aji a jami'ar Afirka ta Kudu

    An bai wa wata mata da aka taɓa ɗaurewa a kurkuku saboda kashe maƙudan kuɗin da aka tura mata asusunta na banki bisa kuskure, muƙamin ma'ajin wani kwamiti a wata jami'a a Afirka ta Kudu.

    Shekara biyar da ta wuce bisa kuskure aka tura wa Sibongile Mani tallafin ɗalibai na karatu na kusan dala miliyan ɗaya a bankinta.

    Sai dai a lokacin maimakon ta kai rahoto ta mayar da kuɗin sai ta shiga facaka, inda ta kashe dala dubu 70 wajen sayen wayoyin salula da kayan ƙawa da barasa da gashin ado iri-iri, har sai da aka kama ta.

    Rahotanni sun ce a lokacin an yanke mata hukuncin ɗaurin shekara biyar amma aka rage mata sannan aka sake ta kafin lokacin.

    Kafofin yaɗa labarai na Afirka ta Kudu na cewa yanzu, an zaɓi Mani a muƙamin ma'aji ta wani kwamitin shirya bikin yaye ɗalibai a Jami'ar Walter Sisulu University (WSU) Eastern Cape.

    Sai dai ba za a tabbatar mata da muƙamin ba har sai nan gaba a wannan makon bayan an bi matakin tantancewa.

    An riƙa yaɗa hotunan yaƙin neman zaɓenta a shafukan intanet.

    View more on facebook