Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza

time_stated_uk

  1. Bankwana

    Masu bibiyarmu anan muka kawo karshe labarai da rahotannin namu.

    Sai da safe..

  2. Saudiyya za ta gayyaci Bashar al-Assad zuwa taron Riyad

    BBC

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce Saudiyya na shirin gayyatar Shugaban Syria Bashar al-Assad zuwa taron da za ta karɓi baƙunci a Riyad cikin watan Mayu, a wani mataki da ake ganin zai kawo ƙarshen saniyar ware da aka mayar da Syria a yankin.

    A cewar Reuters, wasu majiyoyi biyu sun ambato cewa ministan harkokin wajen Saudiyya, Yarima Faisal bin Farham zai kai ziyara Damascus a cikin makonni masu zuwa don kai wa Shugaba Assad takardar gayyata a hukumance.

    Za a yi taron ne ranar 19 ga watan Mayu.

    A cikin watan jiya ne, hukumomin Riyad suka sanar da fara wata tattaunawa da mahukuntan Damascus, a yunƙurin mayar da hulɗar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu.

    Alaƙar diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu ta samu matsala ne a 2011, saboda matsayin da Saudiyya ta ɗauka lokacin juyin-juya-halin ƙasashen Larabawa na neman a cire Shugaba Bashar Assad.

    Al'amarin da ya mayar da shi saniyar ware a tsakanin ƙasashen Larabawa.

  3. China ta gargaɗi Japan kada ta yi wasa da ikonta na ƙasa mai 'yanci

    Hukumomin Japan sun ce ministan harkokin wajen ƙasar Yoshimasa Hayashi, ya yi wata tattaunawar ƙeƙe-da-ƙeƙe da takwaransa na China yayin wata ziyara a Beijing.

    Hong Kong ta ce yanayin da Musulman yankin Xinjiang marasa rinjaye ke ciki, da kuma muhimmancin tabbataccen zaman lafiya a Taiwan na cikin abubuwan da suka tattauna.

    A gefe ɗaya kuma, jami'an China sun ce sun yi wa Japan gargaɗin kada ta riƙa katsalandan cikin harkokin China da Taiwan.

    Kuma kada ta sake ta raina ikonta na kasancewa dunƙulalliyar ƙasa mai cikakken 'yancin cin gashin kai.

    Hukumomin Beijing suna ɗaukar Taiwan, a matsayin wani ɓangare na ƙasarsu China kuma a yanzu haka, sun ƙara yawan ayyukan sojojinsu a kan iyaka.

  4. Labarai da dumi-dumi'Yan adawa a Kenya sun soke zanga-zangar da suka shirya yi ranar Litinin

    BBC

    Jagoran 'yan adawa a Kenya, Raila Odinga ya sanar da soke zanga-zangar da suka shirya yi don ci gaba da nuna bijirewa ga gwamnati a ranar Litinin, da zimmar buɗe ƙofar tattaunawa da hukumomin ƙasar.

    Ya ce gamayyar 'yan adawar a shirye suke su zauna kan teburin sulhu game da batutuwan da gwamnati ta amince su tattauna.

    Tun da farko, shugaban Kenya, William Ruto ne ya nemi 'yan adawar su dakatar da zanga-zangar.

  5. Birtaniya ta kare shirinta na mayar da 'yan ci-rani zuwa Rwanda

    BBC

    Sakatariyar harkokin cikin gida, Suella Braverman ta sake kare matakin gwamnatin Burtaniya na iza ƙeyar 'yan ci-rani zuwa Rwanda ba tare da ƙoƙarin sama musu shaidar neman mafaka ba, kamar yadda ta yi iƙirari.

    An tambayi Braverman a wata tattaunawa da BBC kan abin da ya faru a 2018, lokacin da jami'an tsaro a Rwanda suka harbe wasu 'yan ci-rani da suka koka a kan ƙarancin abinci.

    Sai ta ce ai wannan "tsohon zance ne" kuma babbar kotun Landan ta amince da shirin Burtaniya.

    Ta ɓangaren shari'a game da shirin na Burtaniya mai cike da ka-ce-na-ce hakan na nufin har yanzu ba a mayar da kowa gida ba, a ƙarƙashin yarjejeniyar da ƙasashen biyu suka cimma.

    Suella Braverman ta kai ziyara Kigali kimanin makonni biyu da suka wuce, don tattaunawa kan yarjejeniyar karɓar 'yan ci-rani da Rwanda za ta yi.

    'Yan ci-ranin dai sun je Burtaniya ne ba bisa ƙa'ida ba, akasari kuma ta jiragen kwale-kwale daga Afirka, inda suke tafiyar tsallaka teku mai cike da hatsari.

  6. Post update

    BBC

    Leicester ta rabu da kocinta Brendan Rodgers bayan shekara 4. Leicester ce ta 19 a teburin Premier.

  7. Bankin Duniya ya damu kan yawan bashin da China ke bai wa Afirka

    BBC

    A wata hira da BBC shugaban Bankin Duniya David Malpass, ya bayyana damuw a kan basukan da China ke dumbuza wa ƙasashen Afirka masu tasowa.

    Ya ce kamata ya yi a riƙa bayyana ƙa'idojin yarjejeniyar irin wannan bashi a fili.

    ''Wannan abin damuwa ne a daidai lokacin da ƙasashe irin su Ghana da Zambiya ke fuskantar matsalar kasa biyan bashi ga ƙasar ta China'', in ji Mista Malpass.

    Ita dai, China tana cewa tana ƙulla yarjejeniya da ƙasashen ne bisa tsarin dokokin duniya.

    A shekarun baya-bayan na dai, China ta kasance ɗaya daga cikin ƙasashen da ke samar da bashi ga ƙasashe masu tasowa.

    Wani bincike ya nuna cewa daga 2016 zuwa 2021, China ta ba da rancen dala miliyan 185 ga ƙasashe 22.

    Wasu daga cikin cibiyoyin ba da rance na duniya, sun yi zargin cewa China na karɓar kadarorin da ba a yarda da su ba, a matsayin jingina kafin ba da rancen.

    Sun kuma yi zargin cewa ƙasashen kan biya rancen a wasu lokuta ta hanyar sayar wa Chinar albarkatun ƙasar da suke da su.

  8. Isra'ila na yunƙurin kafa dakarun tsaro na musamman

    BBC

    A yau ne ake sa ran Isra'ila za ta sa hannu a kan shirin ministan tsaron ƙasar Itmar Ben Gvir, na kafa dakarun tsaro na musamman, yayin da ake ci gaba zanga-zanga kan shirin gwamnati na yi wa ɓangaren shari'ar ƙasar garambawul.

    Tuni aka fara watsa labarai a Isra'ila cikin daren jiya cewa gwamnati za ta ware kudin ƙasar shekel biliyan ɗaya, daidai da dala miliyan 224 don samar da wannan runduna, tana cewa za a cire kashi ɗaya na kuɗin da ake keɓewa duk ma'aikatun Isra'ila.

    Gidajen jaridu na ƙasar sun ambato sojoji na cewa za a samar da sabuwar rundunar tsaron ce don rage yawan kuɗin da ake warewa sojoji.

    Wannan na zuwa ne a lokacin da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ke neman amincewa kan sauyin da yake son yi a fannin shari'ar ƙasar, duk da cewa an dakatar da hakan a makon jiya, amma masu zanga-zanga na neman a soke matakin gaba ɗayansa.

  9. Hukuncin mace mai ciki da mai shayarwa a lokacin azumi

    Video content

    Video caption: BBC Hausa

    Malama Habiba Alfadarai, mai ɗakin limamin Babban Masallacin Ƙasa na Najeriya, Sheikh Ibrahim Maqari, ta yi bayani a kan hukuncin addini game da ramuwar azumi, ko ciyarwa ga mace mai juna biyu ko kuma mai shayarwa.

  10. 'Yan bindiga sun sace dalibai mata biyu na jami'ar Gusau

    ggg

    'Yan bindiga sun sace ɗalibai mata guda biyu a jami'ar tarayya da ke Gusau a jihar Zamfara, arewa maso yammacin Najeriya.

    Rahotonni sun ce 'yan fashin ɗauke da muggan makamai, sun sace ɗaliban ne a ɗakunan kwanansu da ke wajen makarantar.

    Wata sanarwa da rundunar 'yan sandan jihar ta fitar, ta ambato kwamishinan 'yan sandan Zamfara, CP Kolo Yusuf na tabbatar wa iyayen ɗaliban da kuma hukumar makarantar cewa rundunar tana ƙoƙari don ganin ta kuɓutar da su.

    Ta ce 'yan sanda sun samu rahoton sace ɗaliban a ɗakunan kwanansu da ke a wajen makarantar, kuma ba ta yi ƙasa a gwiwa ba, ta tura jami'anta zuwa wajen da lamarin ya auku.

    Sai dai kafin zuwan jami'an tsaron 'yan fashin sun tsere da ɗaliban, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

    Haka kuma sanarwar ta ce kwamishinan 'yan sandan ya tura ƙarin jami'an tsaro don bin sawun 'yan fashin da kuma kuɓutar da ɗaliban.

    Zamfara, ta yi ƙaurin suna a matsayin jihar da 'yan fashin daji suka mamaye wasu sassanta, inda suke kai hare-hare da sace mutane a ciki har wajen jihar suna neman kuɗin fansa daga makusanta da dangin waɗanda abin ya ritsa da su.

    An yi imani har yanzu akwai ragowar ɗaliban kwalejin tarayya ta Yawuri su 11 dukkansu mata, waɗanda aka sato daga jihar Kebbi mai maƙwabtaka, kuma ake ci gaba da tsarewa a wani daji da ke cikin Zamfara.

    Ranar 16 ga watan Yunin 2021 ne, 'yan bindigar suka sace ɗaliban su kimanin 100 tare da wasu malamansu, inda suka tafi da su daji, kafin daga bisani su saki mafi yawansu cikin rukuni-rukuni.

  11. Taɓa Kiɗi Taɓa Karatu

    Video content

    Video caption: Latsa lasifikar da ke sama domin sauraron shirin

    Sani Mu'azu Kacako ne da Aminu Abdulƙadir suka gabatar da shirin a wannan makon

  12. Sojojin Najeriya sun kashe 'yan fashi 11 a Birnin Gwari

    dw

    Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kashe 'yan fashin daji 11 lokacin wata arangama, a yankin Birnin Gwari cikin jihar Kaduna, arewa maso yammacin Najeriya.

    Wata sanarwa da ya fitar, kwamishin tsaro da al'amuran cikin gida na Kaduna, Samuel Aruwan ya ce a lokacin gumurzun, dakarun sojin Najeriya sun fatattaki 'yan fashin dajin a ƙauyen Kakangi da katakaki.

    Sanarwar ta ce sojoji sun kuma lalata sansanonin 'yan fashin daji a ƙauyukan Bagoma da Rema da Bugai da Dagara da Sabon layi da Gagumi da Kakangi da katakaki da kuma Randagi.

    Sojojin in ji Aruwan, sun samu nasarar kashe 'yan fashi 11 yayin da wasu da dama suka tsere da raunukan bindiga.

    Haka kuma sanarwar ta ce a lokacin arangamar, sojojin sun ƙwato bindigogi guda biyu ƙirar AK-47, da kurtun albarusan guda biyu, sai albarusai 57 da babur shida.

    Gwamna Malam Nasir El-rufai ya jinjina wa sojojin bisa wannan nasara a jiharsa ta Kaduna, tare da kiran su ƙara ƙaimi a ƙoƙarinsu na fatattakar 'yan fashin daji a faɗin jihar.

    Kaduna na ɗaya daga cikin jihohin arewacin Najeriya da suka fi fama da rikicin 'yan fashin daji da ke kai hare-hare suna tayar da ƙauyuka da tare da hanyoyi, da kuma uwa-uba satar dukiya da ta mutane don neman kuɗin fansa.

  13. Burkina Faso ta kori 'yan jaridar Faransa biyu daga ƙasar

    Jaridun Le Monde da Liberation na Faransa sun ce Burkina Faso ta kori masu aika musu rahotanni daga ƙasar.

    'Yar jaridar Le Monde, Sophie Doss ta ce wasu mutane ne a cikin fararen kaya suka ziyarci gidanta ranar Asabar, inda suka faɗa mata cewa hukumomi sun janye shaidar da aka ba ta ta zama a ƙasar, don haka ana buƙatar ta fice daga Burkina Faso cikin sa'a 24.

    Korar ta zo ne bayan wani labari da jaridar Liberation ta wallafa a makon jiya, wanda ya zargi sojojin Burkina Faso da kashe fararen hula a duk sansanoninsu, ciki har da ƙananan yara.

    Waɗannan 'yan jarida biyu su ne na baya-bayan nan, da ƙasar wadda Faransa ta yi wa mulkin mallaka, ta kora, bayan wani juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Satumba.

    Har yanzu dai hukumomin Burkina Faso ba su fito sun ce uffan a kan wannan lamari ba.

  14. Buhari ya yaba wa Anthony Joshua

    dd

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yaba da nasarar da ɗan damben Burtaniya, haifaffen Najeriya Anthony Joshua ya samu a kan abokin karawarsa Jermaine Franklin a karon battar da suka yi cikin filin wasa na O2 Arena da ke birnin London.

    buhari

    A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Tuwita, Shugaba Buhari ya ce nasarar da Joshua ya samu, na nuna cewa ta hanyar aiki tuƙuru da sadaukarwa gami da jajircewa ne ake samun nasara.

    View more on twitter

    Shugaba Buhari ya yi fatan nasarar ta kasance ɗaya daga cikin waɗanda ba za a taɓa mantawa da su ba a tarihin gasar dambe.

    Ita ce nasara, ta 25 da Joshua ya samu tun bayan zamansa fitaccen ɗan wasan dambe a 2013.

  15. Amsoshin Takardunku

    Shin wacce ƙasa ce ta fi samun girgizar ƙasa a duniya?

    Sannan me ke janyo shanyewar ƙafafuwa ga ƙananan yara?

    Duka a cikin shirin Amsoshin Takardunku na wannan mako, wanda Ahmad Inuwa Fagam ya gabatar

    Video content

    Video caption: Latsa lasifikar da ke sama domin sauraron shirin
  16. Shugaban jam'iyyar NNPP na ƙasa ya ajiye muƙaminsa

    Rufa'i

    Shugaban jam'iyyar adawa ta NNPP a Najeriya, Farfesa Rufa'i Alƙali, ya ajiye muƙaminsa.

    A cikin wata wasiƙa da ya aike wa sakataren jam'iyyar na ƙasa, kuma ya wallafa a shafinsa na Tuwita, Farfesa Alƙali ya ce ya ajiye muƙamin nasa ne don bai wa sabbin jini dama, ta yadda za su ɗora a kan ci gaban da jam'iyyar ta samu cikin ɗan taƙaitaccen lokacin da ya yi yana jagorantar ta.

    Alƙali ya ce la'akari da irin abubuwan da suka faru kafin zaɓukan da suka gabata, da kuma a lokacin zaɓukan, yana cike da fatan cewa jam'iyyar adawar, na da makoma mai kyau.

    Kuma a cewarsa, yana cike da fatan NNPP za ta kasance cikin manyan jam'iyyun siyasar ƙasar, da za su iya cin zaɓen shugaban ƙasa da sauran muƙamai a kakar zaɓe ta 2027.

    Ya ƙara da cewa don cimma wannan buri, NNPP na buƙatar yin tunani da kuma kyakkyawan shiri, abubuwan da yanzu ne lokaci mafi dacewa na yin su.

    Farfesa Rufa'i Alƙali ya kuma ce jam'iyyar na buƙatar sauye-sauye da dama, ta fuskar shugabancinta a matakai daban-daban domin ƙara ƙarfafa matsayinta.

    ''Na kuma gamsu cewa wannan sauyi dole ya fara ta kaina. wannan shi ne dalilin da ya sa na ajiye muƙamina, don ba da dama ga sabbin hannu su ɗora daga inda muka tsaya game da gudunmawar da muka bai wa NNPP'', in ji Alkali.

    Ya kuma miƙa saƙon godiya ga jagoran jam'iyyar na ƙasa Injiniya Rabi'u Musa Kwankwaso da ɗaukacin mambobin kwamitin amintattu na NNPP, da sauran zaɓaɓɓun 'yan siyasa na jam'iyyar bisa damar da ya ce sun ba shi wajen gudanar da mulki cikin kwanciyar hankali.

    View more on twitter
  17. 'Yan sanda sun kama mutum 17 kan zargin aikata miyagun laifuka a Zamfara

    Kolo Yusuf

    'Yan sanda sun ce sun kama mutum 17 bisa zargin laifuka daban-daban ciki har da tashe-tashen hankula bayan zaɓe, da fashin daji da satar shanu da kuma sara suka a jihar Zamfara, arewa maso yammacin Najeriya.

    A wata sanarwa da 'yan sandan suka fitar ta hannun jami'in hulɗa da jama'a na rundunar jihar, SP Mohammed Shehu, ya ce jami'ansu sun yi kamen ne a sassa daban-daban na Zamfara, tare da ƙwato muhimman kayayyaki daga hannun waɗanda ake zargi.

    Rundunar ta ce daga cikin mutanen da ta kama har da wani fitaccen ɗan fashin daji wanda ya addabi jihar mai suna Sulaiman Balarabe, ɗan shekara 25.

    Ta kuma ce ta kama ɗan fashin dajin - wanda da ma sunansa ke cikin jerin mutanen da rundunar ke nema ruwa-a-jallo - ranar Laraba 29 ga watan Maris

    Bayan kama wanda ake zargin ne kuma, ya tabbatar wa 'yan sanda cewa yana da hannu a hare-hare da sace mutane don neman kuɗin fansa.

    Haka zalika a cewar sanarwar 'yan sanda, Sulaiman Balarabe ya ce ya karɓi miliyoyin kuɗaɗee daga hannun imakusantan da ya sace wa 'yan'uwansu.

    masu laifi

    Rundunar 'yan sandan ta kuma ce ta kama ƙarin mutum uku bisa zargin satar shanu da sauran ƙananan dabbobi, a lokacin da suke kan hanyar zuwa Gusau daga Dansadau, da dabbobin a cikin motoci guda biyu.

    Sanarwar ta ambato kwamishinan 'yan sandan Zamfara, CP Kolo Yusuf na yaba wa al'ummar jihar bisa haɗin kai da suke bai wa jami'an tsaro wajen gudanar da ayyukansu.

    Kwamishinan ya sake jaddada kiransa ga Zamfarawa su ci gaba da bai wa jami'an tsaron goyon baya don tabbatar da ganin kwanciyar hankali da zaman lafiya sun dawwama a jihar.

  18. Saudiyya ta kama 'yan ci-rani sama da 16,000

    ss

    Hukumomin Saudiyya sun ce sun kama baƙin haure 16,407 da suka shiga ƙasar ba bisa ƙa'ida ba, a yankuna daban-daban na ƙasar cikin mako ɗaya.

    Jaridar Saudi Gazette ta ambato ma'aikatar harkokin cikin gida ta ƙasar na cewa an kama mutanen ne bayan wani samamen haɗin gwiwa da jami'an tsaro suka ƙaddamar a sassa daban-daban cikin wannan wata na Ramadan.

    Kamen ya haɗar da mutunen da suke zaune a ƙasar ba tare da izini ba, da mutunen da ba su da takardun shiga ƙasar, sai kuma mutunen da suka saɓa ƙa'idojin aiki na Saudiyya.

    Ma'aikatar ta ce ta kama wasu a lokacin da suke ƙoƙarin tsallaka kan iyakar ƙasar, wasu kuma an kama su ne lokacin da suke yunƙurin fita daga ƙasar .

    Ta ce kashi 74 na waɗanda aka kama, 'yan Habasha ne, sai kashi 22 'yan asalin Yemen, kashi huɗu kuma na sauran ƙasashe.

    Ma'aikatar cikin gidan ta ce an tura 'yan ci-rani 6,251 zuwa ofisoshin jakadancin ƙasashensu da ke Saudiyya don samar musu takardun izini, yayin da za a mayar da mutum 10,156 zuwa ƙasashen da suka fito.

    Ta dai gargaɗi duk wani mutum - da ya yi sanadin shigar da wani baƙon haure cikin Saudiyya ba bisa ƙa'ida ba, ko ya ba shi masauki, ko aiki, da dai duk wani nau'in taimako - ya tabbatar cewa zai fukanci hukuncin da zai iya kai wa ɗaurin shekara 15 a gidan yari, matuƙar aka kama shi.

    Sannan da biyan tarar riyal miliyan ɗaya, idan aka same shi da laifin haɗa baki wajen shigar da baƙin haure cikin ƙasar, da kuma samar musu masauki.

    dsds
  19. Sojojin Najeriya sun kashe 'yan fashin daji biyar a Kaduna

    Sojoji

    Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun kashe 'yan fashin daji biyar tare da ƙwato makamai a wani samame da ta kai dajin Kubusu da kuma tsaunukan Kaso a yankin Chikun na jihar Kaduna, arewa maso yamma.

    Wata sanarwa da mai riƙon muƙamin jami'in hulda da jama'a na runduna ta 1 ta sojojin Najeriya da ke Kaduna, Laftanal Kanal Musa Yahaya ya fitar, ta ce dakarun sojin sun kuma ƙwato bindigogi ƙirar AK 47 shida, da harsasan bindigogi, da wasu ƙarin albarusai, da babura uku da ƙarin wasu kayayyaki.

    “A lokacin artabu da 'yan fashin wanda ya ɗauki sa'o'i, dakarun sojin sun samu nasarar fatattakar gungun mahara, tare da kashe biyar a cikinsu.

    Sannan suka ƙwato makamai masu tarin yawa'', kamar yadda sanarwar ta bayyana.

    Daga ƙarshe sanarawar ta ambato babban kwamandan runduna ta 1 da ke Kaduna Manjo Janar Taoreed Lagbaja, na yaba wa dakarun sojin bisa wannan namijin ƙoƙari da ya ce sun yi a lokacin fafatawar.