Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Buhari Muhammad Fagge da Abdullahi Bello Diginza

time_stated_uk

  1. Bankwana

    Masu bin mu a wannan shafi nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.

    Mun yi farin cikin kasancewa da ku a tsawon wannan rana.

    Da fatan za ku ci gaba da bibiyar mu a wannan shafi na BBC Hausa.

    Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya!

  2. Rasha ta kori wasu ma'aikatan diplomasiyyar Jamus a ƙasarta

    BBc

    A yayin da dangantaka tsakanin Rasha da ƙasashen yamma ke ci gaba da yin tsami saboda yaƙin Ukraine, Rasha ta ɗauki matakin korar wasu jami'an diplomasiyyar Jamus da ke ƙasarta.

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Rasha Maria Zakharova a ranar Asabar na cewa matakin ramuwar gayya ne kan matakin da Jamus ɗin ta ɗauka na korar ma'aikatan ofishin jakadancin Rasha Jamus.

    Kafar yaɗa labaran RIA News Channel, ta ce Jamus ta kori fiye da ma'aikatan ofishin jakadancin Rasha da ke Jamus.

    Wani jami'i a ma'aikatar harkokin ƙasashen wajen Jamus ya ce ƙasarsa ta kwashe kusan makonni tana tattaunawa da Rasha kan batun.

    Matakin da Rasha ta ɗauka na korar jami'an diplomasiyyar na Jamus shi ne na baya-bayan nan a jerin korar jami'an diplomasiyyar ƙasashen yamma, tun bayan mamayar Ukraine.

    A 'yan watannin baya-bayan nan ƙasashen Turai irin su Jamhuriyar Ireland da Netherlands da Austria da jamhuriyar Czech da Belgium sun ɗauki matakan korar jami'an diplomasiyyar Rasha a ƙasashensu, bayan da suka zarge su da saɓa ƙa'idar aiki.

  3. Lafiya Zinariya: Kan cutar Basir

    Video content

    Video caption: Latsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
  4. Ƙasashen Larabawa da suka yi sallah ranar Asabar

    BBC

    A yau Asabar ne, ƙasashen Larabawa da dama suka yi Sallah, bayan sanar da cewa ba a ga watan Shawwal ba a ranar Alhamis.

    Masarautar Morocco da ta Oman sun ce ranar Asabar ce 1 ga watan Shawwal, saboda gaza ganin wata da aka yi, abin da ya sa aka cika azumin watan Ramadana kenan ya kai 30 wato aka kammala shi a ranar Juma'a.

    gg

    Ƙasar Libya kuwa rabuwar kai aka samu inda wasu suka yi sallar ranar Juma'a wasu kuma suka yi ranar Asabar.

    Gwamnatin Tripoli babban birnin ƙasar wadda ƙasashen duniya suka amince da ita, ta sanar da ranar Asabar a matsayin ranar Sallah.

    g

    Yayin da gwamnatin da ke ƙarƙashin jagorancin Halifa Heftar da ke gabashin ta sanar da ganin jaririn watan Shawwal a ranar Alhamis ta kuma tabbatar da Juma'a a matsayin 1 ga wata.

    Haka abin ya faru a Iran bayan jagoran addini na ƙasar Ali Kamenei ya ce ba a ga wata ba a ranar Juma'a.

  5. Da kuɗin haram aka gina mafi yawan rukunin gidajen Abuja - EFCC

    Jami'an hukumar EFCC

    Hukumar da ke Yaƙi da yi wa Tattalin Arzikin Najeriya ta'annati EFCC ta ce a yanzu za ta mayar da hankali kan waɗanda ke fakewa da gina rukunin gidaje wajen halasta kuɗin haram da sauran laifukan da suka shafi kuɗi.

    Yayin da yake jawabi a wajen taron haras da 'yan jarida kan yadda za su riƙa bayar da ingantattun rahotonni kan laifukan da suka shafi kuɗi da tattalin arziki a birnin Benin na jihar Edo, lauyan hukumar Chris Mishela ya ce da yawa daga cikin rukunin gidajen da ake ginawa a Abuja da Legas da sauran yankunan ƙasar, ana gina su ne da kuɗaɗen haram.

    Ya ƙara da cewa, ''akwai rukunin gidaje masu yawa a Abuja, waɗanda muka yi amanna cewa an samu kuɗin gina su ta haramtattun hanyoyi''.

    ''Kuɗaɗen haram da yawa da aka samu ta ɓangaren gwamnati ko wasu miyagun laifukan da suka shafi kuɗi na duniya, ana amfani da su wajen kasuwancin rukunin gidaje'', in shi.

    ''EFCC na aiki domin bincike da kuma lura da wannan ɓangare, kuma sabuwar dokar halasta kuɗin haram ta bai wa gwamnati damar lura da bincike kan rukunin gidaje, kuma EFCC na ƙarƙashin gwamnati don haka muna aiki da dokar''.

    “Ba iya binciken kawai muke yi ba, mun ma gano cewa wasu daga cikinsu an gina su ne da kuɗin haram.”

  6. Ra'ayi Riga kan aikin hajjin bana

    Shirin namu na wannan mako ya duba shirin aikin hajjin bana.

    Bayan wucewar azumi, ibada ta gaba da musulmai ke sanyawa a gaba ita ce ibadai aikin hajji, wadda ake gudanarwa a cikin watan Zul-hijja.

    tuni dai hukumomin Najeriya suka sanar da kuɗin aikin hajji na bana, kuma a cikin watan Mayu ne za a fara jigilar maniyyatan aikin hajjin na bana.

    Video content

    Video caption: Latsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
  7. An ba da rahoton cewa 'yan tawaye sun kai hari kan "sansanin sojin Rasha" a Mali

    BBC

    'Yan tawaye masu iƙirarin jihadi sun auka wa wani "sansanin dakarun Rasha" a tsakiyar Mali, kamar yadda aka ba da rahoto..

    Yanzu ne ake samun bayanai, amma dai kamfanin dillancin labarai na AFP ya ba da rahoton cewa mayaƙa sun yi wa filin jirgin sama mafi kusa a garin Sevare, cikin lardin Mopti tsinke.

    A bara, sojoji masu mulki a Mali sun ɗauko hayar "sojojin Rasha masu ba da horo" don taimakawa mata a yaƙin da ƙasar take yi da ƙungiyoyin 'yan ta-da-ƙayar-baya masu alaƙa da ISIS da Al Qaeda.

    Amurka ta ce masu horaswar, sojojin haya ne na Ƙungiyar Wagner ta Rasha.

    An zargi Wagner da take 'yancin ɗan'adam a wasu ƙasashen Afirka irinsu Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

  8. Zazzaɓin Denge ya kashe mutum 45 a Argentina

    dengue
    Image caption: Mafi yawan lokuta, ba a ganin alamomin zazzaɓin denge

    Hukumomin lafiya a Argentina sun sanar cewa an ƙara samun mutanen da suka mutu sanadin zazzaɓin denge a 'yan kwanakin nan.

    Argentina ce ta taɓa samun ɓarkewar zazzaɓin denge mafi muni da yawan mutanen da suka kamu a Kudancin Amurka

    Sai dai mace-macen da aka samu sanadin zazzaɓin da ya sake ɓulla a bana sun disashe na baya.

    Tun a farkon wannan shekara, a cewar jami'an lafiya, mutum 45 suka mutu yayin da wasu fiye da 65,000 suka kamu da zazzaɓin.

    Denge, wani zazzabi ne mai saurin yaɗuwa kuma sauro ne yake haddasa shi.

    Hatsarin zazzaɓin shi ne a mafi yawan lokuta, ba a ganin alamomin cuta, sai dai ƙwayar cutar sau da yawa tana iya kai wa ga mutuwa.

  9. Gobara ta hallaka mutum biyu a wurin sayar da abinci a Madrid

    BBC

    Wata gobara da ta tashi a wurin wani cin abinci a Madrid babban birnin Spaniya, wadda ta yi sanadin mutuwar mutum biyu da jikkata wasu 10 na daban.

    Wutar ta tashi ne a wajen cin abincin wani ɗan ƙasar Italiya da ke tsakiyar birnin kusa da Salamanca.

    Waɗanda lamarin ya faru a kan idanunsu sun ce wutar ta tashi a lokacin da wani mai kai abinci ya ke ƙoƙarin kunna wuta a kan wani tire sai wutar ta tashi ta kama bango da rufin wurin.

    A cewar masu aikin ceto, lokacin da wutar ta tashi, sai kwastomomi suka fara gudun tsira da rayuwarsu.

    Yan sandan birnin sun fara bincike kan musabbabin tashin wutar.

  10. Hotunan yadda aka yi bikin ƙaramar salla a Ghana

    Ghana
    Image caption: A yau ne al'ummar Musulmi a Ghana ke bikin Ƙaramar Salla, bayan cika azumin watan Ramadana zuwa 30.
    Ghana
    Image caption: Mafi yawan ƙasashen Musulmi a duniya sun yi nasu bikin Ƙaramar Salla ne a jiya Juma'a.
    Ghana
    Image caption: Jami'ai a Ghana sun ce ba a ga jaririn watan Shawwal ba a ranar Alhamis, abin da ya sa al'ummar Musulmi a ƙasar suka cika azuminsu a ranar Juma'a.
    Ghana
    Image caption: Musulmai dai bisa ƙa'ida kan cika azumin watan Ramadan zuwa 30, idan ba su jaririn wata a ranar 29 ba.
    Ghana
    Image caption: Ƙasashe irin su Saudiyya da Najeriya da Nijar duka sun sanar da ganin jaririn watan Shawwal ranar Alhamis, abin da ya sa suka gudanar da shagalin ƙaramar salla a jiya Juma'a.
    Ghana
    Image caption: Mutane na cike da farin ciki da sada zumunci bayan sauke azumin watan Ramadan.
  11. Gane Mini Hanya

    A jamhuriyar Nijar Maganar ilimi na kan gaba a batutuwan da shugaban ƙasar Muhammad Bazoum mayar da hankali, don haka shugaban ke ƙoƙarin kawo gyara a fannin, ta hanyar horar da malamai da inganata karatun ‘ya’ya mata da ƙoƙarin kawar da azuzuwan zana.

    Muhammad Kasim Muktar shi ne ministan ilimin makarantun koyar da fasaha da sana’o’in hannu ga kuma ƙarin bayanin da ya yi wa wakiliyarmu Tchima llla Issoufou

    Video content

    Video caption: Latsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
  12. Rikicin Sudan: An fara kwashe 'yan Saudiyya daga Sudan

    .

    Ma'aikatar Harkokin Wajen Saudiyya ta fara kwashe 'yan ƙasar da kuma wasu 'yan ƙasashen Larabawa da ma sauran jama'ar ƙasashe abokan ƙawance.

    Rundunar sojojin Sudan ta faɗa a yau Asabar cewa, an fara tsare-tsaren kwashe jami'an diflomasiyya da mutanen ƙasashen Larabawa da ke son fita daga Sudan.

    Matakin na zuwa ne bayan tattaunawa da Shugaban Majalisar Iko da Iyakokin ƙasar, Laftanal Janar Abdel Fattah Al-Burhan, da shugabannin wasu ƙasashe game da hanyar da za a tabbatar da kwashe mutanen.

    An kwashe jami'an ofishin jakadancin diflomasiyyar Saudiyya ta ƙasa zuwa yankin Port Sudan daga nan kuma aka kwashe su a jirgin sama zuwa Masarautar Saudiyya.

    Haka kuma an tsara cewa su ma jami'an diflomasiyyar Jordan za a kwashe su ne ta irin wannan hanya.

    Yayin da ƙazamin yaƙin Sudan yake shiga makonsa na biyu, ƙasashe da yawa sun yanke shawarar kwashe mutanensu daga Sudan, kuma su ci gajiyar yarjejeniyar tsagaita wuta mai tangal-tangal don kwashe 'yan ƙasashen waje.

    Dakarun RSF sun nuna muradinsu na taimaka wajen sake buɗe filayen jiragen sama don sauƙaƙa aikin kwashe 'yan ƙasashen wajen.

    Majalisar Ɗinkin Duniya da Amurka da Burtaniya da Japan da Switzerland da Koriya ta Kud da Sweden da Sifaniya na tattaunawa kan shirye-shiryen kwashe ma'aikatansu daga Khartoum.

    Sojojin Jamus sun fara shirye-shirye a wani sabon yunƙuri na kwashe 'yan ƙasarsu daga Sudan, bayan sun gaza yin haka a yunƙurin da aka yi a baya saboda al'amari ya ƙazance.

    Ƙasashen Yamma da China za su kwashe jami'an diflomasiyyansu da kuma mutanensu da jiragen sojoji na dakon kaya.

  13. An hau Idin Ƙaramar Salla yau Asabar a Iran

    BBC

    Jagoran addini na Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Ali Khamenei ya faɗa yayin hudubar Sallar Idi a yau Asabar cewa "Idan masu iko a ɓangaren majalisar dokoki da na zartarwa da ɓangaren shari'a za su samu cikakken haɗin kai, al'amura ba za su ci gaba da cakudewa har a rasa shawo kansu ba".

    A cewar rahotannin kafofin yaɗa labarai daga Iran, shugaban addinin Musulunci na Jamhuriyar, ya jagoranci Idin Ƙaramar Salla a bana, bayan dakatar da hawan tsawon shekara uku a baa saboda annobar korona.

    A zagaye na biyu na hudubarsa ta Idi, Ali Khamenei ya yi kira ga al'umma da hukumomi a kan kada su fifita wani ɓangare, wani kuma su mayar da shi saniyar ware, lamarin da ya bayyana da "wata dabarar mulki da ta zama dole".

    Ya ƙara da cewa "mayar da wata jama'a saniyar ware, ba abu ne da ko yaushe abokan gaba ke shiryawa ba, wasu lokuta, yana faruwa ne saboda sakaci da sauran matsaloli da kuma dalilai.

    Jagoran addinin ya kuma ce, "Maƙiya suna ƙoƙari su haɗa mutane faɗa ko su shiga tsakanin mutane ne saboda bambancin ra'ayi da hangen zuciya.

    Amma bambancin ra'ayin mutane a kan batutuwa mabambanta abu ne da tun fil'azal bai kamata ya zama shamaki ko kuma sanadin rikici da tashe-tashen hankula ba.

    Da yake jawabi ga jama'a da jami'an gwamnati, Ali Khamenei ya ce "Dole ne mu zauna tare kuma mu kyautatawa juna ta hanyar yin biris da zugar maƙiya da ke jefa shakku da mummunan fata a tsakanin al'umma da kuma a tsakanin al'umma da gwamnati."

    An yi bikin Sallar Idi ne yau Asabar a Tehran da sauran birane.

  14. Yau take Sallah a Ghana

    A yau ne al'ummar Musulmi a Ghana ke bikin Ƙaramar Salla, bayan cika azumin watan Ramadana zuwa 30.

    Mafi yawan ƙasashen Musulmi a duniya sun yi nasu bikin Ƙaramar Salla ne a jiya Juma'a.

    Jami'ai a Ghana sun ce ba a ga jaririn watan Shawwal ba a ranar Alhamis, abin da ya sa al'ummar Musulmi a ƙasar suka cika azuminsu a ranar Juma'a.

    Musulmai dai bisa ƙa'ida kan cika azumin watan Ramadan zuwa 30, idan ba su jaririn wata a ranar 29 ba.

    Don haka washe gari, za ta zama 1 ga watan Shawwal kai tsaye ko da ba a zahiri ba a ga wata ba, kamar yadda ya faru a Ghana.

    Ƙasashe irin su Saudiyya da Najeriya da Nijar duka sun sanar da ganin jaririn watan Shawwal ranar Alhamis, abin da ya sa suka gudanar da shagalin ƙaramar salla a jiya Juma'a.

    Mutane na cike da farin ciki da sada zumunci bayan sauke azumin watan Ramadan.

  15. Barka da rana

    Mabiya wannan shafi namu Buhari Muhammad Fagge ne ke fatan an wayi gari lafiya.

    Da fatan sallah ta riske ku lafiya kuma cikin ƙoshin lafiya, Allah ya kare mu da karewarsa.

    Ku kasance da mu domin kawo muku labarai da rahotanni daga sassan duniya.