Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Ahmad Tijjani Bawage da Abdullahi Bello Diginza

time_stated_uk

  1. Rufewa

    Masu bibiyar mu a nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa musamman kan zaɓen Najeriya na 2023.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.

    Amma ku ci gaba da kasancewa a shafinmu na BBC Hausa.com domin samun sabbin labarai da muke wallafawa a kowanne lokaci.

    Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafai

  2. An garzaya da ɗalibai sama da 100 asibiti bayan harin guba a makarantarsu

    Kafafen yada labarai a Iran sun bayar da rahoton cewa sama da dalibai 'yan mata ɗari aka garzaya da su asibiti bayan an gano suna ɗauke da alamomin shaƙar guba a sanadiyyar wani harin gas da aka ƙaddamar a wata makarantar 'yan mata.

    Kafar yaɗa labaran ƙasar ta ce 'yan sanda sun tsare mutum uku da ake zargi da hannu wajen kai hare-haren guba na baya-bayan nan.

    Akalla ɗalibai 'yan mata goma ne aka kai wa harin a birnin Tehran.

    Sama da ɗalibai mata duba ɗaya ne suke buƙatar a duba lafiyarsu sakamakon matsalar shaƙewar numfashi.

    Masih Alinejad wata mai fafutikar kare hakkin ɗan adam ce a ƙasar, wadda kuma take gudun hijira a ƙetare ta shaida wa BBC cewa iyayen ɗaliban da dama ba su gamsu da binciken da gwamnatin Tehran ke gudanarwa ba.

    Tace, "Ina ci-gaba da tattaunawa da iyalan daliban da aka kai wa harin. Suna cikin damuwa matuƙa, suna cikin yanayin matuƙar baƙin ciki da takaici saboda gwamnatin Iran ta yi alƙawarin gudanar da bincike kan lamarin amma wai shugaban makarantar ya ce an kashe kyamarorin ɗaukar hotunan a ranar da aka ƙaddamar da harin."

  3. Tinubu ya kai wa Buhari ziyara bayan lashe zaɓe

    Bashir Ahmad/Facebook

    Sabon zaɓaɓɓen shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu tare da mataimakinsa Kashim Shettima sun kai ziyara ga shugaban ƙasar Muhammadu Buhari a gidansa da ke Daura ta jihar Katsina.

    A wani saƙo da babban mai taimaka wa shugaban ƙasar kan kafofin sadarwa na zamani Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na Tuwita ya ce Zaɓaɓɓen shugaban ƙasar da mataimakinsa na tare ne da wasu gwamnonin APC mai mulki yayin ziyarar.

    View more on twitter
    Bashir Ahmad/Facebook

    Cikin gwamnonin da suka yi wa sabon shugaban ƙasar rakiya har da gwamnan Kaduna Malam Nasir EL-Rufai da gwamnan Jigawa Muhammad Badaru Abubakar da sauran jiga-jigan jam'iyyar.

    Bashir Ahmad/Facebook

    Da asubahin ranar Laraba ne dai hukumar zaɓen Najeriya ta ayyana Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar ranar Asabar da ta gabata.

  4. Netanyahu ya bayyana zanga-zangar da ake yi a ƙasar da cewa maƙarƙashiya ce

    Firaministan Israela ya bayyana zanga-zangar da ake gudanarwa a birnin Tel Aviv - saboda matakan gwamnatinsa na garambawul a fannin shari'a - da cewa wata maƙarƙashiya ce.

    Ɗaruruwan masu zanga-zangar su taru a garin Hawara na Falasɗinawa tun a farkon wannan mako.

    A jawabin da ya gabatarwa 'yan ƙasar, Benjamin Netanyahu ya zargi shugabannin 'yan adawa ta kitsa zanga-zangar..

    Tunda farko shugaban ƙasar Israela, Isaac Herzog, ya ce yana fargabar faɗawar ƙasar cikin rikici.

  5. Zulum ya amince da ware biliyan ɗaya don sake gina kasuwar Maiduguri

    Gwamnan jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya Babagana Umara Zulum ya amince da ware naira biliyan ɗaya domin sake gina kasuwar birnin maiduguri da ake kira 'Monday Market'.

    A ƙarshen mako ne dai kasuwar ta gamu ta iftila'in gobara, inda aka gamu da asarar dukiya mai yawa.

    View more on twitter
  6. EFCC ta gurfanar da A.A Zaura kan zambar dala miliyan 1.320

    Zaura

    Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin Najeriya zagon ƙasa ta gurfanar da ɗan takarar Majalisar Dattawa na Kano ta Tsakiya na jam'iyyar APC, AA Zaura a kotu.

    EFCC ta gurfanar da ɗan takarar ne wanda cikakken sunansa shi ne Abdulsalam Abdulkarim Zaura a gaban wata babbar kotun tarayya a Kano a yau Laraba 1 ga watan Maris, 2023 a bisa zargin laifuka huɗu da suka danganci zamba.

    A ɗaya daga cikin laifukan da aka karanta masa a kotun wadda mai shari'a Mohammed Nasir Yunusa ya jagoranta, an zarge shi da cewa a wani lokaci a watan Agusta na 2014, ya karɓi dala dubu 200 daga Dr Jamman Al- Azmi a kano, da nufin zamba, da karyar za su yi wata harkar kasuwanci ta haɗin gwiwa

    Wanda ake zargin ya musanta aikata laifin da ake tuhumarsa da shi, bayan lauya mai gabatar da ƙara Aisha Tahar Habib ta karanta masa.

    Lauyan AA Zauran, Ishaq Mudi Dikko,( SAN) ya nemi kotu ta bayar da belin wanda yake karewa, inda bayan 'yar taƙaddama, alkalin kotun, Justice Yunusa ya amince da belin.

    Yanzu dai an ɗage shari'ar har zuwa ranar 2 ga watan Mayu na 2023 domin fara saurare.

    Za a fara shari'ar ne tun daga farko bayan da kotun ɗaukaka ƙara ta soke saki da kuma wanke wanda ake zargin a kan laifin zamba da alkalin babbar kotun tarayya a Kano A. L. Allagoa ya yi a baya.

    Ana zargin A.A Zaura da zambatar wani ɗan ƙasar Kuwait dala miliyan 1,320,000, a kan cewa shi ɗan kasuwa ne da ke harkar gidaje a Dubai da Kuwait da kuma wasu ƙasashen Larabawa.

  7. Kotu ta tura Alhassan Ado Duguwa zuwa gidan yari

    Alhassan Ado Doguwa

    Wata kotun majistare a jihar Kano ta aike da shugaban masu rinjaye na majalisar wakilan Najeriya Alhassan Ado Duguwa zuwa gidan yari bayan gurfanar da shi a gaban kotun.

    Ana zargin ɗan majalisar da muggan laifuka ciki har da zargin aikata kisan kai da mallakar makami ba bisa ƙa'ida ba da hannu a kunna wuta a wani gini.

    An gurfanar da shi tare da wani mutum wanda ake zargi sun haɗa baki wajen aikata kisan kai da tayar da zaune-tseye a ƙaramara hukumar Tudun wada da ke jihar ranar Asabar da ta gabata.

    Alƙalin kotun ya ɗage shari'ar zuwa ranar 7 ga watan Maris domin duba buƙatar yiyuwar bayar da belin ɗan majalisar ko kuma akasin haka.

  8. An gurfanar da Alhassan Ado Doguwa a gaban kotu

    Doguwa

    An gurfanar da shugaban masu rinjaye na Majalisar Wakilan Najeriya Alhassan Ado Doguwa a gaban wata kotu a jihar Kano bisa laifuka masu alaƙa da haɗin baki wajen aikata kisan kai.

    Saurn laifukan da ake zarginsa da sun sun haɗa da raunata mutane da da dama, tare da zargin hannu a kunna wuta a ofishin jam'iyyar hamayya ta NNPP.

    Tayar da gobarar a ofishin a ranar Lahadi 26 ga watan Fabarairu, 2023 ya yi sanadin ƙona wasu mutane da ke cikin ofishin.

    A wata sanarwa da rundunar 'yan sandan jihar ta fitar ta ce kwamishinan 'yan sandan jihar da ke lura da al'amuran zaɓen 2023 CP Muhammad Yakubu ne ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan zarge zargen.

    Laifukan sun haɗa da kisan wasu mutum uku tare da raunata wasu mutum takwas a ƙaramar hukumar Doguwa a ranar, a lokacin da ake karɓa tare da bayyana sakamakon zaɓen ɗan majalisar.

    An yi ta yaɗa hotuna da bidiyon wasu mutane da ake zargi an harba da bindiga a shafukan sada zumunta, inda daga nan kuma rundunar 'yan sandan ta gayyaci ɗan majalisar domin gudanar da bincike kan batun.

    Sanarwar ta ce bayan da ɗan majalisar ya ƙi amsa gayyatar ne, rundunar 'yan sandan jihar ta kama shi a filin jirgin saman Malam Aminu Kano da ke jihar.

  9. Tinubu ya karɓi shaidarsa ta cin zaɓe

    Zaɓen Najeriya

    Hukumar zaɓen Najeriya ta miƙa wa zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu shaidar cin zaɓen 2023.

    Shugaban Hukumar Zaɓen Ƙasar, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya miƙa masa shaidar a Abuja.

    Haka ma, shugaban na INEC ya bai wa mataimakinsa Kashim Shettima, shaidarsa.

    An danka musu takardar shedar ne sa’o’i kalilan bayan da INEC ta ayyana Bola Tinubu a matsayin wanda ya yi nasara a zaben ranar Asabar 25 ga watan Fabarairun 2023, inda ya samu kuri’a 8, 794, 726, da suka ba shi galaba a kan sauran 'yan takara 17.

  10. Mutane a mahaifar Obi na cikin takaici

    Voters in Awka

    Ana cikin zaman takaici a Awka babban birnin jihar Anambra.

    Jihar ta kasance mahaifar ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam'iyyar Labour Peter Obi, wanda ya zo na uku a zaɓen da aka kammala.

    A'amura sun koma yadda suke yayin da mutane ke ci gaba da harkokinsu a jihar da Mista Obi wanda ya kasance hamshakin ɗan kasuwa, ya yi mulki a matsayin gwamna har sau biyu.

    Amma idan ka duba, za ka gansu cikin bakin-ciki kan sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar a ranar Asabar.

    Mutane da dama da aka tattauna da su, sun nuna suna cikin ɓacin-rai - kamar hukumar zaɓe ta ƙwace musu kuri'unsu, zaɓe kuma da suka ce yana cike da kura-kurai.

  11. Zaɓen 2023: Za mu ƙalubalanci nasarar Tinubu a kotu - LP

    Datti Baba Ahmed

    Jam'iyyar Labour Party (LP) mai adawa a zaɓen shugaban ƙasa na Najeriya ta bayyana cewa za ta ƙalubalanci sakamakon zaɓen da ya bayyana Bola Tinubu na jam'iyyar APC mai mulki a matsayin wanda ya yi nasara.

    Yayin da yake jawabi a Abuja a yau Laraba, ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a jam'iyyar LP, Datti Baba Ahmed, ya jaddada cewa akwai kura-kurai a zaɓen.

    "Mun shiga zaɓen a matsayin LP kuma mun yi nasara da sunan LP," a cewarsa. "Kuma za mu ƙwaci haƙƙinmu da sunan LP".

    Tun a ranar Talata jam'iyyun adawa na PDP da LP da ADC suka yi watsi da sakamakon a wani taron haɗin gwiwa, suna masu cewa hukumar zaɓe ta Inec ta gaza saka sakamakon a rumubun IReV da zai sa a gan shi ta shafin hukumar na intanet.

    Peter Obi na LP ne ya zo na uku a zaɓen da ƙuri'u 4,223,277, inda Atiku Abubakar na PDP kuma yake biye wa Tinubu da ƙuri'u 6,301,741.

  12. Sakamakon zaɓen jihohin da ya ba da mamaki a Najeriya

    Zaɓen Najeriya

    A ranar Asabar 25 ga watan Fabarairu, Najeriya ta gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na 'yan majalisar tarayya.

    Zaɓen dai ya kasance mai zafi wanda rabon da aka irin haka tun bayan dawowar ƙasar mulkin dimokuraɗiyya a 1999.

    Sai dai sakamkon zaɓen da ya fito daga wasu jihohi ya bayar da mamaki ganin cewa wurare ne da jam'iyya mai mulki ke samun nasara, amma a wannan aro ‘yan adawa ne suka ci jihohin.

    Katsina

    Katsina dai ta kasance mahaifar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, jam’iyyar hamayya ta PDP ce ta lashe zaɓe a jihar, inda ta samu kuri’u 489,045 yayin da ita APC kuma ta samu 482,283.

    Yobe

    Wata jiha da sakamakonta ya bayar da mamaki kuma ita ce Yobe, inda nan ma jam’iyyar PDP ta lashe zaɓen jihar da kuri’u 198,567 yayin da APC kuma ta samu kuri’u 151,459. Hakan ya faru duk da cewa APC ce ke mulki a jihar.

    Lagos

    Haka nan ma, a Legas, mahaifar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC Bola Tinubu, jam’iyyar adawa ta Labour ce ta samu nasara a zaɓen jihar da kuri’u 582,454, inda APCn kuma ta samu kuri’u 572,606. Hakan kuma ya faru duk da cewa APC ce ke mulki a jihar na tsawon shekaru.

    Benue

    A Benue da ta kasance jihar da PDP ke mulki, APC ce ta samu nasara da kuri’u 310,468, inda ta doke PDP wadda ta samu kuri’u 130,081. Sakamakon ya bayar da mamaki sosai ganin irin yawan sukar gwamnatin tarayya da gwamnan jihar Samuel Ortom ya sha yi.

    Filato

    Wani sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da bayar da mamaki shi ne na jihar Filato. Duk da cewa APC ke mulki a jihar, amma hakan bai hana jam’iyyar Labour samun nasara ba da kuri’u 466,272 yayin da APC ta zo na biyu da kuri’u 307,195.

    Nasarawa

    A Nasarawa ma sakamakon ya bayar da mamaki saboda duk da cewa APC ce ke mulki a jihar da kuma ta kasance mahaifar shugaban jam’iyyar Abdullahi Adamu, hakan bai hana jam’iyyar faɗuwa ba. Jam’iyyar Labour ce ta samu nasara da kuri’u 191, 361 yayin da PDP ta zo na biyu da kuri’u 172,922, sai APC mai 147,093.

    Ribas

    A can Ribas ma, sakamakon ya zo mutane da dama bazata, inda jam’iyyar APC ta doke PDP da ke mulki a jihar a zaɓen shugaban ƙasa, inda ta samu kuri’u 231,593 yayin da Labour ta zo ta biyu da kuri’u 175,555.

    Sakamakon zaɓen waɗannan jihohi dai ya bayar da mamaki ainun saboda ganin cewa ba a taɓa zaton za a ga irin sakamakon da aka gani ba.

  13. Ahmad Lawan ya taya Tinubu murnar cin zaɓe

    Zaɓen Najeriya

    Shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmad Lawan ya taya sabon zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Najeriya, Bola Tinubu murnar lashe zaɓe.

    Lawan ya ce nasarar da Tinubu ya samu ta ɗaukacin 'yan Najeriya ne.

    Ya kuma taya Kashim Shettima murna na zamantowa sabon mataimakin shugaban ƙasa.

    View more on twitter
  14. Osinbajo ya jagoranci taron majalisar zartaswa a Abuja

    Osinbajo

    Mataimakin shugaban ƙasar Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranci taron majalisar zartaswa da aka saba gudanarwa a kowace ranar Laraba.

    Taron ya gudana ne a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

    Ana gudanar da taron ne na mako-mako don tattauna kan matsaloli da ke damun ƙasar kama daga matsalar rashin tsaro da tattalin arziki da kuma sauransu.

    Osinbajo
    View more on twitter
  15. Kungiyar Dattawan Yammacin Afirka sun yaba da yadda aka gudanar da zaɓen Najeriya

    Zaɓen Najeriya

    Kungiyar Dattawan Yammacin Afirka ta yaba wa 'yan Najeriya bisa jajircewarsu lokacin gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na 'yan majalisar tarayya a ranar Asabar, inda ta buƙaci 'yan siyasa da su guji yin kalaman da za su harzuka 'yan ƙasar.

    Kungiyar ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata.

    Shugaban tawagar da kungiyar ta tura Najeriya domin sa-idoa zaɓe kuma tsohon shugaban ƙasar Ghana John Dramani Mahama da tsohon shugaba Goodluck Jonathan, sun buƙaci 'yan siyasa da jam'iyyu da kuma magoya baya da su kai zuciya nesa ta hanyar samawa zaman lafiya wuri.

    Kungiyar ta buƙace su da su bi hanyoyi da suka kamata wajen bin hakkokinsu.

    “A don haka, muke yin kira gare su da su guji yin abubuwa da za su tayar da rikici a wannan lokaci domin kar su jefa ƙasar cikin wani yanayi na rashin zaman lafiya,'' in ji Kungiyar.

  16. Shugaba Bazoum ya taya Bola Tinubu murnar cin zaɓe

    Shugaban Niger Mohamed Bazoum ya taya sabon zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu murnar cin zaɓen da aka gudanar a ranar Asabar.

    Shugaba Bazoum ya bayyana haka ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na twita, inda ya ce yana taya 'yan Najeriya murna bisa wannan nasara da kuma jajircewarsu na tabbatar da ci gaban dimokuraɗiyya.

    Ya ce nasarar ba ta Najeriya kaɗai ba, amma ga illahirin nahiyar Afirka.

    View more on twitter
  17. Ganduje ya taya Tinubu murnar lashe zaɓe

    Ganduje/Tinubu

    Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya kwatanta zababben shugaban Najeriya da aka zaɓa Bola Tinubu a matsayin ɗan kishin dimokuraɗiyya.

    Gwamna Ganduje ya bayyana haka ne yayin taya Tinubu murnar lashe zaɓen shugaban Najeriya da ya yi a aɓen ranar 25 ga watan Febrairu.

    A cikin wata sanarwa da sakataren watsa labaru ga gwamnan Abba Anwar ya fitar, Ganduje ya yaba da irin jajircewar Tinubu da kuma na sauran mutane da suka tsaya wajen ganin sun cimma nasara.

    "Bola Ahmed Tinubu jajirtaccen mutum ne da ke son ci gaban ƙasa da kuma al'umma saboda irin ayyuka da ya yi a faɗin ƙasa,'' in ji Gwamnan.

    Ganduje ya ce jajircewar da Tinubu ya yi na tsawon shekaru wajen ganin tabbatuwar dimokuraɗiyya a Najeriya, shi ya sa suka ga ya dace ya mulki ƙasar nan.

    Ya tabbatar wa 'yan Najeriya cewa zaɓaɓɓen shugaban ƙasar zai yi aiki tukuru waje ganin ya shawo kan matsaloli da ƙasar ke fuskanta.

    Gwamna Ganduje ya gode wa mambobin jam'iyyarsu da kuma dukkan waɗanda suka jajirce wajen samun nasararsu.

  18. NBC ta ci tarar gidan talabijin na Arise naira miliyan biyu

    NBC

    Hukumar da ke kula da kafofin watsa labaru a Najeriya ta ci tarar gidan talabijin na Arise naira miliyan biyu bayan samunta da laifin yaɗa kalaman da za su tunzura 'yan ƙasa.

    A cikin wata sanarwa da NBC ta fitar wadda ta samu sa hannun shugaban hukumar Balarabe Shehu Ilelah, ta ce an kama gidan talabijin ɗin da laifi ne bayan da ya watsa wata magana da gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike ya yi a ranar 24 a watan Febrairu, inda yake suka ga magoya bayan jam'iyyar APC.

    NBC ta ce a cikin maganganu da Wike ya yi ya ce "Ni ba ɗan APC bane kuma ba zan shiga jam'iyyar ba, amma sun sanya na amince da su a matsayin jajirtattu, don haka mulki ya koma kudu".

    Sanarwar ta NBC ta ƙara da cewa Arise ya kuma saka wata tattaunawa da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar APC a daidai lokacin da ake kaɗa kuri'a a ranar zaɓe wanda abu ne da ya saɓawa dokokin hukumar.

    Har ila yau, ta ce gidan talabijin ɗin ya gayyato baki da dama waɗanda suka yi kalamai na tunzura 'yan ƙasa zuwa cikin rikici.

    NBC ta kuma ce cikin laifukan da Arise ya yi, akwai saka wakar wani ɗan Najeriya mai suna Fela Kuti da ke magana kan batun maguɗin zaɓe da kuma cin hanci, inda ta ce bai kamata gidan talabijin ɗin ya saka wakar a lokacin ba saboda ana cikin zaɓe.

    A don haka, NBC ta ce ta ci tarar gidan talabijin naira miliyan biyu saboda aikata waɗannan laifuka da suka saɓawa dokokin kafafen yaɗa labaru a ƙasar.

  19. Hotunan yadda magoya bayan APC ke murnar nasarar Tinubu

    Zaɓen Najeriya
    Zaɓen Najeriya
    Zaɓen Najeriya
    Zaɓen Najeriya