Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza

time_stated_uk

  1. Ya kamata a bai wa matan Afirka damar yin shugabanci – Kamala Harris

    Kamala Harris

    Mataimakiyar Shugaban Amurka, Kamala Harris ta ce ya zama dole a rika bai wa mata dama domin a dama da su a kowane fanni na rayuwa har da shugabanci.

    Ta bayyana haka ne a Accra, babban birnin Ghana inda ta ce bai wa mata dama zai kawo ci gaba ga duniya.

    Ta kuma yi alkawari cewa Amurka za ta yi aiki kafada da kafada da dukkan abokan huldarta domin cike gibin da ke akwai kan batun jinsi.

    Kamala Haris dai na ziyara ne a kasashe uku na nahiyar Afirka.

    Da take jawabi a yau, Mrs Harris ta jinjinawa Afirka ta bangaren basira da kirkira inda ta ce akwai bukatar a magance kalubale kamar tsaro da tasirin sauyin yanayi.

    A jiya ne dai ta sanar da tallafin dala miliyan dari domin yakar ayyukan ta'addanci a Afirka.

  2. Ƙarancin naira: Ƙungiyoyin ƙwadagon Najeriya sun jingine ƙudurin yajin aiki

    NLC

    Ƙungiyar ƙwadago ta NLC da ta TUC sun dakatar da ƙudurinsu na tsunduma yajin aiki daga ranar Laraba saboda ƙarancin takardun kuɗi da ake fuskanta a Najeriya.

    Ƙungiyoyin biyu sun ce za su sa ido tare da bibiya domin tabbatar da ganin babban bankin ƙasar ya ci gaba da samar da takardun kuɗin ga bankunan kasuwanci don sauƙaƙa wahalhalun jama'a.

    Sun ce za su sa ido ne tsawon mako biyu domin ganin ko al'amura za su sauya game da ƙalubalen samun takardun kuɗi a hannu.

    Shugaban NLC, Joe Ajaero da takwaransa na TUC, Festus Osifo ne suka bayyana hakan a taron da suka gudanar yau Talata a Abuja, babban birnin Najeriya.

    Bayan samun bayanai daga rassanta da ke jihohi 36 har da babban birnin tarayyar, NLC ta yanke shawarar jingine yajin aikin da ta shirya yi.

    Ya ce NLC za ta aiwatar da ƙudurinta bayan cikar wa'adin mako biyun da suka ƙara bayarwa matuƙar ƴan Najeriya suka ci gaba da fuskantar ƙarancin takardun naira.

  3. Amnesty ta koka kan yadda aka kashe dubbai da take haƙƙoƙin bil adama a Nigeria

    Sojojin Najeriya

    Ƙungiyar Amnesty International ta yi tsokaci game da yadda ake take haƙƙoƙin bil adama a Najeriya har da hare-haren ta'addanci na Boko Haram da kashe-kashe da azabtarewa da satar mutane da kuma tsare mutane da ba su ji ba su gani ba.

    Ƙungiyar ta bayyana haka ne a rahoton da ta fitar na 2022/2023 wanda kuma ta wallafa a shafinta na intanet.

    Yayin da kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) ke bikin cika shekaru 20 da kafuwa, Amnesty ta ce matakin da kotun ta ICC ta dauka ya sanya ayar tambaya kan ko ka'idojinta na aiki daidai da wadanda aka azabtar a karkashin dokokin kasa da kasa a kowane yanayi ko yanki.

    Ƙungiyar ta kuma koka kan yadda aka kashe ko raunata ko ma ɗaiɗaita dubban farar hula a Najeriya sakamakon tashin hankali tsakanin Boko Haram da ISWAP da kuma sojojin Najeriya da ke arewa maso gabashin ƙasar.

    Amnesty ta ce a wasu wuraren kuma, ƴan fashin daji sun yi kashe-kashe inda kuma aka samu hukumomi da da azabtar da mutane da sanyawa wasu takunkumi da kuma hana su yin zanga-zanga.

    "Hukumomi sun daƙile ƴancin kafafen yaɗa labarai da ƴan jarida na faɗin albarkacin baki. Masu fafutuka da masu zanga-zanga sun fuskanci ƙalubale game da haƙƙoƙinsu na bayyana ra'ayinsu da kuma yin zanga-zanga.

    "Sama da mutum 60,000 aka tilastawa ficewa daga gidajensu. An samu matsala ta rashin bai wa mutane kariya daga tasirin sauyin yanayi lamarin da ya janyo mace-mace da ɗaiɗaita wasu," in ji ƙungiyar.

  4. An kashe mata biyu a cibiyar addinin musulunci a Lisbon

    ss

    'Yan sanda sun ce wani mahari ya kashe wasu mata biyu, bayan da ya daɓa musu wuƙa a wata cibiyar addinin musuluci a birnin Lisbon na ƙasar Portugal.

    An kai harin ne a cibiyar addinin musulunci ta 'Ismaili Centre' da ke birnin

    'Yan sanda sun samu nasarar harbe maharin - wanda ke riƙe da sharɓeɓiyar wuƙa - a ƙafa, bayan da ya yi yunƙurin guduwa.

    Kawoyanzu dai ba a san dalilin maharin na kashe matan ba.

    'Yan sanda sun ce sun samu kiran waye inda aka shaida musu cewa an ga maharin ya shiga cibiyar da misalin ƙarfe 11 na safe agogon ƙasar.

    Shugaban cibiyar Nazim Ahmad ya ce maharin ɗan Afghanista ne, yayin su kuma matan biyu 'yan Portugal ne.

    A wata sanarwar da cibiyar addinin ta fitar a shafinta na intanet ta ce ta kaɗu matuƙa da kisan matan, tare da alƙawarta bayar da tallafi ga iyalan mamatan.

  5. Gobara ta tashi a kasuwar Balogun da ke Legas

    Gobara

    Wata gobara ta tashi a babbar kasuwar Balogun a Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya.

    Rahotonnin sun ce wutar ta kama a inda ake sayar da takalman mata a hawa na biyar.

    Kawo yanzu dai ba a san musababbain tashin wutar ba.

    Tun farko dai gobarar ta kama hawa na biyar kafin ta gangaro zuwa hawa na huɗu har zuwa na uku

    Wani ganau ya shaida wa BBC cewa wutar ta tashi ne da misalin ƙarfe 9 na safe a lokacin da mutane ke shirin fito da kayyakinsu.

    Jami'an kashe gobara na ƙoƙarin kashe wutar, inda tuni kuma aka yi ƙoƙarin killace wutar domin ka da ta haura zuwa wasu sassa.

    Gobarar ita ce ta biyu a cikin ƙasa da wata guda a jihar, inda ko a mako uku da suka gabata wata gobarar ta tashi a kasuwar da ake sayar da kayan motoci a unguwar Apapa.

  6. Magoya bayan APC na zaman dirshan a Abuja

    c

    Magoya bayan jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya sun yi wani maci a Abuja babban birnin ƙasar domin nuna goyon bayansu ga zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu.

    x

    Magoya bayan jam'iyyar sun ce suna zaman dirshan din ne domin taya murna ga zaɓaɓɓen shugaban ƙasar.

    x

    Sun kuma ce sun taru ne domin tabbatar da cewa an rantsar da Bola Tinubu a matsayin shugaban ƙasar aranar 29 ga watan Mayu.

    g
  7. Gobara ta kashe mutum 39 a sansanin 'yan ci-rani

    ee

    Wata mummunar gobara ta tashi a sansanin da ake tsare da 'yan ci-rani a birnin Ciudad Juarez da ke arewacin ƙasar Mexico.

    Rahotonni sun ce aƙalla mutum 39 ne suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon tashin gobarar.

    Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce an ga jami'an kashe gobara da masu aikin ceto na lulluɓe gawarwaki da dama da barguna, a harabar inda lamarin ya auku.

    Wani mutum da AFPn ta tattauna da shi, wanda kuma ya buƙaci a sakaya sunansa ya ce akwai aƙalla 'yan ci-rani 70 da ke tsare cikin sansanin, ya kuma ce mafi yawancinsu 'yan ƙasar Venezuela.

    Babban sifeton 'yan sandan ƙasar ya bayar da umarnin gudanar da bincike domin gano musabbabin tashin wutar.

    Birnin Ciudad Juárez - wanda ke kusa da kan iyakar ƙasar da Amurka - na ɗaya daga cikin garuruwan da 'yan ci-rani ke amfani da su wajen shiga Amurka.

    Mafi yawan 'yan ci-ranin da ba su da takardun izinin kan zauna a sansanin domin samun mafaka.

  8. Buhari ya ƙaddamar da rijiyar man fetur a jihar Nasarawa

    BUHARI

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ƙammadar da aikin haƙar rijiyar man fetu a ƙaramar hukumar Obi a jihar Nasarawa da ke arewa ta tsakiyar ƙasar.

    Ƙaddamar da aikin tona rijiyar zai sa kamfanin mai na ƙasar NNPC Ltd, ta fara tono man fetur daga jihar.

    A cikin watan Nuwamban bara ne dai shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da aikin haƙo man fetur a yankin Kolmani da ke tsakanin jihohin Bauchi da Gombe a yankin arewa maso gabashin ƙasar.

    Yawancin man da ƙasar ke da shi dai tana haƙoshi ne daga yankin Niger Delta a kudu maso kudancin ƙasar.

    Najeriya dai ta dogara ne kan man fetur da take fitarwa a matsayin hanayr samun kuɗin shiga, duk kuwa da ƙoƙarin da gwamnatocin ƙasar ke yi na faɗaɗa hanyoyin samun kuɗin shiga ga ƙasar.

  9. Hatsarin mota ya kashe masu aikin Umara 20 a Saudiyya

    accident

    Aƙalla mutum 20 ne suka mutu wasu kuma 29 suka jikkata bayan da wata motar bus ɗauke da mutane masu niyyar zuwa aikin Umara ta yi hatsari a Saudiyya.

    Rahotonni sun ce motar bas din ta yi hatsarin ne bayan da ta yi karo da wata gada a Aqaba Shaar da ke lardin Asir a kudu maso yammacin ƙasar.

  10. Abin da ya kamata mai azumi ya mayar da hankali a kai a goman farko

    Video content

    Video caption: Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon

    Sheikh Jabir Maihula ya yi mana ƙarin haske kan abubuwan da suka kamata mai azumi ya mayar da hankali a kai a cikin kwanaki goma na farkon watan Ramadana.

  11. Priyanka Chopra ta faɗi abin da ya sa ta daina fitowa a fina-finan Indiya

    dd

    Fitacciyar tauraruwar fina-finan Indiya Priyanka Chopra ta bayyana dalilan da suak sa ta fice daga masana'antar shirye fina-finan ƙasar ta Bollywood.

    Yayin da ta bayyana a wani shirin podcast na Amurka, Priyanka Chopra ta ce ba ta jin ɗaɗin yadda ake cusa harkokin siyasa a masana'antar shirya fina-finan ƙasar.

    Sannan kuma ta ce ba ta jin dadin aikin da take yi a masana'antar.

    Priyanka Chopra ta yi magana kan batutuwa da dama a shirin na podcast, ciki har da ƙaurarta daga masana'antar Bollywood ta Indiya zuwa Hollywood ta Amurka inda ta yi wasu fina-finan.

    Ta kuma yi bayanin yadda ta bar Indiya tare da fara zama a Amurka, da yadda labarin soyayyarta da mijinta mawaƙi Nick Jonas.

    A shekarar 2018 ne Chopra ta auri mawaƙi kuma tauraron fina-finan Amurka Nick Jonas, inda suka ci gaba da zama a Amurka, inda a shekarar da ta gabata kuma ta haihu.

  12. Ahmed Musa ya kamo tarihin da Zidane ya kafa

    RR

    Kyaftin ɗin tawagar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Najeriya Super Eagles ya kamo tarihin da Zidane ya kafa na yawan buga wa ƙasarsa wasa.

    Ahmed Musa - wanda shi ne ya fi kowa buga wa Najeriya wasa - ya buga wasansa na 108 a karawar da Super Eagles ta doke Guinea-Bissau da ci 1-0 ranar Litinin.

    Ɗan wasan wanda ya fara taka wa Najeriya leda a shekarar 2010 na daga cikin tawagar ƙasar da ta lashe kofin ƙasashen Afirka a shekarar 2013.

    Da wannan wasa ɗan wasan ya kamo tarihin da tsohon ɗan wasan Faransa Zinedine Zidane, da ɗan wasan Jamus Jurgen Klinsmann da kuma Tim Cahill na Ingila waɗanda duka suka taka wa tawagogin ƙasashensu wasa sau 108.

    Ɗan wasan mai shekara 30 ya zarta Patrick Vieira da Frank Lampard a yawan wasannin da suka taka wa ƙasashensu wasa

    Ahmed Musa ya ci wa Najeriya ƙwallaye 16, kuma shi ne ɗan wasan da ya fi kowanne ɗan wasan ƙasar zura ƙwallo a gasar Kofin Duniya inda ya zura kwallaye huɗu.

    Ya kuma zura ƙwallaye 92 a ƙungiyoyi daban-daban da ya buga wa wasa.

  13. EU ta bayar da miliyan 75 don magance cutar mashaƙo a Najeriya

    Cutar mashaƙo

    Ƙungiyar Tarayyar Turai ya bayar da tallafin euro 150,000, kwatankwacin naira miliyan 75 don yaƙi da yaɗuwar cutar mashaƙo a Najeriya.

    Tare kuma da taimaka wa al'umomin da suka kamu a jihohin Kano da Katsina da Legas da kuma Osun.

    Tarayyar Turan ta ce ta ɗauki matakin ne sakamakon ƙaruwar yaɗuwar cutar a Najeriya tun farkon shekarar 2023.

    Za a bayar da tallafin ne ga mutane sama da miliyan daya da rabi, inda za a fi bayar da fifiko kan mutanen da ke cikin haɗarin kamuwa da cutar.

    Waɗanda ke zaune a wurare masu wahalar zuwa, kamar yadda ƙungiyar ta EU ta bayyana a wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin.

    Tallafin wani ɓangare ne taimakon da ƙungiyar ke haɗawa na tara asusu don magance aukuwar bala'o'i a ƙasashen duniya ta hanyar ƙungiyoyin Red Cross da Red Crescent.

  14. Yunwa da take hakkin bil adama sun ƙaru a Najeriya - Amnesty

    pppp

    Ƙungiyar kare haƙƙin bil adama ta Amnesty International ta ce an samu ƙaruwar yunwa da take hakkin bil adama a Najeriya da wasu ƙasashen Afirka.

    A cikin rahoton da ƙungiyar ke fitarwa shekara-shekara ta bayyana irin tasirin tashe-tashen hankula a mafi yawan ƙasashen Afirka kudu da hamadar sahara, inda ta ɗora alhakin hakan kan rashin ingantaccen shugabanci da ƙungiyoyin duniya.

    Rahoton ya ce a nahiyar Afirka 'yan jarida da masu rajin kare hakkin bil adama da 'yan adawar siyasa na fuskantar danniya a ƙasashe irinsu Kamaru da Ethiopia da Eswatini da Guinea da Mali da Mozambique da Senegal da kuma Zimbabwe.

    Haka kuma rahoton ya ce ''an samu mace-macen masu zanga-zanga da ƙungiyar ta alaƙanta da amfani da ƙarfi fiye da kima da jami'an tsaro ke yi wa masu zanga-zanga a ƙasashen Najeriya da Chadi da Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo da Guinea da Kenya da Senegal da Sierra Leone da Somalia da Sudan, da wasu ƙasashe.”

    Amnesty International ta kuma nuna cewa rashin hukunta masu take haƙƙin bil adama ya ƙara rura rikice-rikice awasu ƙasashen Afirka.

    Rahoton ya kuma ambato raunin ƙungiyoyin duniya ciki har da Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da ƙungiyar Tarayyar Afirka wajen kasa magance laifukan take haƙƙin bil adama da aka aikata ƙarƙashin dokokin duniya a ƙasashe irin su Myanmar da Yemen,da wasu ƙasashen nahiyar Afirka da suka haɗar da Ethiopia da Burkina Faso da kuma Sudan ta Kudu.

    ''Rikice-rikice, da ƙarancin abinci - wanda yaƙin Ukraine ya haddasa da ɗumamayar yanayi - sun kawo cikas wajen yunƙurin farfaɗo da tattalin arzikin ƙasashen duniya da annobar korona ta haddasa'', in ji rahoton

    Kan haka ne rahoton ya ce an take 'yancin miliyoyin mutane na samun abinci, da lafiya da samun ingantacciyar rayuwa a faɗin ƙasashen Africa.

    Domin kuwa a cewar rahoton''mamayar da Rahsa ke yi wa Ukraine ta kawo nakasu wajen samun alkama a mafi yawan ƙasashen Afirka da suka dogara da alkamar ƙasashen biyu.

    Sannan tashin farashin makamashi ya haddasa tashin farashin kayan abinci a ƙasashen na Afirka, kamar yadda rahoton ya bayyana

  15. Taliban ta kama wani fitaccen mai fafutikar samar da ilimi

    MATIULLAH WESA

    Iyalan wani fitaccen mai fafutikar samar da ilimi a Afghanistan Matiullah Wesa, sun ce Taliban ta kama shi a babban birnin ƙasar Kabul.

    Kawo yanzu dai ba a dai san dalilin da ya sa suka kama shi ba.

    Mista Wesa wanda shi ne ya kafa wata ƙungiyar agaji mai suna Pen Path ya yi aiki da shugabannin ƙabilu a faɗin ƙasar ta Afghanistan domin ganin an sake buƙe makarantu da ɗakunan karatu.

    Shi dai Matiullah Wesa ya yi fice wajen fafutika a kan ilimi a ƙasar ta Afghanistan, domin yana bayyana ilimi a matsayin ‘yancin da addinin Musulunci da ya bai wa kowa.

    Duk da irin barazanar da ake yi masa ba ya ko gezau wajen faɗi tashin ganin an tabbatar wa da mata da ‘yan mata ‘yancinsu na neman ilimi.

    A wani lokaci mai fafutukar yakan ɗebi littattafai a kan babur ya je ƙauyuka domin ƙarfafa wa ɗaliban karkara gwiwa kan yin karatu.

    A jiya Litinin aka kama wasu mata biyu da suka yi zanga-zanga a Kabul domin nuna damuwa kan hana mata zuwa makarantun boko.

    A watan Disamba na bara ne Taliban ta hana ‘yan mata da mata zuwa jami’o’i.

    Ƙasashen duniya da dama sun ƙi yarda da halascin gwamnatin ta Taliban bisa dalilai da suka haɗa da na hana mata neman ilimin boko.

  16. Assalamu alaikum

    Masu binmu a wannan shafi barkan mu da safiyar wannan rana ta Talata.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci, domin ci gaba da kawo muku irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya.

    Ku leƙa shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.