Mu kwana lafiya
Karshen rahotannin kenan a wannan shafi.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Mu kwana lafiya.
Muna amfani da ka'idoji domin samar maku da abubuwa masu kayatarwa a Intanet. Muna rokonku da ku sanar da mu idan kun gamsu da duka wadannan ka'idoji.
Wannan shafi ne da ke kawo muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya - Laraba 23 ga watan Afrilu, 2025.
Umar Mikail da Habiba Adamu da Ibrahim Yusuf Mohammed da Ahmad Bawage
Karshen rahotannin kenan a wannan shafi.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Mu kwana lafiya.
Asalin hoton, Reuters
Indiya ta sanar da daukar matakai kan Pakistan, kwana guda bayan da wasu ƴanbindiga suka kashe mutane 26 a wani hari da aka kai a yankin Kashmir da ke ƙarƙashin ikon Indiya.
Sun haɗa da rufe babbar mashigar kan iyakar da ta haɗa ƙasashen biyu da dakatar da yarjejeniyar raba ruwa da korar jami'an diflomasiyya.
India ta kuma soke bizar da wasu ƴan Pakistan ke riƙe da su, sannan ta umarci masu riƙe da su da su fice cikin kwanaki biyu, yayin da ta buƙaci Pakistan ta yi watsi da "tallafi ga ta'addancin kan iyaka" - zargin da Islamabad ta musanta.
Kisan ƴan yawon buɗe ido na ranar Talata a wani wurin shakatawa a garin Pahalgam na ɗaya daga cikin mafi muni da ya faru a yankin Kashmir da ke ƙarƙashin ikon India a cikin ƴan shekarun baya bayan nan.
Gwamnatin India ta mayar da martani da kakkausar murya kan harin tare da nuna cewa ta rataya alhakin harin ne a wuyar Pakistan.
Hukumomin tsaron India sun yi imanin wata ƙungiya da ake kira Kashmir Resistance ce ta kai harin, kodayake BBC ba ta tabbatar da wannan iƙirarain bahakan ba.
Asalin hoton, Getty Images
Shugaba Donald Trump ya soki kalaman da Volodymyr Zelensky ya yi cewa ƙasarsa Ukraine ba za ta amince da yankin Crimea da aka mamaye a matsayin yankin Rasha ba.
Cikin wata sanarwa, Mista Trump ya ce kalaman na shugaban Ukraine na da matukar illa ga tattaunawar zaman lafiyar da ake yi da Rasha.
Kalaman Mista Zelensky sun zo ne bayan rahotannin kafafan yaɗa labarai da ke cewa Amurka ta amince da yankin Crimea a matsayin yankin Rasha a wani ɓangare na yarjejeniyar zaman lafiya da ake son cimma wa da Rasha.
Trump dai bai tabbatar da rahotannin ba.
Ukraine da wasu ƙasashe ƙawayenta na fargabar cewa Amurka ta fi karkata ga Rasha wajen biyan buƙatunta a kan nasu yayin tattaunawar.
Sanatan da ke wakiltar kudancin jihar Kano, Abdulrahman Kawu Sumaila, ya sanar da sauya sheƙa daga jam'iyyar NNPP.
Wata sanarwa da mai taimakawa ɗan majalisa dattijan kan harkokin yaɗa labarai, Abbas Adam ya fitar, ya ce Kawu Sumaila ya ɗauki matakin ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki da magoya baya da kuma ƴan mazaɓarsa.
"Kamar yadda Kawu Sumaila ya sha nanatawa, dukkan abin da yake yi a siyasance - yana yin sa ne domin walwalar mutanen da yake wakilta kuma zai ci gaba da yin haka," in ji sanarwar.
Sanarwar ta ƙara da cewa Sanata Sumaila zai ci gaba da kyautata rayuwar ƴan mazaɓarsa, da kuma tabbatar da cewa an cika musu alkawuran da aka ɗauka.
Ya kuma ce zai bayyana jam'iyyar da zai koma nan ba da jimawa ba.
Asalin hoton, Twitter/@nysc_ng
Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a Najeriya, NDLEA, ta bayyana cewa nan ba da jimawa ba za ta fara yi wa matasa ƴan hidimar ƙasa da kuma masu shirin yin aure gwajin ƙwayoyi.
Shugaban hukumar ta NDLEA, Janar Buba Marwa (mai ritaya), ya ce an ɗauki matakin ne domin rage shan ƙwayoyin maye tsakanin matasa.
Marwa ya bayyana haka ne lokacin ganawa da darekta-janar na NYSC, Janar Olakunle Nafiu, inda ya ce ba a ɗauki matakin don hukunta waɗanda aka samu suna sha ba - illa kawai ƙoƙarin yi musu magani domin kare lafiyarsu.
"Shan ƙwayoyi abu ne da yake ci gaba da yi wa ƴaƴanmu da iyalai da al'umma illa. Babu inda za ka je a ƙasar nan ba ka ga mai shan ƙwaya ba.
"Mutum ɗaya cikin bakwai na ƴan Najeriya ƴan ƙasa da shekara 15 zuwa 64 na amfani da ƙwayoyi. Muna ƙoƙarin dakile yawaitar ƙwayoyin, amma mu kaɗai ba za mu iya ba sai da taimakon maus ruwa da tsaki - ciki har da NYSC domin ganin an rage masu tu'amalli da ita," in ji Marwa.
Ya ce ɗaya daga cikin hanyar da suke ganin za a iya kawo karshen matsalar ita ce yi wa ƴan bautar ƙasan gwaje-gwaje.
Asalin hoton, Dorset Police
An yankewa wani mutum hukuncin ɗaurin shekara 30 a gidan yari bisa laifin caccakawa wata yarinya ƴar shekara 9 wuka.
Jordan Wilkes, mai shekaru 29, daga yankin New Milton, ya kai hari ne kan yarinyar da ke wasa a wajen gidansa tare da wata abokiyarta a watan Agustan 2024.
Kotun Bournemouth Crown ta saurari bayanai cewa binciken da aka gudanar a kan wayar Wilkes ya nuna cewa ya yi bincike kan kisan James Bulger, da tashin hankalin da ya biyo bayan kashe-kashen Southport, gabanin ya kai harin.
Kotun ta ce Wilkes bai san yarinyar ba kafin ya kai ma ta harin, wanda ya faru a wani adireshi a Glider Close a lokacin hutun makaranta.
Yarinyar da abokiyarta sun yi nasarar tserewa inda suka riƙa ƙwanƙwasa kofofin gidaje da dama kafin wani maƙwabcinsu ya cece su ya kuma kira hukumar agajin gaggawa.
A wani bidiyon da ƴansandan Dorset suka naɗa a lokacin da suka je kama Wilkes, ana iya jin muryarsa a lokacin da ya ke kwatanta wa jami'ai inda makamin ya ke a cikin ɗakinsa.
A binciken da aka gudanar a gidan wanda ake tuhuman, an gano wasu wuƙaƙe da dama da aka ɓoye a wurare daban-daban a cikin gidan.
An yanke wa Wilkes hukuncin ɗaurin shekara 30 a gidan yari bisa samunsa da laifin yunƙurin kisan kai.
Asalin hoton, Reuters
Mataimakin shugaban Amurka JD Vance ya ce ƙasarsa za ta “ tsame hannunta” matuƙar Ukraine da Rasha ba su cimma matsaya kan wata yarjejeniya ba.
Gargadin nasa ya zo ne bayan tattaunawar da aka yi a Landan tsakanin jami'ai daga Burtaniya da, Faransa, da Jamus, da Ukraine da kuma Amurka da nufin tabbatar da tsagaita wuta bayan da sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio da wakilin Amurka na musamman Steve Witkoff suka fice daga taron.
Amurka ta mayar da hankali ne kan tattaunawa a wannan makon a birnin Moscow, inda Witkoff zai gana da shugaban Rasha Vladimir Putin a karo na huɗu, yayin da ake ƙara ƙaimi a yunƙurin kawo ƙarshen yaƙin.
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky, ya ce yana na kan bakansa na a "tsagaita wuta nan take, kuma ba tare da wani sharaɗi ba",
A yau Laraba ne sakataren harkokin wajen Burtaniya David Lammy ke karɓar baƙuncin takawransa na Ukraine domin tattauna batun yaƙin.
A halin yanzu dai, babu wani ƙarin haske game da inda sabuwar tattaunawar ta dosa da kuma yiwuwar nasarar ta.
Asalin hoton, Serhiy Lysak
Mutane 9 ne suka mutu yayin da fiye da 40 suka jikkata bayan wani jirgin saman Rasha mara matuƙi ya afkawa wata motar safa da ke jigilar ma'aikata a gabashin Ukraine.
Harin ya afku ne da safiyar Laraba a tsakiyar birnin Marhanets da ke yankin Dnipropetrovsk da ke kudu maso tsakiyar ƙasar, yankin da ke tsallaken kogi daga tashar makamashin nukiliyar Zaporizhzhia da Rasha ta mamaye.
Shugaba Volodymyr Zelensky ya kira shi "wani mummunan hari - kuma cikakken laifin yaƙi ne da gangan...da aka kai kan fararen hula".
Ya ce akasarin waɗanda suka jikkata mata ne da ke aiki a wani kamfanin haƙar ma’adinai.
Harin dai ya zo ne a daidai lokacin da manyan jami'an Trump suka fice daga tattaunawar da aka yi a London tsakanin Burtaniya da wasu ƙasashen tarayyar Turai da kuma Ukraine da nufin tabbatar da tsagaita wuta.
Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio da wakilin Amurka na musamman Steve Witkoff ne ya kamata su halarci taron, amma daga baya aka sanar da cewa sun fice.
Wakilin Trump na Ukraine, Gen Keith Kellogg ne ya maye gurbinsu.
Asalin hoton, Reuters
Shugaban hukumar Falasɗinawa Mahmud Abbas ya kira Hamas da ƴaƴan karnuka a wani jawabi mai zafi da ya yi inda ya buƙaci ƙungiyar ta sako mutanen da ta yi garkuwa da su, ta ajiye makamanta, tare kuma da tsame hannunta daga mulkin Gaza domin kawo ƙarshen yaƙin da ta ke yi da Isra’ila.
Abbas ya shaidawa wani taro a yankin gaɓar yamma da kogin Jordan da aka mamaye cewa ƙungiyar Hamas ta bai wa Isra'ila uzuri na ci gaba da kai hare-hare a zirin Gaza.
Kalaman nasa dai sun kasance mafi zafi a da shugaban ya furta kan ƙungiyar tun bayan da aka fara yaƙin watanni 18 da suka gabata.
Wani jami'in Hamas ya yi Allah wadai da abin da ya kira "Kalaman ɓatanci" na Abbas wanda ya yi kan "kaso mai yawa ... na mutanensa"
A makon da ya gabata, ƙungiyar ta yi watsi da daftarin da Isra'ila ta gabatar na sabon yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, wanda ya haɗa da buƙatar kwance damarar yaƙi na tsawon makonni shida a yakin da kuma sako 10 daga cikin 59 da suka rage.
Hamas ta sake nanata cewa za ta miƙa dukkan mutanen da ta yi garkuwa da su domin kawo karshen yakin da kuma ficewar Isra'ila daga zirin baki ɗaya.
Amma dai ta yi watsi da batun miƙa makamanta.
Aƙalla mutane 151 ne suka samu raunuka bayan sun durgo daga dogayen gine-gine saboda tsoron da girgizar ƙasa ta haifar, a cewar ofishin gwamnan Istanbul.
Ofishin ya kuma wallafa a shafinsa na X, cewa ba a samu asarar rayuka ba, kuma babu wani gini da mutane ke zaune a ciki da ya ruguje.
Sai dai wani gini wanda babu kowa a ciki ya ruguje sakamakon girgizar ƙasar.
Ministan ilimi na Turkiyya, Yusuf Tekin ya sanar da cewa za a rufe makarantu na kwana biyu Alhamis da Juma'a.
Aƙalla an samu girgiza sau 51 a birnin a ranar Laraba, inda mafi girmansu ya kai ƙarfin maki 6.2, wanda ya shafi Istambul tun da fari, a cewar ministan cikin gida, Ali Yerlikaya.
Tuni masana kimiyya sun ce babbar girgizar ƙasa za ta iya afkawa birnin a kowane lokaci, hakan ya sa a abin da ke faruwa a yanzu ya sanya fargaba a cikin zukatan mazauna birnin.
Asalin hoton, KWS
Wata kotu a Nairobi, babban birnin ƙasar Kenya ta sanya ranar bakwai ga watan Mayu, domin yanke hukunci ga wasu mutane huɗu da ake zargi da fasaƙaurin tururuwa don fitar da su daga Kenya.
Mutanen sun haɗa da ɗanƙasar Vietnam, Duh Hung, ɗanKenya, Dennis Ng’ang’a da kuma wasu ƴan Belgium biyu, Lornoy David da Seppe Lodewijckx.
Kotun ta yi taiƙaitaccen zama a ranar Laraba, kafin ɗage zamanta zuwa ranar yanke hukuncin.
Tuni dukkaninsu suka amince da tuhumar da ake yi musu.
Hukumomi sun ce biyu daga cikin mutanen sun shiga ƙasar ne a matsayin ƴan yawon buɗe idanu.
Masu bincike sun ce an ɓoye turuwar fiye da 5,000 masu rai, a wasu ƙananan robobi da kuma sirinji.
A cewar hukumar kula da namun daji ta ƙasar, (KWS), ana safarar nau'ukan turuwar ne zuwa kasuwannin nahiyar Turai da na Asiya.
Inda ake sayar da kowace turuwa uwa, a kan dala $130.
Ana ɗaukar hukuncin da za a yanke a matsayin mai matuƙar muhimmanci, kuma irinsa na farko da zai kafa tarihi a ƙasar.
Asalin hoton, @GoitaAssimi
Ƙasashen Nijar, Burkina Faso da Mali da ke ƙarkashin ƙawancen ƙasashen Sahel (AES), sun bayyana aniyarsu ta kafa wani gidan rediyon hadin gwiwa.
Ƙasashen uku waɗanda ke ƙarƙashin mulkin sojoji, sun ce za su yi hakan ne domin yaƙi da labaran ƙasashen waje da kuma samar da “sahihan bayanai” ga jama’a.
Hakan na zuwa ne bayan da ƙasashen uku suka ƙaddamar da wani gidan talbijin na intanet na haɗin gwiwa wanda suka ce sun yi don "yaƙi da rashin fahimta" a watan Disambar 2024.
A baya dai ƙawancen ya bayyana aniyar kafa kamfanin zirga-zirgar jiragen sama da kuma bankin zuba jari.
Akalla mutum 250,000 ne ake sa ran za su halarci jana'izar Fafaroma Francis ranar Asabar.
Tuni dubun dubatar mutane suka isa birnin Vatican City cikin kwana biyu da suka wuce domin yin bankwana da fafaroman.
Haka nana, ana sa ran shugabannin ƙasa 100 ne za su je jana'izar, inda za a tsaurara tsaro.
Aƙalla mutane 22 masu yawon buɗe ido aka kashe, bayan wasu ƴanbinga sun buɗe musu wuta, a wani wuri mai kyaun gaske da ake yawan ziyarta, a yankin Kashmir da ke ƙarƙashin ikon Indiya.
An kai harin ne a Pahalgam, wani gari mai matuƙar ban sha'awa a tsaunukan Himalaya da ake yi wa kirari da "Switzerland ɗin Indiya".
Shugaban yankin, Omar Abdullah, ya ce 'harin shi ne mafi muni da suka taɓa gani an kai wa fararen hula, a ƴan shekarun baya-bayan nan.'
Yayin da rahotanni ke cewa wasu da dama daga cikin masu yawon buɗe idon na cikin gida sun jikkata, wasunsu ma na cikin mawuyacin hali.
Shugaban Amurka, Donald Trump, shugaba Vladimir Putin na Rasha da shugabar tarayyar Turai,Ursula Von der Leyen na daga cikin shugabannin duniya da suka yi tur da harin.
Asalin hoton, Reuters
Mai kamfaninTesla, Elon Musk ya yi alƙawarin matuƙar rage rawar da yake takawa a gwamnatin Shugaban Amurka, Donald Trump, bayan ribar da ya ke samu a kamfanin da ke ƙera motoci masu amfani da wuta ta yi mummunar faɗuwa.
Musk shi ne shugaban wata sabuwar ma'aikata da ke bai wa gwamnati shawara kan inganta ayyuka.
Kuma tun a shekarar da ta wuce hamshaƙin mai kuɗin ya kasance a gaba-gaba wajen rage kuɗaɗen da Amurka ke kashewa da kuma rage guraben ayyuka.
Sai dai a yanzu ya ce zai yi matuƙar rage lokacin da yake bayarwa wurin yin aiki da ma'aikatar, inda ya ce zai dinga aiki na kwana ɗaya ko biyu ne kawai a mako, bayan an zarge shi da rashin mayar da hankali a kan Tesla.
Shiga siyasar da ya yi ya sa an nuna masa rashin amincewa a duniya, tare da juya wa motocin da kamfanin na Tesla ke ƙerawa.
Ma'aikatan gwamnati na wucin-gadi irin Musk, yawanci ana ƙayyade musu kwanakin aiki zuwa kwana 130 a shekara.
Kuma idan aka ƙidaya tun lokacin da aka ƙaddamar da Trump, wa'adin zai ƙare a ƙarshen watan gobe.
Sai dai abin da ba a sani ba shi ne, ko mutumin da ya bayar da gudunmawar dala biliyan 250 wurin sake zaɓen Trump, sai haƙura da muƙaminsa.
Asalin hoton, GHANA PRESIDENCY/FACEBOOK
Ƙananan jami'iyyun adawa da kuma ƙungiyar ƴanmajalisar dokoki ɓangaren adawa a Ghana, sun yi tur da matakin da shugaba John Dramani Mahama ya ɗauka na dakatar da babbar mai shari'a ta ƙasar.
A ranar Talata aka dakatar da mai shari'a Gertrude Torkornoo, sakamakon ƙorafe-ƙorafen da shugaban ƙasar ya samu waɗanda ba a bayyana ba.
Ƙananan jam'iyyun adawar sun bayyana matakin da cewa yana da nasaba da siyasa, kuma an ɗauke shi ne domin yankan baya da zai yi zagon ƙasa ga ƴancin ɓangaren shari'a.
An shigar da ƙararraki da dama gaban kotun ƙolin ƙasar domin ƙalubalantar hanyar da shugaban ya bi wajen dakatar da ita.
Inda ƴan'adawar kuma ƴanmajalisar dokoki suka buƙaci a mayar da babbar mai shari'ar kan kujerarta, har sai an kammala shari'un.
Asalin hoton, Reuters
Masu makoki na shiga cocin St Peter's Basilica domin yin bakwana da gawar Fafaroma Francis.
Za a bar cocin a buɗe har ƙarfe 11 na dare agogon Najeriya, Nijar da Burtaniya.
Kuma jama'a zasu ci gaba da yin bankwana da gawar a tsawon kana uku zuwa ranar Asabar, lokacin da za a yi masa jana'iza a binne shi.
Harabar cocin tayi cikar kwari da mabiya ɗarikar katolika da sauran masu alhinin mutuwar jagorar ɗariƙar na duniya.
Kimanin mutane 20,000 ne suka taru a dandalin da ke wajen cocin na St Peter's Basilica, a cewar kafar watsa labarai ta fadar Vatikan.
Asalin hoton, Reuters
Asalin hoton, Reuters
Asalin hoton, Reuters
Asalin hoton, facebook/Multiple
Gwamnan jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya, Uba Sani ya bayar da umarnin ƙwace gidaje da filayen da tsohuwar gwamnatin da ta shuɗe ta Malam Nasiru El-Rufa'i ta sayar a jihar.
Gidajen da filayen da aka ƙwacen sun haɗa da waɗanda tsohon gwamnan ya sayar a kwalejin Queen Amina da ke Kaduna da kwalejin Alhuda-huda da kwalejin Government Commercial da ke Zaria.
Umarnin na ƙunshe ne a wata sanarwar da aka fitar, a ranar Talata da daddare, mai ɗauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar, Dr AbdulKadir Mu’azu Meyere.
Sanarwar ta bayyana cewa an ƙwace gidajen da filayen ne saboda amfanin al'umma.
Sai dai an jima ana takun saƙa tsakanin gwamna Uba Sani mai ci yanzu, da kuma wanda ya gada, Malam Nasir El-Rufa'i.
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban ƙasar Ghana, John Mahama ya dakatar da shugabar masu shari'a ta kotun ƙolin ƙasar, mai shari'a Gertrude Torkornoo.
Matakin dakatarwar shi ne irinsa na farko da ƙasar ta taɓa shaidawa a tarihi.
An fara gudanar da bincike bayan wasu ƙorafe-ƙorafe guda uku da aka yi a kanta, da ke neman a cire ta daga muƙaminta.
Alƙalin- aƙalan ƙasar na da kariya a lokacin da suke kan kujerarsu ta yadda babu abin da zai cire su daga muƙaminsu, sai wasu dalilai ƙalilan da suka haɗa da rashin ƙwarewa a aiki da kuma nuna halayyar da bata dace ba.
Sai dai ba a bayyana wa jama'a abubuwan da ƙorafin ya ƙunsa ba, kuma kawo yanzu ba babbar mai shari'ar da aka dakatar ba ta ce komai ba game da lamarin.
Sai dai tsohuwar babbar lauyar gwamnati ta ƙasar, ta yi ikirarin cewa dakatarwar wani yunƙuri ne na yiwa fannin shari'a zagon ƙasa.
Gwamnatin Najeriya ta ce kimanin ƴanƙasar miliyan 61 da dubu ɗari biyar ne aka yi wa rigakafin cutar maleriya, ƙyanda, shawara, ƙyandar biri da kwayar cutar HPV mai janyo sankarar bakin mahaifa.
Hukumomi a ƙasar sun ce mafiya yawa daga cikin waɗanda aka yi wa rigakafin yara ne ƙanana.
Kuma alkaluman an tattara su ne tun daga shekarar 2023 zuwa yanzu.
Shugaban hukumar kiwon lafiya a mataki na farko na ƙasar, Muyi Aina, ya sanar da hakan a wani taron bikin makon rigakafi na Afrika da aka yi a ranar Talata a Abuja.
Inda ya ƙara da cewa aƙalla yara kusan miliyan 26 ne da ke zaune a jihohu 26 na ƙasar aka yi wa rigakafin ƙyanda a shekarar 2024.
Yayin da wasu miliyan 22 da dubu ɗari biyar da ke jihohin Borno, Yobe da kuma jihar Legas suka ƙarbi rigakafin shawara.
A ƙasar ta Najeriya ana samun ɓullar wasu cututtuka da suke shafar yara daga lokaci zuwa lokaci, waɗanda kuma a wasu lokutan kan kai ga asarar rayuka.