Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Ahmad Tijjani Bawage, Buhari Muhammad Fagge da Mukhtar Adamu Bawa

time_stated_uk

  1. China da Faransa sun jaddada aniyar hana yaɗuwar makaman nukiliya

    Macron da Xi

    Kamfanin dillancin labaran ƙasar China Xinhua ya bayar da rahoton cewa ƙasar ta China da Faransa sun jaddada aniyarsu na hana yaɗauwar makaman nukiliya, da kuma kawar da makaman nukiliya cikin lumana.

    Sanarwar ta ce ƙasashen biyu suna goyon bayan duk wani yunkuri na mai do da zaman lafiya a Ukraine bisa dokokin ƙasa da ƙasa, da ka'idojin yarjejeniyar MDD da kuma adawa da kai hare-hare a kan tashoshin nukiliya.

    Macron na Faransa na ziyarar kwanaki uku a birnin Beijing domin tattauna kan harkokin kasuwanci da kuma yakin Ukraine da shugaban China.

  2. Gwamnati ta shirya muƙabala da Sheikh Idris game da kalamansa a kan Annabi

    Bauchi cleric

    Hukumar Shari’a ta Jihar Bauchi a arewacin Najeriya ta shirya muƙabala tsakanin malamai da kuma Sheikh Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi kan kalaman da ya yi game da Annabi Muhammadu (SAW).

    Wata wasiƙa da hukumar ta aike wa malamin, ɗan asalin jihar Bauchi, ta ce za a gudanar da tattaunawar ilimin ne gobe Asabar, 8 ga watan Afrilu a birnin Bauchi.

    A farkon makon nan ne kalaman malamin suka fara tayar da hazo musamman a shafukan zumunta, bayan ya yi iƙirarin cewa "ba ya buƙatar taimakon Annabi".

    “Ana gayyatar ka zuwa tattaunawa ta ilimi [munaƙasha] game da kalamanka cewa ‘kai! ...Manzon Allah ma ba ma son taimakonsa, ƙarewarta kenan’,” kamar yadda hukumar ta bayyana cikin wasiƙar.

    Bauchi Cleric

    An ga malamin ya bayyana cikin wani bidiyo a ranar Alhamis yana cewa ya ji daga wata majiya cewa zai yi muhawara da wakilan wasu ƙungiyoyin addini a jihar, waɗanda suka haɗa da Izala da ɗariƙa.

    An yi irin wannan muhawara a Kano cikin watan Yulin 2021 lokacin da aka zargi Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara da yin kalaman ɓatanci ga Annabin Muhammadu.

    Bayan muhawarar ne kuma, hukumomi suka gurfanar da malamin a gaban kotu, wadda ta yanke masa hukuncin kisa.

  3. Hajjin 2023: Maniyyata za su biya N2.8m a matsayin kuɗin kujera

    Hajjin Bana

    Hukumar kula da aikin hajji ta Najeriya NAHCON, ta sanar da cewa maniyyata aikin hajjin bana za su biya kuɗi da ya kai naira miliyan biyu da dubu 890 a matsayin kuɗin kujera.

    Shugaban hukumar Zikrullah Hassan, shi ya bayyan haka a yau Juma'a, inda ya ce matsalar hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya da kuma Saudiyya a matsayin abubuwan da suka janyo ƙaruwar kuɗin hajjin bana.

    Hassan ya ce farashin ya kai matakai takwas, inda jihohin Borno da Yobe suka kasance jihohi da za su biya kuɗi mafi ƙanƙanta yayin da Legas da Ogun za su biya kuɗi mafi girma da ya kai naira miliyan biyu da dubu 990.

    Hakan ya faru ne sakamakon bambancin kuɗin jirgi da kuma kuɗin masaukai a Makka.

    Maniyyatan jihohin arewacin ƙasar za su biya naira miliyan biyu da dubu dari tara da goma sha tara.

    Jihohin kudancin kasar kuma su ma za su biya kusan miliyan uku.

    Hassan ya ce abin da ya sa aka samu bambancin kuɗi shi ne yankin arewacin Najeriya ya fi kusa da Saudiyya a kan kudancin ƙasar, kuma irin masaukin da kowace jiha ke kama wa, shi zai nuna adadin kuɗin da za su biya.

    Ya ce kamfanonin jiragen sama da aka amince su yi jigilar maniyyata daga jihohi sun haɗa da Air Peace da Azman da Fly Nas da Aero Contractors da kuma Max Air yayin da Arik Air da Value jet aka amince da su a matsayin jiragen haya masu zaman kansu.

    View more on twitter
  4. Mahara sun kashe mutum 50 a jihar Benue

    Ƴan bindiga

    Rahotannin kafafen yaɗa lababru sun ce an gano akalla gawarwakin ƙauyawa 51 da aka kashe a unguwar Umogidi da ke Otukpo a jihar Benue bayan da wasu gungun 'yan bindiga suka far wa ƙauyen.

    An kuma ruwaito cewa ba a ga mutanen kauyen ba da dama kawo yanzu.

    Shugaban matasan yankin, Adakole Inalegu Daniel ya shaida wa BBC cewa mazauna yankin, ciki har da kungiyoyin matasa na ci gaba da bincike cikin daji domin gano karin gawarwaki.

    Rahotanni sun ce wasu ‘yan bindiga ɗauke da makamai sun mamaye al’ummar yankin a ranar Laraba, inda suka fara shiga ta kasuwar ƙauyen da harbi kan mai uwa da wabi.

    Mazauna yankin sun ce da dama daga cikin waɗanda suka kutsa cikin daji, an yi ta harbin su da bindiga, inda aka yanke kawunan wasu daga cikinsu.

    Duk da cewa an tura jami'an tsaro zuwa yankin, hakan bai dakatar da waɗannan hare-hare ba.

    Mazauna ƙauyukan waɗanda galibi manoma a jihar ta Binuwai, sun sha artabu da makiyaya.

    Manoman dai na zargin makiyaya da amfani da dabbobinsu wajen lalata musu amfanin gona, yayin da makiyayan ke zargin manoman da far wa dabbobinsu.

  5. Hari ya hallaka matan Isra'ila biyu a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan

    Hari a Isra'ila

    An kashe wasu mata biyu a Isra'ila, yayin da wata guda ta samu munanan raunuka sakamakon harbi da bindiga da aka kai a gaɓar yamma da kogin Jordan da aka mamaye, a cewar sojojin Isra'ila da kuma ma'aikatan lafiya.

    Matan na cikin wata mota da ta yi hatsari bayan da aka harbe su a kusa da unguwar Hamra da ke gaɓar kogin Jordan.

    Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Magen David Adom ta ce matan biyu ‘yan shekara 20 sun mutu nan take a wurin, inda na uku, daga cikinsu wanda ke da shekaru 45, ke cikin mawuyacin hali.

    Rundunar ta ce dakarunta sun fara farauto maharan.

    Tun da farko dai an bayar da rahoton faruwar lamarin a matsayin taho-mu-gama tsakanin wata motar Isra'ila da kuma ta Falasɗinawa, amma okacin da sojojin suka isa wurin, sun ga harsashi da dama a cikin motar mallakin ƴan Isra'ilan.

    Jirgi mai saukar ungulu ya ɗauki matar da ta samu rauni zuwa asibiti domin yi mata magani.

    Kwamishinan ‘yan sandan Isra’ila, Kobi Shabtai ya yi kira ga dukkan ‘yan Isra’ila da ke da lasisin mallakar bindigogi da su fara ɗaukar makamansu.

  6. Ƴan bindiga sun sace tsohon mataimakin gwamna a jihar Nasarawa

    Onje Gye-Wado

    Wasu da ake zargin ƴan bindiga, sun yi garkuwa da tsohon mataimakin gwamnan jihar Nasarawa, farfesa Onje Gye-Wado.

    Mai magana da yawun ƴan sandan jihar, DSP Ramhan Nansel, ya tabbatar wa manema labarai afkuwar haka, inda ya ce lamarin ya faru ne da safiyar yau Juma'a.

    Ya ce an yi awon gaba da tsohon mataimakin gwamnan ne lokacin da ƴan bindigar suka kutsa cikin gidansa da ke ƙauyen Gwagi a karamar hukumar Wamba na jihar.

    Mai magana da yawun ƴan sandan ya ce haɗin gwiwar ƴan sanda da wasu jami'an tsaro suna can suna ci gaba da bin sawun maharan da nufin ceto wanda aka yi garkuwa da shi.

  7. Faɗan ƙabilanci ya yi sanadin mace-mace a Taraba

    Darius Ishaku

    Ana fargabar cewa mutane da dama ne suka rasu a wani faɗa tsakanin Kuteb da Fulani makiyaya a cikin ƙaaramar hukumar Ussa ta jihar Taraba.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa "Duk da yake, ba a san musabbabin rikicin ba, amma wani ganau ya ce ƴan ƙabilar Kuteb ne suka zargi Fulani da kai hari kan mutanensu, abin da ya haddasa kisan kai da kuma yin garkuwa da wasu".

    Ganau ɗin ya ce hakan ta sa 'yan ƙabilar Kuteb suka kai wa Fulani hari a Kwe Sati, jiya Alhamis, abin da ya sa faɗan ya bazu zuwa garin Fikye in ji shaidan.

    Ana kyautata zaton cewa mutane da yawa sun rasu.

    Jagoran ƙungiyar al'ummar Kuteb, Emmanuel Ukwen, ya faɗa wa Daily Trust cewa an samu asarar rayuka daga dukkan ɓangarorin kabilun biyu.

    Ya ce mutane sun tsere wa yankin yayin da ake ci gaba da faɗa, inda kuma aka ƙona gidaje da dama.

    Rahotanni sun ce an kai hari gidan Sarkin Lisam Kwe, Ando Madugu, inda wasu fusatattun matasa suka ƙona fadarsa bayan sun zarge shi da mara wa Fulani baya.

    A cikin makon nan ne, shugaban ƙaramar hukumar ta Ussa, Abershi Musa, ya yi murabus, bayan ya zargi gwamnatin jihar da kasa ɗaukar mataki a kan kashe-kashen mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba, da ya zargi Fulani da yi.

    Lokacin da aka tuntuɓi shugaban ƙungiyar Miyetti Allah na ƙaramar hukumar, Alhaji Bello, ya ce ba zai yi magana kan lamarin ba a halin yanzu.

    Shi ma, mai magana da yawun ƴan sandan jihar, SP Usman Abdullahi, ba a same shi ba lokacin da aka kira wayarsa don ji daga gare shi game da wannan al'amari.

  8. Sojojin Najeriya sun ce sun kashe ƴan Boko Haram 48

    Sojojin Najeriya

    Rundunar sojin Najeriya ta ce ta yi nasarar kashe mayaƙan Boko Haram 48, sannan wasu 974 sun ajiye makamai tare da miƙa wuya.

    Daraktan yaɗa labaran hedkwatar tsaron ƙasar, Manjo Janar Musa Danmadami ya bayyana wa manema labarai cewa ƴan ta-da-ƙayar-bayan sun miƙa wuya ne haɗe da iyalansu cikin makonni biyu da suka gabata.

    Ya ce rundunar ta yi amfani da salo iri daban-daban wajen kai hare-hare "a kan ƴan ta'addan Boko Haram".

    Danmadami ya ce dakarunsu na Operation Haɗin Kai sun ƙaddamar da wasu hare-hare a kan ƴan Boko Haram ranar 23 ga watan Maris, cikin ƙananan hukumomin Askira Uba da Mafa da kuma Bama, inda suka kashe bakwai daga cikinsu yayin da wasu kuma suka tsere.

    Ya ce sun yi nasarar ƙwato kayayyaki da makamai masu yawa kama daga kayan haɗa bama-bamai da kekuna da babura da sauransu.

    Danmadami ya ce sun kuma samu nasarar tarwatsa maɓoyar ƴan ta-da-ƙayar-bayan abin da ya yi sanadin mutuwar da dama a cikinsu da jikkata wasu.

    Ya ce hare-haren da suka ƙaddamar da jiragen sama kuma, sun lalata kayayyakin ƴan Boko Haram.

    A baya-bayan nan, dubban mayaƙan Boko Haram ne suka miƙa wuya ga sojojin Najeriya, mai yiwuwa saboda matsin lambar da suke fuskanta daga dakarun ƙasar.

  9. Wayewar masu zaɓe a Najeriya ta hana gwamnoni 10 zuwa majalisar dattawa – Buhari

    Muhammadu Buhari

    Shugaba Muhammadu Buhari ya ce zaɓukan 2023 sun nuna yadda mulkin dimokuraɗiyya ke ci gaba da ginuwa da ƙara ƙarfi musamman ganin yadda masu zaɓe suka waye da kuma sanin shugabannin da za su zaɓa.

    Shugaba Buhari ya bayyana haka ne lokacin da ya karɓi bakuncin sabon Sarkin Dutse, Alhaji Muhammad Hamim Nuhu a fadarsa da ke Abuja.

    Ya ce sakamakon zaɓen da ya nuna gwamnoni guda 10 sun kasa samun nasarar zuwa majalisar dattawa, wata manuniya ce cewa yanzu babu tabbas game da samun mulki, kuma yanzu masu zaɓe ne ke da wuƙa da nama.

    "Hakan ya nuna cewa dimokuraɗiyyarmu na ƙara bunƙasa da kuma yadda masu zaɓe suka waye.

    Abin da ya ba ni mamaki shi ne ɗan Najeriyar da aka raina, a yanzu shi ne ke da wuƙa da nama wajen zaɓar wanda ya dace," in ji Buhari.

    "An mayar da abin kamar al'ada ta yadda idan gwamna ya kammala mulki tsawon shekara takwas a jiharsa, daga nan sai ya tafi majalisar dattawa, ba tare da wata wahala ba.

    Daga yanzu babu wanda zai sake raina mai zaɓe a Najeriya. Siyasa za ta zama abu mafi wahala nan gaba," a cewar Buhari.

    Da yake jawabi, sabon Sarkin Dutse, Alhaji Muhamamd Hamim, ya yaba wa Shugaba Buhari saboda taimaka wa jihar Jigawa wajen samun ci gaba a ɓangaren noman shinkafa da amincewa da gina layin dogo daga Kano zuwa Dutse baya ga dawo da zaman lafiya a jihar.

    View more on twitter
  10. Ana aikin ceto mutum 10 da suka ɓata a hatsarin jirgin sojin Japan

    Hatsarin jirgi

    Ma'aikatar tsaron Japan ta yi alkawarin cewa zata yi duk mai yiwuwa wajen gano mutane 10 nan da suka bace bayan wani jirgin soji mai saukar ungulun ya yi haɗari inda ya fada gabar tekun Miyako da ke kudancin Okinawa.

    Masu tsaron gaɓar tekun sun gano tarkace da dama na jirgin ciki har da kofar shiga cikinsa.

    Ana dai ci gaba da aikin ceto inda aka shafe dare ana yi amma ba a kai ga gano kowa ba.

    Har yanzu ba a san abin da ya haddasa hadarin jirgin ba.

  11. Ƴan bindiga sun kashe ƴan sanda uku a Edo

    Ƴan bindiga

    A ranar Alhamis ne wasu ‘yan bindiga suka kashe jami’an ‘yan sanda uku da jikkata wani guda ɗaya a wani hari da suka kai a jihar Edo.

    Bayanai sun ce jami’an bakin aiki ne lokacin da aka yi musu kwanton ɓauna a kusa da garin Agor, kan hanyar Igarra zuwa Auchi na jihar ta Edo.

    Rahotanni sun ce an kashe ɗaya daga cikin maharan da jikkata wani daga cikinsu.

    An ruwaito cewa an ƙwato bindigogi shida daga hannun maharan.

    Lamarin ya faru ne tsakanin karfe 5:30 zuwa 6 na safe kusa da babbar kasuwar Agor.

    Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar ta Edo, SP Chidi Nwabuzor, ya ce har yanzu rundunar ba ta samu cikakken bayani kan harin ba, amma suna ci gaba da bincike.

  12. Ministan harkokin wajen Rasha zai kai ziyara Turkiyya

    Sergei Lavrov

    Ministan harkokin wajen Rasha, Sergei Lavrov zai ziyarci Turkiyya domin tattaunawa a kan abubuwan da suka hada da makomar yarjejeniyar da aka cimma da zata bayar da damar fitar da hatsin Ukraine ta tekun baharul aswad.

    Wani babban abu da aka cimma a yakin Ukraine kawo yanzu shi ne yarjejeniyar da Turkiyya da Majalisar Dinkin Duniya suka jagoranta a watan Yulin bara.

    Yakin ya janyo Turkiyya da Rasha sun samu kusanci da juna musamman a kan Syria inda dukkaninsu ke goyon bayan bangarorin 'yan adawa.

    Shugaba Recep Tayyip Erdogan wanda za a fafata da shi a zaben kasar da za a yi a watan gobe, yana son fara mayar da wasu miliyoyin 'yan gudun hijirar Syria da ke Turkiyya gida a wani mataki na kara samarwa kansa farin jini a zaben.

  13. Ƴan sanda sun yi artabu da masu zanga-zanga a Paris

    Zanga-zanga

    An yi arangama tsakanin 'yan sanda da masu zanga zanga a Paris, a yayin zanga zangar nuna kin amincewa da kara shekaru riyata a kasar.

    Ɗaruruwan mutane ne suka bi titunan da ke sassan biranen kasar.

    Masu zanga zangar sun kona gine gine da dama da suka hada da bankuna biyu.

    An dai shafe fiye da kwana 10 ana wannan zanga zanga a kan kin amincewa da kara shekarun ritaya ga ma'aikatan kasar.

  14. Buɗewa

    Ma'abota BBC Hausa barkan mu da safiyar Juma'a - Hajj Babbar Rana.

    Kun shigo shafin labarai kai-tsaye tare da ni Ahmad Tijjani Bawage.

    Za mu kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwaɓtanta da sauran sassan duniya.