Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Ahmad Tijjani Bawage, Haruna Kakangi da Buhari Muhammad Fagge

time_stated_uk

  1. Masu zanga-zanga sun yi arangama da 'yan sanda a Paris

    BB

    'Yan sandan kwantar da tarzoma sun yi arangama da masu zanga-zanga a birnin Paris, wannan yamutsi dai na zuwa ne kwanakin 11 da ma`aika su ke yajin aiki don rashin amincewa da wasu canje-canje da shugaban kasar ya yi a tsarin fansho.

    Masu zanga-zangar sun banka wuta a wani gidan abinci da Shugaba Macron ke yawaita ziyara don cin abinci.

    A wani bangare na birnin na Paris kuwa ma`aikatan jiragen ƙasa sun afka cibiyoyin kasuwanci.

    Karsashin masu zanga-zanagar ya fara raguwa bayan gwamnatin Faransa ta ce ba gudu ba ja baya

  2. Isra'ila ta ɗora alhakin harin da aka kai mata a kan Lebanon

    Sojojin Isra`ila sun sanar da kama wasu rokokin yaƙi da a ka harbo daga Lebanon guda 25.

    Wasunsu sun dura a Isra'ilan kuma sun lalata tituna da ababan hawa.

    Hukumar bayar da agajin gaggawa ta ce wani mutum guda ya samu rauni kaɗan da harbin bindiga, wasu rahotanni da ba a tantance sahihancin su ba sun ce ƙasar ta mayar da martani ta iyakokinta.

    Babu wanda ya ɗauki nauyin kai harin wanda ya afku a lokacin da hankula suke a tashe.

    Wani bidiyo ɗauke da yadda 'yan sanda su ke korar Musulmi ma su Ibada a Masallacin Al-Aqsa ya haifarwa da Isra`ilan martanin hare-hare daga bangarori daban-daban.

    Kakakin rundunar sojin Isra`ila ya shaida wa manema labarai cewar kungiyoyin 'yan bindiga daga Falasdinu da ko Hamas ko 'yan Jihadi, kuma ana zargin Iran na da hannu.

    Firaiminista Benjamin Netanyahu ya jagoranci taron tsaro da majalisar zartaswar kasar.

  3. 'Yan mata 20,000 da aka aurar bara sun haifi jarirai 10,000 a Iran

    .

    'Yan mata fiye da 20,000 ne 'yan shekara 15, aka yi wa aure a cikin wata taran da ya gabata a ƙasar Iran, a cewar alƙaluman Cibiyar Ƙididdiga ta Ƙasar.

    A cewar alƙaluma da jaridar intanet ta Etemad ta wallafa, an kuma samu "sakin aure 179 a cikin 'yan matan 'yan ƙasa da shekara 15".

    Akwai 'yan mata 'yan ƙasa da shekara 15 da suka haifi jarirai 1,085.

    Cibiyar Ƙididdigar ta wallafa wannan rahoto ne a kan halin rayuwar zamantakewa da ta al'adar al'ummar Iran a cikin watanni ukun farkon shekara.

    A cewar dokokin kula da hulɗar jama'a na Iran, shekarun aure ga 'ya mace suna farawa ne daga 13, maza kuma daga shekara 15.

    Haka zalika, ana iya aurar da mutum wanda shekarunsa ba su cika ƙa'ida ba, bisa doka amma da sharaɗin yardar mahaifi ko wani mai kula da shi sannan sai kotu ta amince.

    Yunƙurin canza shekarun aure a majalisar dokokin Iran yana da dogon tarihi a ƙasar.

  4. Gamayyar 'yan adawa a Kenya na son a yi wa tsarin mulki garambawul

    bbc

    Gamayyar 'yan adawa a Kenya Azimio, na son a sake yi wa kundin tsarin mulkin ƙasar da aka yi shekara 13 baya garambawul, a wani ɓangare na sharaɗin da suka gindaya na tattaunawar da suka yi ta kawo ƙarshen zaga-zangar da suke yi ta ƙin jinin gwamnati.

    Wata sanarwa da shugaban 'yan adawar Raila Odinga ya sanyawa hannu bayan wani taro da gamayyar ta yi, sun ce za a sake bibiyar kundin tsarin mulkin domin cire bangaren ƙarshe na ragowar manyan masu iko na fadar shugaban ƙasa.

    Masu adawar sun ambato tsarin wanda ya lashe zaɓen ya cinye komai a matsayin matsalar tsarin zaɓen Kenya.

    A makon da ya gabata ne gamayyar 'yan adawar suka janye wata zanga-zanga da suka shirya gudanarwa a ranar Litinin.

  5. An kashe mutum tara da ake zargi da fashi a musayar wuta da 'yan sanda

    .

    Yan sanda a Afrika Ta Kudu ta ce an kashe mutum tara da aka samu da hannu cikin wani hari da aka kai wa motar jami'ai da ke ɗauke da kuɗi, bayan musayar wuta da suka yi da 'yan sanda.

    Da yake aikin ziyara a yankin da abun ya faru na Sebokeng, a kudancin Juhannesburg, Ministan 'yan sanda Bheki Cele ya ce an kwato bindigogi da dama a yayin bata kashi.

    Fashi babban laifi ne a Afrika ta Kudu.

    A ranar Laraba, 'yan fashin sun kashe mutum biyu garin harbin jami'an tsaro.

    An fi samun irin waɗannan hare-hare a Gauteng da gabashin lardin Cape.

  6. Guinea ta ƙwace tan 1.5 na hodar iblis

    .

    Hukumomi a Guinea sun ƙwace tan 1.5 na hodar iblis a wani jirgin ruwa mai ɗauke da tutar Saliyo.

    A tawagar matuƙa jirgin akwai yan Saliyo huɗu, da yan Ghana uku da kuma wasu 'yan Guinea uku suma, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya tawaito.

    Gidan talabijin na Guinea ya ce an kama mutanen baki ɗaya.

    Hukumomin sun ƙara samun wasu jakankuna 60 da kowacce ke ɗauke da hodar da takai nauyin kilogiram 25 kwatan kwacin tan 3.9, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato.

  7. Ghana za ta girke sojoji 1000 a kan iyaka da Burkina Faso

    Garin Bawku

    Mahukunta a Ghana sun umarci sojoji dubu da 'yan sanda su koma aikin tsaron iyakokin ƙasar a Arewa maso Gabas.

    An ɗauki matakin ne sakamakon kashe wani jami`in hukumar hana shige da fice da wasu 'yan bindiga suka yi, tare da jikkata wasu ma`aikatan biyu.

    Babu tabbaci a kan ko su wane ne suka buɗe wa motar jami`an tsaron wuta a ranar Talata lokacin da suke aikin sintiri.

    Amma akwai fargabar yawaitar ayyukan masu iƙirarin jihadi a ƙasar Burkina Faso wadda ke makwabtaka da Ghana.

    Yankin Bawku ya jima yana fuskantar rikicin ƙabilanci.

  8. Shugaba Macron ya tattauna da takwaransa na China kan buƙatar kawo karshen yakin Ukraine

    Ziyarar Macron China
    Image caption: Mr Xi ya tarɓi Mr Macron da Ms von der Leyen a Beijing

    Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya tunasar da Shugaba Xi Jinping na Chaina muhimmancin shawo kan Rasha ta dakatar da yaki da ukraine, a ya yin ziyarar aikin da ya kai Chaina.Kakakin fadar Kremlin Dmitry Peskov ya bayyana wa manema labarai a Rasha cewar la`akari da kyakkyawar dangantakar China da Rasha, babu shakka za ta iya yin tasiri a batun sulhun.

    Wakiliyar BBC ta ce shugabanni a ƙasashen Turai biyu sun bukaci China ta yi amfani da damar da ta ke da ita a Rasha wajen kawo karshen yaki.

    Faransa ta roki Shugaba Xi ya rarrashi Putin ya kara nuna masa illar yaki.

    Ita ma Shugabar Hukumat Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen, ta bukaci China yin duk abin da za ta yi wajen kawo zaman lafiya, ta kuma gargaɗi Beijing da ta guji sayar wa da Rasha makamai.Da ya ke mayar da martani game da wannan bukata, shugaban na China ya bayyana cewa Beijing za ta fi kaunar zaman lafiya ya samu a Ukraine, amma ta hanyar tattaunawa irin ta siyasa.

  9. Bene mai hawa biyar ya rushe a birnin Santanbul na Turkiyya

    Rushewar bene

    Wani gini mai hawa biyar ya rushe a garin Beyoğlu da ke birnin Santanbul na ƙasar Turkiyya.

    Ginin wanda aka daɗe ba a yi amfani da shi ba, ya rushe ne da tsakar ranar yau Alhamis.

    Hukumomi sun ɗauki matakin rufe titin Karaköy Kemeraltı bayan faruwar lamarin.

    View more on twitter
  10. Manyan jami'an Saudiyya da na Iran sun tattauna karon farko a cikin shekara bakwai

    Saudiyya da Iran

    Ministocin harkokin wajen ƙasashen Iran da Saudiyya sun yi tattaunawa a hukumance karon farko tun a shekara ta 2016.

    Wani faifan bidiyo ya nuna Hossein Amir-Abdollahian da Yarima Faisal bin Farhan Al Saud na musabaha da takwaransu na China a birnin Beijing.

    Sanarwar haɗin gwiwa ta ce sun tattauna batun sake buɗe ofisoshin diflomasiyya cikin watanni biyu masu zuwa, da kuma sake buɗe harkokin zirga-zirgar jirage tsakanin ƙasashen.

    Ƙasashe sun amince su dawo da alaƙar da ke tsakaninsu a wata yarjejeniya da China ta jagoranta a watan jiya.

    Ana kallon hakan a matsayin wata alama ta ƙaruwar tasirin da China ke da shi a yankin Gabas ta Tsakiya, da kuma ƙalubale ga babbar rawar da Amurka ke takawa a yankin.

    China na da hulɗa ta ƙuƙut ta diflomasiya, da kuma ta tattalin arziƙi,tsakaninta da ƙasashen Saudiyya da Iran, yayin da dangantakar Amurka da Saudiyya ta yi tsami a shekarun baya-bayan nan, kuma Amurka ba ta da wata alaƙa ta diflomasiyya da Iran tsawon shekara 40.

  11. Chelsea ta naɗa Lampard kocin rikon kwarya

    Frank Lampard

    Frank Lampard ya zama kocin Chelsea na rikon kwarya zuwa ƙarshen kakar nan, bayan shekara biyu da ta kore shi.

    Tsohon ɗan wasan Chelsea ya horar da ƙungiyar tsakanin Yulin 2019 zuwa Janairun 2021, wanda Thomas Tuchel ya maye gurbinsa.

    Ranar Lahadi Chelsea ta raba gari da Graham Potter, wanda ya maye gurbin Tuchel a Stamford Bridge.

    Chelsea tana mataki na 11 a teburin Premier League, bayan tashi 0-0 da Liverpool a kwantan wasa ranar Talata a Stamford Bridge.

    Bruno Saltor ne ya ja ragamar Chelsea a karawar - Lampard, mai shekara 44 ya kalli wasan na hamayya a ranar a Stamford Bridge.

  12. Kotu ta yanke wa mutum biyu hukuncin ɗaurin shekara tara kan aikata fyaɗe

    Wata kotu a birnin Busan na ƙasar Koriya ta Kudu, a ranar Laraba ta yanke wa wasu ma'aikatan hukumar kula dasufurin jiragen ruwa ta ƙasar Liberia hukuncin ɗaurin shekaru tara a gidan yari, bisa samun su da laifin yin lalata da wasu ƴan mata guda biyu.

    Moses Owen Brown da Daniel Tarr dai ana tsare da su a Koriya ta Kudu tun a shekarar da ta gabata, kan zargin yi wa ƴan matan fyaɗe, kamar yadda ‘yan sandan ƙasar suka bayyana.

    Gwamnatin Laberiya ta ce ta bukaci wakilanta na shari'a a Koriya ta Kudu da su samar mata da zaɓin ɗaukaka kara da ake da shi.

    "Gwamnati za ta ci gaba da kasancewa tare da Jamhuriyar Koriya ta hanyar diflomasiyya a hukumance don samar wa Browne da Tarr zaɓi," in ji sanarwar gwamnati.

    Ta ce an sanar da iyalan 'yan ƙasar Laberiyan biyu hukuncin da kotun ta yanke, kuma za a ba su damar ziyartar mutanen.

  13. Yadda ya kamata a ciyar lokacin Ramadan

    Video content

    Video caption: Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
  14. Ƴan Argentina na zanga-zangar adawa da matakin tsuke bakin aljihu

    Zanga-zanga

    Dubban mutane ne ke zanga-zanga a sassan Argentina, don nuna kin amincewa da matakan tsuke bakin aljihun da asusun lamuni na duniya ya sa ƙasar ta yi, a karkashin sabuwar yarjejeniyar da aka kulla kan yadda ƙasar za ta biya asusun bashi.

    A babban birnin ƙasar, masu zanga-zangar sun datse hanya a wurare da dama abin da ya hana ababan hawa wucewa.

    Ɗaya daga cikin masu zanga-zangar ya ce akwai talakawa kusan kashi 40 cikin 100 a Argentina, wanda yawancinsu ba su da gidan zama.

    Ya kuma ce yaro ɗaya cikin biyu a ƙasar na fama da yunwa, don haka abin da ake so a yi babban bala'i ne.

    Al'amura sun tsaya cik a birane 135 na ƙasar.

    Asusun ba da lamuni na duniyar ya sassauta wa Argentina a yarjejeniyar bayar da bashin dala biliyan 44, amma masu suka sun ce yarjejeniyar za ta kara durkusar da tattalin arzikin ƙasar.

  15. Yadda kyanwa ta hau jikin liman a lokacin sallar dare

    Video content

    Video caption: Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
  16. Ana zargin Boka da kisan mutum 12

    KOMPAS

    Ƴan sandan Indonesia sun kama wani boka kan zarginsa da kashe akalla mutane 12 bayan gano gawarwaki da dama binne a bayan gidansa.

    Bokan mai suna Slamet Tohari mai shekara 45, ya faɗa wa ƴan sanda cewa ya binne mutane da dama a wurin da yake zama.

    Ana kuma zarginsa da kashe waɗanda suka je neman taimako gidansa da ke garin Banjarnegara.

    Ƴan sanda sun ce yana yi wa mutane alkawarin ninka musu kuɗinsu, inda lokacin da suka bukaci a dawo musu da kuɗin, sai ya saka musu guba.

    An kama shi ne a makon nan bayan da wani yaro ya kai rahoto wurin ƴan sanda cewa wuri na karshe da aka san mahaifinsa yaje shi ne gidan bokan.

  17. Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Basarake a jihar Filato

    Ƴan bindiga

    Ƴan bindiga sun yi garkuwa da wani basarake mai daraja ta ɗaya a jihar Filato.

    Basaraken wanda ƴan bindigar suka ɗauka a fadarsa mai suna Sunday Dajep, ya kasance hakimin al'ummar Mhiship da ke karamar hukumar Pankshin na jihar.

    Wani ganau ya ce ƴan bindigar sun isa fadar sarkin ne da ke kusa da hanyar Mangu-Shendam da misalin karfe 11 na daren jiya Laraba, inda suka kutsa cikin fadar tare da yin awon gaba da shi.

    Mai magana da yawun ƴan sandan jihar ta Filato DSP Alfred Alabo, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce suna ci gaba da bibiyar sawun ƴan bindigar domin kama su da kuma kuɓutar da basaraken.

  18. Bankin Duniya ya bai wa Najeriya tallafin dala N800m

    Bankin Duniya

    Najeriya ta samu tallafin dala miliyan 800 daga Bankin Duniya domin bunƙasa shirinta na inganta rayuwar al'ummar ƙasar gabanin cire tallafin man fetur a watan Yunin wannan shekara, daidai lokacin da tattalin arzikin ƙasar ke tafiyar hawainiya.

    Gwamnati ta ce za a raba tallafin ne ta hanyar amfani da na’urar aika kuɗi ga ‘yan Najeriya kusan miliyan 50 ko gidaje miliyan 10, inda ta ce waɗannan mutane suna cikin mafi raunin rukunin al'umma.

    Ta ce hakan na da nufin rage tasirin cire tallafin man fetur kan al'umma.

    Bankin Duniya ya damu a kan cewa ƙaruwar tattalin arzikin da Najeriya ta samu na kashi 2.8, bai wadatar ba wajen rage tasirin fiye da kashi 40 na al'ummar da ke fama da matsanancin talauci.

    Najeriya da ta kasance ƙasa mafi girman tattalin arzikin a Afirka, ta ware naira tiriliyan 3.36 a bana domin kashewa a matsayin tallafin man fetur har zuwa tsakiyar shekara ta 2023 lokacin da za ta daina biya.

    Najeriya ita ce ƙasa mafi yawan arzikin danyen mai a Afirka amma tana shigo da man fetur daga ƙasashen waje saboda rashin aiki da matatunta na mai ke yi.