Matsalar 'yan daba na gawurta ne a arewacin Najeriya?

Asalin hoton, Kano State Police
- Marubuci, Ahmad Bawage
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
Al'ummar Minna, babban birnin jihar Neja sun shiga wata rayuwa ƙarƙashin wani sabon mataki na taƙaita zirga-zirga da dare, a yunƙurin hukumomi na daƙile ƙaruwar 'yan daba.
Rikicin 'yan daban da ke neman zama ruwan dare, ya fara hana birnin Minna sakat, har ta kai mutane a wasu unguwanni na jan ƙofa su rufe gida ruf da zarar duhun dare ya kunno kai.
Rahotannin hare-haren 'yan daba na ƙaruwa kusan a kullu yaumin cikin wasu jihohi kama daga arewa maso yamma da arewa maso gabas, har ma da arewa ta tsakiya.
Cikin matakan da gwamnatin ta Neja ta ɗauka akwai: hana fita a kan babura masu ƙafa biyu da masu ƙafa uku ko kuma keke-napep tun daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe.
Ana zargin 'yan daba da sauran masu aikata laifi na amfani da ababen hawan wajen zuwa su kai hari, ko kuma su riƙa bin lungu da saƙo suna auka wa mutane don satar waya.
Gwamna Umaru Mohammed Bago, wanda ya sanar da ɗaukar wannan mataki a wani taro kan tsaro ranar Talata, ya ce ''Babu wanda zai sake ɗaukar duk wani nau'in makami a birnin Minna".
Za a riƙa kama waɗanda ake zargi da laifin daba ko kuma suke da alaƙa da su, in ji gwamnan.
Sannan ya umurci hakimai da dagatai da masu unguwanni su fara aikin tantance duk baƙin da ke shiga yankunansu.
'Ana rufe kasuwanni saboda fargaba'

Asalin hoton, Niger State Government
Wani ɗanjarida mazaunin Minna, ya ce lamarin 'yan daba waɗanda aka fi sani da ƴan sara-suka a jihar ya daɗe yana ciwa al'umma tuwo a ƙwarya.
Lamarin a cewarsa na shafar rayuwar yau da kullum da walwalar jama'a da kuma harkokin tattalin arziƙin jihar.
"Munin batun daba ya janyo kasuwanni na rufewa a wasu lokuta, saboda fargabar abin da zai je ya dawo.
"Ta kai ga dole wani lokaci ana idar da sallar Magriba, mutane ke shiga gidajensu (su rufe) kan tsoron irin tashin hankali da matasan ke haddasawa," in ji Nurudden Daza.
Ya ƙara da cewa abin da ya janyo tashin hankali na baya-bayan nan shi ne salwantar da ran wani direban banki da wani ɗan daba ya yi a Minna, lokacin da suka kai hari.
"Lamarin ne ya (tayar da hankulan jama'a har ta kai) Gwamna Umar Bago ya ƙaƙaba matakin taƙaita zirga-zirga da nufin daƙile ayyukan ɓata-garin," in ji Ɗanjaridar.
Ya ce gwamnan jihar ya ba da umarnin cewa duk gidan da aka san mafaka ce ta miyagu da kuma masu shaye-shaye, to ba makawa a rushe shi nan take.
Ya ƙara da cewa matakin da gwamnatin ta ɗauka ya shafi harkokin yau da kullum na mutane, amma duk da haka mazaunan birnin Minna sun yi na'am da shi - inda suke fatan hakan zai kai ga kawo ƙarshen ayyukan ƴan daba.
"Zuwa yanzu ana ci gaba da kama yawancin waɗanda ake zargin ƴan daba ne.
Rahotanni ma na bayyana cewa wasu ƴan daba tuni suka tattara komatsansu suka bar jihar.

Asalin hoton, Kano State Police
Ya girman matsalar daba take a arewacin Najeriya?
Matakin na jihar Neja, na zuwa ne yayin da rikici ko hare-haren 'yan daba ga alama suka zama wata ja'iba kuma babbar matsalar tsaro a Kano, birni na ɗaya mafi harkokin kasuwanci a arewacin Najeriya.
Hukumomi ba su cika fitar da alƙaluma kan yawan hare-haren 'yan daba ba, sannan da wuya a iya cewa ga adadin matasan da ke shiga harkar daba, saboda rashin aikin yi da shan miyagun ƙwayoyi da kuma rashin ilmi, amma rahotannin kafofin labarai na nuna ƙaruwar mutanen da ke gamuwa da ajalinsu ko samun munanan raunuka a hannun 'yan daba masu zafin kai.
Neja da Bauchi na cikin jihohin da ake jin ƙaruwar rahotannin samun rikicin daba a baya-bayan nan.
Ƴan daban waɗanda yawanci shekarunsu na kamawa daga 17 zuwa 30 suna auka wa mutane tare ƙwace musu wayoyi ko abin hawa, a wasu lokuta ma sukan fasa gidaje su yi fashi.
Haka zalika, an lura da yadda 'yan daban ke daɗa zama masu ƙuru da rashin tsoro, ta yadda da rana tsaka har suna iya auka wa jami'an tsaro da makamai.
A baya-bayan nan, wani bidiyo da ya karaɗe shafin sada zumunta na Facebook, ya nuna yadda wasu tsagerun 'yan daba suka zare wuƙaƙe da sauran makamai suke artabu da 'yan sanda.
Sanarwar 'yan sandan Kano washe gari ta ce wani riƙaƙƙen ɗan daba, Baba Beru ya mutu bayan an garzaya da shi asibiti sanadin raunukan da ya ji. Yayin da ƴan sanda biyu su ma suka jikkata kafin a kai su asibitin Murtala Mohammed don yi musu magani.
Rahotanni sun yi zargin cewa Baba Ɓeru, na cikin 'yan daban da suka addabi unguwannin Gwammaja da kuma Kofar Mazugal.
Ana kuma zarginsa da sace-sace da ƙwacen babura da wayoyi a hannun mutane.
Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Kano, SP Abdullahi Kiyawa, ya ce sun ƙaddamar da bincike domin ganin an kama sauran masu alaƙar aikata laifi da ɗan daban.
Gwamnatin Kano dai ta yi ta ɓullo da matakai iri daban-daban domin shawo kan ƙaruwar ayyukan 'yan daba a birnin.
Na baya-bayan nan shi ne wani kwamitin murƙushe ayyukan 'yan daba, wanda ta ɗora wa alhakin kawo ƙarshen barazanar da suke yi wa al'ummar jihar.
Kafin sannan, mahukuntan Kano sun taɓa ɓullo da matakin taƙaita zirga-zirgar babura masu ƙafa uku daga ƙarfe 10 na dare zuwa ƙarfe 6 na safe, abin da ya durƙusar da harkokin kasuwanci da dama a wannan lokaci tsawon watanni.
Makonnin baya ma, Majalisar Dokokin Jihar ta amince da wani ƙudurin doka da ke ba da ikon kafa rundunar tsaro mallakar gwamnatin Kano, duk dai a ƙoƙarin shawo kan matsalolin tsaron da Kano ke fama da su a yanzu ciki har da rikicin daba.
Shi dai SP Kiyawa ya yi iƙirarin cewa an fara samun raguwar ayyukan ƴan daba a Kano cikin ɗan tsakanin nan.
Ya ce unguwannin da a baya aka fi samun rikicin daba sun haɗa da Sheka da Ɗorayi da kuma Kofar Mata.
'Rashin sana'a ne yake ƙara ta'azzaara dabanci a Bauchi'

Asalin hoton, Kano State Police Command
Can ma a jihar Bauchi, rikicin 'yan daban na ƙara abin damuwa ga mazauna birnin na arewa maso gabas.
Wani mazaunin Bauchi kuma ɗan jarida ya shaida wa BBC cewa kafin zuwan rikicin Boko Haram, ba a san da matsalar daba ba a jihar.
Mu'azu Harɗawa ya ce mahukunta sun yi iyakar ƙoƙarinsu wajen daƙile matsalar, sai dai har yanzu rikicin 'yan daba na nan yana faruwa a unguwanni nan da can.
Sai dai, mun tuntuɓi kakakin ƴansandan jihar Bauchi SP Ahmed Wakili kan lamarin, inda ya tabbatar da cewa a iya saninsu babu ayyukan ƴandaba da ke barazana ga jihar.
"Gwamnatocin baya musamman na Mallam Isa Yuguda ta ɓullo da wani tsari na yi wa ƴandaba aure, da ba su jari don kama sana'a bayan an karɓe makamansu".
Sai dai ya ce lamarin ya riƙiɗe zuwa na ƴan sara-suka daga baya.
Ya ce unguwannin da ayyukan daba suka fi addaba a birnin Bauchi sun haɗa da Kofar Dumi, Konar Kwaila da Anguwan Borno da sauransu.
Ɗan jaridar ya kuma alaƙanta matsalar da siyasa, inda ya yi zargin cewa wasu daga cikin ƴan daban na aiki ne ta ƙarƙashin ƙasa ga wasu manyan 'yan siyasa.
"Rashin sana'a ya ƙara ta'azzara matsalar. Yanzu an wayi gari ayyukan tsagerun matasan ya zame wa mutane alaƙaƙai," in ji Harɗawa.
'Akwai unguwar da ba ka isa ka fito da babur ba'
Ɗan jaridar ya ƙara da cewa matsalar ta shafi rayuwar yau da kullum sosai a Bauchi.
"Akwai anguwar da ba ka isa ka fita da babur ɗinka ba, ko kuma ka ɗaga waya da daddare," in ji shi.
Ya ce rashin abin hannu shi ne ummul'abaisin ci gaba da wanzuwar ayyukan 'yan daba a jihar.
Don haka ya shawarci gwamnati ta haɗa da matasan a cikin sabbin ma'aikatan da take shirin ɗauka domin ragewa ko kuma kawo karshen matsalar.
Ya ce cikin matakan da al'ummomin jihar Bauchi ke ɗauka don rage kaifin ayyukan daba har da saukar karatun Al-Kur'ani a masallatai da kuma addu'o'i a coci-coci.